DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????
COPY BY ZAINAB BUTALAWA

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM

    BISMILLAH

INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA SABON NOVEL,MASOYA MAKARANTA NOVELS DINA INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA GODIYA ME TARIN YAWA,ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA.

FREE PAGE

    NA KUDI NE

Dari biyu 200 ne shiga group.

ga Accnt number
0175487861 Asmau Garba Muhammad Gtbank.

Masu Tura katin MTN ko VTU ga Number
08033933642

‘Yan Niger ku Nemi wannan number
+227 90 79 59 39

Littafan Dana Rubuta sune
GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MAAIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
HADIN KAI
ME MAGANI
TUBABBIYA

Novels Dina na kudi ko wanne Complt Dari Uku 300 ne sune

RASHIN SA’A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA AND
DANGIN RABI….

          1

By
AsmaBaffa

Page naku ne

MAMAN SAMHA
AUTA

   Ranar Asabar misalin karfe Sha daya na dare Ana tafka ruwan sama me karfi tare da Iska Mama na wacce nake Kira da Iya ta Bude wata ragargajajiyar kofar mu ta gidan ta banko Ni waje kofar gida Ina kuka da Ihu ga tsoro Amma Iya ta barni tare da Rufe gidanta gaba Daya Ina ihu na shiga buga kofar gidan ba ji ba gani Kamar Zan balla kofar,Allah sarki Uwa Bata iya kyale Ni ba tana jikin kofar daga ciki ta Bude kadan tare da leko da kanta tace Yaya Kika ce? Cikin Sauri nace Alqur'an na yarda kiyi aurenki Iyata,Ni kina Uwata mahaifiyata ta ya Zan hanaki yin Aure sunnar Manzo kiyi Hakuri Iyata na yarda Zan biki duk inda Zaki zauna a matsayin Agola,Murmushi Iya Mahaifiyata ta saki sannan ta Bude min kofa na fada gidan cikin Sauri ta rufe muka shiga dakinmu, Kaya na canja tare da matse Wanda Suka jike na shanya,Iyata ta Miko min Tyga tare da cewa gashi ki shafa sabo da Kar mura ta kamaki, Karba nayi, Iya ta kalle ni tace Rumaila gwara ma ki hakura da Kaddarata ta Aure Aure,Nifa ban yadda da Zaman Hakuri ba matukar ba soyayya ko akwai Talauci da wahala dole a sake Ni na fito ban gaji wahala ba sannan bana zaman hakuri ba soyayya kawai a fito.

 Ina kallon Iya Hawaye ya gangaro min a saman kumatu na nace Iya Ra'ayinki ne Amma yanzu ko kunyar mutane Baki ji Ana kallonki a wata bi ta can Ace Aurenki Takwas kina Fitowa yanzu na Tara Zaki Yi kuma gashi sai ki tafi dani Agola bana karatu sabo da yau Muna wancen garin kwana kadan kin Koma wani garin kinyi sabon Aure, Yan Uwana da muke Uwa Daya kowa garinsu daban Babansa daban ba Shakuwa ba komai tsakaninmu ,Ni Babban tsoro na Iya karki auri me cutar Hiv mu Shiga uku,Idan Baki rufe min Baki ba sai na kore ki kofar gida Ana ruwan Nan ba abinda ya dameni,Kuma wlh Kika sake magana akan auren da zanyi sai na karya ki,Ni da nake so ma na samo Mana miji me kudi Wanda zamu Huta Amma ke Yar iska ko baza ki yarda ba sai nayi,ke din banza har Zaki juya ni,to Uban naki wata tsiya yayi min? 

Iya na kalla na furta ai kuwa kinci tuwo da man shanu sabo da kince kullum Affa na sai da man shanu ake Miya a gidansa kullum,man shanun banza me zai Kara in Banda shawara a jikin bawa cewar Iya.
Shuru nayi ban cewa Iyata komai ba kawai na kwanta abina ba Addua ba komai sabo da ba wata makaranta nayi ba Babu na Addani bare Boko sai yawon Agola gida gida ga tallan Awara kullum ba fashi kasuwannin kauyukan dake kusa da mu muke zuwa ko yaushe tare da kawaye na.

 Washe Gari nice na dama Mana Koko naje na siyo kosai Muka karya ,Iya Kuma tayi wanke wanke Ni Kuma nayi shara tare da wanke bayi harda goge ledar tsakar dakin mu,Ina gamawa na gyara waken soya na Awara na Kai markade sanye cikin Wata tsohuwar Shadda ta ja wacce ta Gama rubewa kadan take jira ta dare gida gida,Bayan na dakko markade na koma Palo na zauna,Ina Zama rigata ta yage ji kake Beeeeee tun daga Hammata zuwa ciki na,Nace Iyata Shadda tayi Esfaya (Expired) Zo ki gani,Iya tana daga daki Tace Haba? Yasin, Alqur'an Iya ta beke Amma wannan Shadda Bata da mutunci,Allah ya Isa Kudi na,Tsakanina da kamfanin Daya buga wannan Shadda sai Allah ya Isa ace Shekara goma kacal sai ta beke,yanzu Duniya ta lalace Rumaila Atamfa ma yanzu Bata Shekara biyar lafiya kalau,shi yasa nake so na auri me kudi ko zamu samu mu rabauta a gidan duniya cewar Iya, Amma inda kisan Bakin Uwa Rumaila Aure nake tayi Ina hango kudi Amma sai na Shiga sai Naga ba haka ba,nayi Addu'ar nayi har na Gaji Shuru kake ji,Rumaila Ni kuwa na kyalkyalewa iya da dariya nace Iya ai idan baka gode Rahmar Allah ba ka gode azabarsa, Babana gashi Nan kullum sai hararata yake Yi sabo da abinda Kika Masa kin goga min bakin fenti Iyata bani da Inda zanje naji sanyi a raina, Billahillazi gwara ki kaini wanke wanke da shara da wannan Agolancin da nakeyi.

Har yanzu Iya kin Rasa me kudi farko Iya Kika Auri Alha.....zanci Ubanki tashi ki dafa Awara a soya ki tafi kasuwa Jibi za a daura Aure da tarewarmu Baki daya,nace Iya ai Bazawarin naki yace sai kinyi wata Daya a gidansa Zan bi bayanki gidan wa zan tafi na zauna kin San dai kaf Yan Uwana basa kaunata bama shiri sabo da Rashin Shakuwa kowa ba ruwansa da kowa ki duba yanda muke Shan bakin Talauci Amma duk cikinsu Babu me iya siyo ko Omo ya kawo miki,Kawai ki Bari Nabi Rabi kawata Birni gidan Yan uwansu Tace zasu je ko zasu samo kwancen Kaya tana ta rokata mu tafi tare Kinga sai mu tafi idan kinyi auren idan wata ya cika sai mu dawo na dawo gidanki ko? Iya ta washe Baki tace halina da ke Basira watarana Kuma Baki da maraba da tinkiya Rumaila,kuje hakan yayi Amma kafin ki tafi zamuje gidan Yan uwanki ki Kai musu ziyara,Allah ya kaimu Na Furta sannan na mike na Isa gindin Murhu na Fara Awara.

Karfe biyu na Gama naci tawa iya ma ta iba sannan nayi wanka na shirya cikin wata jemammiyar doguwar rigata ta wani tsohon lace Wanda aka Yi Yayinda tun lokacin mulkin Obasanjo rigar ta tsingile min sosai fararen kauri na a waje domin tun Ina karama Babana ya dinka min yanzu Kam na girma Amma Haka nake kakabawa a jikina kadan take wuce gwiwa ta,ni ba gwanar kwalliya bace Mai kawai nake laftawa na Kara gaba,na dauki Awarar kenan a katin bokiti sai kuwa Rigata daga Hammata ta sake yake darewa ji kake keeeeeeett ga su Rabi kawayena su Hudu sun biyo min zamu tafi kasuwa,Rabi Tace Oh Rumaila ji rigarki ta barke, wallahi Rabi Bari na canja wata,Dakinmu na shiga na canja wata tsohuwar atamfa Riga da zani wacce itama kadan take jira, Awara na dauka a saman kaina katon botiki, ya Maganar mu Zaki je Birnin kuwa?Rabi ta tambaya, Mun fita a gidan Nace ai Iya ta amince Ihu Muka saki gaba daya na Murna,Rabi ta duro Ashar Tace Ashe zamu Nemo suna a can,idan muka je mu tsaya mu kalli harka mu dawo a waye,Nace Wai Rabi ya kuke da Yan Birnin ne? Ban taba gani sunzo inda kuke ba Amma ku duk Shekara sai kunje ko idan suna biki Amma ku ko me kuke Yi Basu taba zuwa ba.

Rabi ta gyara Daurin zaninta Kamar bakin almakashi tace Kutmar ai dangantakar ba wata me karfi bace kawai dai suna Aiko Mana da zakka idan sun fitar da sauran su,a kakanni muka hada jini da su,duk Shekara suna hada wani Abu Wai ko famali Mitti(family meeting) ko me oho dai da turanci suke fada abinsu,Cikin kawayen Saude tace tab kice Dangin dangarere ne ,Hajara ma tace kalan dangi Dorin dofino kunu Bayan Ludayi,Rabi Tace gashi Basu da mutunci kakar su ce kawai me kirki Ana ce Mata Nenen kauye,Akwai wani saurayi a gidan na rantse da Allah Rumaila idan Kika ganshi sai kin Raina kanki duk kyawunki Baki Kama kafarsa ba,gashi in fada Miki Bai fiye Hausa ba sai turanci gashi mugu bashi da mutunci ga masifa kowa tsoronsa yake ji,idan fa shigo Palo kowa sai ya fita,idan Kuma zaiyi magana ba a magana sai ya Gama ya fita,idan Kika ganshi da kanki Zaki ji kina rawar sanyi, Rumaila tace Rawar sanyi kamar wacce Iro ya San min kwaya na Sha, mu Ina ruwanmu kawai birni zamu gani muyi harkar mu abinmu mu koyi abinda muka koya mu dawo,Hajara tace bazan je ba to ba ruwana,Nace zanje Ni zuciya Babu Kare ya dauke ba abinda ya dameni da ace zasu daukeni aikatau ma Dana lallaba Iyata ta barni na tafi ko banza na koyi gayu,Yo Ni me ya dameni ,Kamila Zan koma suyi zaton wata Ustaziya ce Ni su kauna ce Ni na dangwali arziki,suna surutu har Suka Isa bakin titi sannan Suka hau machine su hudu a machine guda Daya jal,Haka Suka je kasuwa talla.

Bamu dawo daga Talla ba sai dare,wanka nayi dake dama ba damuwa mukayi da Sallah ba sai munga dama Muke dungurawa sabo da bamu iya karatun komai ba sai Iya irga kudi,Lissafin kudi a kaina kamar computer sabo da Talla,Allah yasa Muna da tsafta sosai da sosai bama Zama da kazanta Haka Bakina kullum sai nayi Brush da safe sannan Kuma duk abinda naci sai nayi aswaki kullum zaka ganni fes sai kayan sawa ta Babu na kirki sabo da talauci.

Bayan kwana Uku aka Daura Auren Iyata da Ali Me Shayi Dake wata rigar kusa da mu kauye ce sosai na Fulani Kamar Garinmu,Bakin ciki ya cika min zuciya na fashe da kuka a gaskiya Auren Nan Na Iya Yana damu na,ganin Ina ta kuka Iya tace gwara ma ki hakura Rumaila idan kin gaji ki fito da miji ayi Miki aure ai kin Kai shekaru har Goma Sha biyar gaba Daya sai surutu ake Yi a kanku ke da kawayenki su Rabi cewar Kun gandame Anki a muku aure ubanki ma yace ya zare Hannu a kanki ba ruwansa ko Zaki Shekara dari,Nan da kwana Uku Zan tare a gidan Ali me Shayi Indomie da kwai da Shayi sai kin gaji da shi Rumaila ai ko iya wannan ya Isa a so auren Ali Me shayi,Nace Iya sabo da Indomie? Indomie fa Iya? Dan babanta ita Indomie din abinda sai naci guda uku ko Hudu take Isa ta,Iya ta Harare ni tare da furta tashi ki tafi Gona ki Yo Mana itace sannan ki ebo kashin Bilade( kashin Shanu) dake kusan girkinmu gaba Daya garin da kashin Shanu mukeyi bushashe shi ake zubawa a cikin Murhu duk warin Nan ba ruwanmu.

 Haka na Biya ta gidan su Saude Babu ko Riga a jikinmu Daura kirji ne kawai har dankwali Babu a kanmu sabo da Rashin Ilimin Addini,Da fanteka Muka je Muka ciko su da kashin Shanu busashe da itace Kuma dauri guda a hannun kowaccen mu,Muna tafiya Muna Hira Saude ta kalleni tace Rumaila nima fa Dani za a je Birni Inna ta yarda,Heeeeee....muka saki shewa,Saude tace Rumaila Allah ya zuba Miki kyau ke Kam gaba Daya Dangin Babanki Kika yo Kamar larabawa da ku Amma duk kinfi su kyau,Hmm Allah ya taimake Ni banyi Hancin Iyata ba Kato da shi ga Fadi da kafafen shakar Isa maka Maka sai dai Iyata ma tana da haske ba laifi,Haka har muka Karasa gida Bayan mun Tara itace da kashin Shanu Rijiyar dake garin mu kwara biyu ne kacal Nan Muka je tare da ebo ruwa muka cika gidanmu da ruwa sannan nayi wanka.

Dare na Yi muka fita kofar gidan Su Hajara can muke taruwa mu raba dare Muna zance da samari tare da wasan banza kokawa da maza sabo da jahilci ya Gama ratsa mu bamu San komai ba abinda muka ga dama shi muke Yi bamu dauki Wasa da maza a komai ba ko wasan doke doke.

Yau ban kula kowa ba na koma kofar gidanmu na zauna Ni kadai Ina tunanin Rayuwa ta da Kuma ta Mahaifiyata,Kai na daga sama Ina tunani na,sai ga yaron makwafta ya fito daga gidanmu yace Rumaila Wai kizo Inji Iyanki,Juyowa nayi tare da kallon yaron nace ka fada Mata bazan samu damar zuwa ba Tunani nake Yi.
Yaron da gudu ya fada gidanmu yace Iya Tace baza tazo ba tunaninta takeyi,Iya dariya Maganar ta Bata tasan Yarta zata aikata sai kawai Tace da yaron jeka abinka yaro.

Kafin Iya ta tare yau da Sassafe tasa na shirya nayi wanka Nasa sabuwar atamfa ta guda Daya tilo da nake da ita ta Sallar bara Riga da zani banyi kwalliya ba Haka na Samu dankwali me santsi Wanda bana atamfar bane na daura a kaina tare da zamge kaina goshina ya fito tal Yana kyalli sabo da yaji wahalar Dauri,Hausar mu Bata Gama fita kamar ta Hausawan Asali Muna magana kasan Real fulani ne mu,A kafa Muka taka zuwa Babban titi Yayinda Muka shiga Motar Birnin kudu dake duk kauyukan da Iya tayi Aure Aurenta kusa da juna suke har garin mu a Jigawa state,can gidan Mijin Iya na farko Muka shiga Gidan Alhaji Rabiu a Nan Iya tana da Yarta Rukayya wacce ta Dade da Aure yaranta Shida,Sam bamu Shaku ba shi yasa Basu damu da Ni ba Nima bana saurarsu,Munyi Dace Alhaji Yana gidansa na kasa Wanda yasha siminti Iya an auri masu kudin kauye,Matarsa ta sannmu tunda Muna zuwa jefi jefi ganin Rukayya tun Ina karama,a mutunce ta karrama mu a cikin palonta ta kawo Mana ruwa da Abinci wake da taliya taji man gyada da yaji,Muka ci muka koshi Ina ta Santi sabo da tsakani da Allah Iyata Bata iya daga yaji me Dadi ba sai dai ta gambaza uban gishiri,Surutu na yasa nace Iya ki koyi daka irin wannan yajin,Dundu Iya ta Durma min a gadon bayana na saki Kara,Matar Alhaji tace Haba Iya Yaya Haka yarinya ce fa,Hawaye na fara nace Iya yo ai gaskiya na fada akan nace yajin mu ba dadi sai gishiri….harara ta watsa min nayi shuru.

A Nan ta zuba Mana ruwa tace kuje kuyi Alwala kuyi Sallah sai ku Karasa gidan Rukayyan,Bana son Sallah na Saba bana Yi don Kar nayi sai nace Bani da tsarki bana Sallah Ina sani ban Fara Jinin Haila ba karya nayi kawai,Iya Ce kadai tayi Sallah Dake Iya gaskiya tayi makarantar Allo da iliminta dai dai gwargwado kawai Bata damu tayiwa Yayanta tarbiyyar hakan ba,Bayan tayi Sallah Haka muka tafi gidan Rukayya,Rukayya itace mace ta biyu a wajen mijinsu mijinta Ba laifi Haya yake yi da machine Dan acaba ne kuma Yana da kokarin ciyar da matansa da sutura,Rukayya kuma tana yin Alalar siyarwa,Da fara'a ta karbe mu zuwa dakinta,Har mijinta da Kishiyarta Muka gaisa da su sannan ta kawo Mana Alala me zafi,Na Bude kwanon nace Iya yau sai dai ki juya kanki Yamma can matukar Kika Yi kwanciyar Kai da kafa da Ni kamar yanda mukeyi to fa baza Kiji dadin bacci ba domin gaskiya Alalar Nan zanci cikin dare kuwa kin San Dole na sarareki da tusa,Dariya su Iya da Rukayya Suka dinga Yi nace ai gaskiya ne,Wai ke Rukayya ya kikeyi da mijinki? Tunda Kina Alala kullum ai Dole kina ci shima Yana ci yanzu cikin dare Haka zaku kashe kanku a gado Daya? Ki banko Taki ya shanye shima ya banko tasa ya kukeyi da safe bakwa Jin kunyar juna? 

Fuska Rukayya ta Bata Tace zanci Ubanki Rumaila dama Ni halina Dake kenan,cin Alala nayi sosai sannan muka Mata Sallama ta Bamu dari biyar da Sabulun wanka da Omo Rukayya tace sai nazo Inshaallah watan gobe Iya,Allah ya kaimu,Can wani kauyen muka nufa a machine me shegen nisa Nan ma Gidan Tsohon Mijin Iya ne wani babban Malamin Tsubbu Malam Hamisu,can ma Iya tana da Danta Jabeer Wanda Yana da aure da Yarsa daya,Jabeer shima Malamin soro ne a Nan ma muka Dan jima shima yace zai Zo ya bamu dubu uku,daga Nan Kusa da kasuwar Shuwarin muka je gidan Isyaku shima me Arzikin kauye ne Iya tana da Danta Imran a can saurayi ne sosai shima da Matarsa Daya Bata Haihu ba,a garin dai Iya ta Auri Malam Muktar Wanda shi Baya Haihuwa ta fice daga gidan sabo da aure auren Muktar da son mata.

 Daga Nan Iya taje Rimgim gidan Alhaji Muzammilu dagaci ne tana da Basira da basiru Yan biyu ta haifa Wanda Basira tana da aure da Yarta Daya,Basiru Kuma ya Gama NCE teaching yake Yi a secondary school, a gidan Basira Muka kwana,Daga Basira Da Basiru Iya kauyenmu na Asali ta dawo ta Auri Babana wato Ahmad Ana ce Masa Malam Amadu,tana Haifa ta ko yayeni ba a Yi ba ta fita ta Auri Dahiru Bayan an yayeni, a Hannun Dahiru Roni ta Haifi Ameera da Mustapha, Ameera ma an kusa bikinta a Haka,bayan Nan Hadeja ta dauke Ni Muka je gidan Tsohon mijinta Dauda tana da Yan matasan Mata Jamila da Kubra,duk inda muka je Ana bamu Dan Alheri muka dawo kusa da Garinmu Muka ya da zango gidan Buhari wajen Yan Kanne na Sakina da Kabir,kwana biyu muka Gama zagaye muka dawo Wanda yaran Iya basa zuwa ko sunce zasu Zo basa zuwa karya sukeyi basa taimaka Mata da komai sai in taje a bamu Dan abinda ya samu,kowa yasan Aure Auren Iya ba Wanda ke damuwa.

 Wace ce Ni Rumaila?

Mu Asalin Fulanin Yola Adamawa ne Amma rayuwa da tashi irin na Fulani Babana Ahmad Wanda aka Fi sani da Amadu dukkan Danginsu kakanni Jigawa state Suka dawo tare da shanunsu da dabbobinsu karkashin Birnin kudu rigar Manu,Babana Ahmad su Uku ne a wajen Iyayensu Ahmad shine Babba sai Sulaimanu sai Kuma Autarsu Rafia,Iyayensu da kakanni basuyi tsawon Rai ba Allah ya karbi rayuwarsu sai Yan Uwansa Sulaimanu da Rafia,Bayan Auren Rafia wurin Haihuwa ta rasu Suka koma daga shi sai kaninsa,Sunyi karatun Addini sosai sannan suna kula da shanunsu na gado shi da kaninsa har sukayi Auren fari tare rana Daya Affa na Ya auri Matarsa ta farko uwar gidansa me hankali da hakuri Maryam Ana ce Mata Mairo,Shi Kuma Sulaimanu Kawu na ya Auri Aisha Ana ce Mata shatu itama ta kirki ce,tunda Affa yayi aure har shekaru Biyar Allah Bai bashi Haihuwa ba shi kuwa Kawu Matarsa har ta Haifi Yara biyu,ganin Haka yasa aka bashi Shawara da ya Kara Aure,Anan Kuma lokacin Iya ta fito Daga Hannun Muzammilu tana zawarci,ganin an tabbatar Hafsatu Iya tana Haihuwa sai Amadu ya Fara sonta ya nemi Aurenta Wanda lokacin ma an gaji da Daurawa Iya aure tana fitowa,mutane Yan tsirari Suka daura Auren Hafsatu da Ahmad,Bayan Shekara da Auren Iya ta samu ciki,Murna wajen Affa ba a magana,ko wata Uku Iya Bata Yi ba Uwargidan Affa Mairo itama ta samu cikinta,Basa kishi suna zamansu lafiya har Iya ta Fara Haihuwar Yarta kyakyawar gaske Fara tas ranar suna taci suna Rumaila,na taso cikin kulawa bulbul Dani wata uku tsakani Mairo itama ta Haifo yan biyu duka Maza ranar suna suka ci Hassan da Hussaini,Daga Nan Kuma sai karayar Arziki ta samu Affa da Kaninsa shanunsu Suka dinga mutuwa Daya Bayan Daya,noma ma idan Suka Yi ba Albarka matayensu Suka Fara Shan wahalar rayuwa ko wata Biyar ba ayi ba Iyata ta tashi masifa ita Bata Zama da talauci Bata gaji tsiya ba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Back to top button