GURBIN IDO

GURBIN IDO 56-60

Da zafi zafi ya dinga hada steps din bibbiyu yana haurawa samansa,yana shiga dakin ya fidda dukka kayan jikinsa,ya rage daga shi sai pant na maza daya sanya kafin ya fita,gaba daya zufa ke karyo masa sosai,bugun zuciyarsa na canzawa,tun ba yau ba yasan kanshi sarai,ta wannan fannin ba kasafai yake da dauriya ba,dabi’arsa kuma ta banbanta data sauran maza,wannan ya sanya ya riga kowa aure a cikin sa’anninsa.

Zama yakeson yi amma ya gaza zaman,sai ya matsa ya diba remote na dukka acn dake falo da kuma bedroom dinsa ya qure temperature dinsu,ya watsar dasu a gefe guda.

Dai dai lokacin da unaisa ke takowa zuwa saman nasa,duk taku daya tana yinsa ne da manufar practical na yadda zata tunkareshi,tana ji a ranta yau komai zai qare tsakaninta dashi,itama zata kai wani bigire da tsohuwar matarsa takai,zata tsallake shingen da take da tabbacin tsallakewarta zuwa nan wajen ne kawai zai bata soyayya da martabar da takeso daga wajensa.

Knocking ta fara yi,abinda yaja hankalinsa ya kuma bashi mamaki kenan,ya zubawa qofar idanu qwaqwalwarsa nason tuno masa waye yayi saura a gidan da xai doshi sashensa a wannan lokaci?,unaisa ya bawa kansa da kansa amsa,sai ya maida wandon pajama dinsa ya nufi qofar kawai kai tsaye,ya mance cewa babu riga a jikinsa.

Mutuwar tsaye tayi sanda sukayi arba dashi,idanunta qur bisa fuskarsa zuwa qirjinsa,wani abu ya soma zagaya jikinta,lallai kaman dai tazo da sa’arta kenan?,batayi qasa a gwiwa ba ta sakar masa murmushi,sannan cikin dabara ta turo qirjinta zuwa gaba tana karkacewa cikin kwarkwasa.

Koda bata ce komai ba shi din ba yaro bane qarami,dai dai gwargwado yasan mata ciki da bai,ya kuma karanci mabanbantan hali da dabi’a irin tasu,uw uba ma ya taba yin aure,don haka daga uya sleeping dress da ta saka a jikinta take tsaye kuma a gabansa ya isa ya gaya masa me take nufi?

“Zanyi maganinki” ya ayyana hakan a ransa yana mata duban baki da wayo,yayin da ita kuma ke masa duban so da kuma sha’awa……..
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 60

Cikin mamaki ta sauke idanunta daga fuskar laulo zuwa kan kwanon da laulon yake ajjiyewa a gabanta

“Gashi inji innarmu,tana gaisheki,wai kuma tana hanya” maganar laulo ta sake jefata a wani mamakin bayan wanda take ciki,duk da haka yuuma batayi qasa a gwiwa ba ta girgiza kai da dan guntun murmushi saman fuskarta

“Haii laulo,yau kuma tuwo ne a idanunka ka mance da dakin daada ka kawo aiken nan?” Kansa ya girgiza

“Nan inna tace na kawo,dakinki yuuma” mamakinta sake ninkuwa yayi fiye da dazu

“Ni kuma laulo?” Kai ya gyada

“Eh ke”, kafin ta sake samun damar cewa wani abu yaron ya juya ya five abinsa.

  Har sai daya baceea ganinta sannan ta dawo da dubanta ga kwanon,lafiyayyen dambu ne daya wadata da kayan zogala da gyada,maida murfin tayi ta rufe kana ta matsar da kwanon gefe cikin tantama,zuciyarta na bata za'aje a dawo.

  Tasan babu wani abu da ya hadata da innar da har zata nanngo abinci irin wannan ta kawo mata,tabbas laulo shirme yayi,zaya kuma dawo,da wannan tunanin ta tashi ta shiga sabgarta na kula da sanwar abincin daren data dora.

    Dai dai sanda ta sallame sallar la'asar inna fureran ta kwada sallama  a tsakar gidan nasu,gaba gadi ta kuma tako sassan dakin yuuma,ba tar data waiwaya ta kalli sashen daada ba.

   Sauraren isowarta yuuma tayi,fuskar inna fureran fal fara'a tayi sallama ta danno kai

“Anata sallah hajiya yuuma?” Cike da qarin wani mamakin tace

“Eh la’asariya ce na idar,maraba furera” ta fada tana ware mata babbar lallausar daddumar dake gefanta,wadda duk cikin siyayyan da anni ke mata ne.

Zama inna fureran tayi tana qarewa dakin kallo a fakaice,wannan shine kusan karon farko data shigo dakin a lokaci irin wannan kuma a nutse tayi zaman dirshan, komai na dakin yuuma me kyau ne,batajin kaf rugar tasu za'a samu daki ya nata,babu ko shakka maimunatu nacan a muhallin daya kere wannan din,lallai ko zata samu kudi babu ko tantama a wajenta

“Barkanmu da almuru” yuuma ta fada ganin irin kallon da takema dakinta,sai tayi caraf ta amshe

“Barka kade yuuma,ina wuninmu?” Gaisawa sukayi,itadai yuuman nata saurare,saboda ta tabbatar ruwa baya tsami banza.

  Shuru ne ya biyo bayan gaisuwar tasu,sai da yuuma tace

“Saiga laulo da dambu yayo batan kai dashi ya kawo dakin nan” bakinta har qeya tace

“Kai haba,ba batan kai bane wallahi,dai dai yayo,ke nace ya kawowa” cikin mamaki ta jinjina kai

“Ni kuma?,harda wahala haka furera?na tsammaci na daadar himu ne”

“Babu komai fa,banda abun yuuma ai mun xama daya,daada?,ai wata kusan tafi kusa,ai yanzu munfi kusanci da ita akan ke”

“Gaskiya ne,gashi kuma naga ta fita”

“Dama.ba wajenta nazo ba,wajenki nazo mu sada zumunta,tunda jininki ya auri jinina kuma ai yanzu dangi muke ni dake yuuma” inna furera ta fada tana ta gyara zama kamar wadda ke zaune akan qaya

“Gaskiya kam” yuuma ta amsa mamaki yana kasheta,kafin ta fita a wannan mamakin kuma sai taji inna furera ta fashe da kuka,cike da wani zallar mamakin da kuma tsoron kada ta qulla mata wani sharrin take kallonta

“Toooo…..subhanallahi, meye haka furera?, lafiya?”

“Dole nayi kuka yuuma,dole nayi kuka,kusakuren dana tafka wa yarinyar nan maimunatu,kiga yadda ta gujeni,aka dauketa daga wajena aka aurar da ita a wani waje daban,har yanzu bata waiwayeni ba,ni kuma bansan muhallinta ba bare naje na nemi yafiyarta” sai ta kama habar zaninta tahau fece majina.

    Dariya hade da mamakin furera suka kama yuuma,saidai ta danne kawai taci gaba da kallonta tana cewa

“Allah sarki,ai sai a godema Allah da yasa aka gane kuskuren da akayi,alhamdulillahi,Allah ya yafe mana”

“Ameena….ameena” ta shiga amsawa tana sharce hawaye,wanda kusan hawayennata dukka akan naggenta da suka dinga mutuwa ne,asarar data tafka.

     Sai data gama dukka koke kokenta ta miqe zata tafi sannan tace

“Umm….nace ba,ai sai a bani kwatancen gidan nata,can inda take a gomben ko?,sai a leqa aga dakin nata,a kuma nemi yafiya,bai kamata a matsayina na uwar riqonta ba kuma ya zamana bansan inda mazauninta yake ba”

“Tooo….anzo wajen” yuuma ta fada,ta shafa addu’ar da takeyi sannan tace

“Yanzu kam bana ce miki ga inda muhallin maimunatu yake ba,tunda ba zuwa nayi ba ko sanda ake bikin,ban samu na leqa ba” gaban inna furera ya fadi,har yanayin fuskarta yadan sauya

“To,ikon Allah,to kuma su can gidan surukan nata fa?” Kai yuuma ta sake girgizawa

“Shima bana ce ba,tunda nafi shekara rabona da garin gombe,sannan koda can ma kinsan ba ni nake kai kaina ba,yafendo ke aikomin da mota ta daukeni daga nan qofar gidan zuwan wancan” shuru furera tayi,ga qoshi ga kuma kwanan yunwa,yanzu ya kenan?.

“To ai inaga ta zo da sauqi ko,me zai hana ki waya da ita ki gaya mata surukarsu nason ganin dakin diyarta,idan yaso nima basai motar tazo ta daukeni ba?”. Binta da kallo yuuma tayi galala,sai kuma ta gyada kai

“Haba furera,dama dai na tashi zuwa ne”

“Zan iya jiran tafiyar taki indai ba zatayi tsaho ba”

“Allah ya bamu aron rai” ta amsa mata a taqaice,sabida takaicinta daya fara kama yuuma,murna ta cika inna furera

“To alhmdlh,don Allah a qoqarta muje anan kusa yuuma,na gode Allah ya qara zumunci” ta fita tana zabga mata addu’a tare da hango nesa a kusa,duk daba haka taso ba,so tayi gobe ko jibi ta dage.

    A tsakar gida sukayi kacibus da daada,sai tabi fureran da kallo cike da mamakin abinda tazoyi gidan,harara suka zabgawa juna,inna furera tayi gaba tana yada habaici

“A hayye na gaba kam ai yayi gaba,na baya ko tsintar hula ba zaiyi ba,yo mu da muke jinin sa’a da nasara,haihuwa me rana,ta jefa mu gidan arziqi,ai an rabu ne kuma ba’a rabu ba,yuuma gidan karamci” sak daada tayi tana duban dakin yuuma,ta sani cewa yuuman ba munafuka bace,da sai tace wani abun suke qullawa,hakanan ta san yuuman bata daukar raini ko cin kashi bare tace zata je tayi mata tatas kan ganin furera da tayi cikin gidan,amma duk da haka sai ta kasa daurewa,ta ajjiye faifan dake hannunta ta nufi dakin yuuma.

 Yuuman na tsaka da nade abun sallah daadan ta shigo,ta daga kai ta dubeta

“Mamaki nake yuuma da ganin fitowar furera a dakinki,me tazo yi?” Tambayar sai ta bata mamaki da haushi,salon yadda tazo mata da maganar mai kama da titsiye

“Kunfi kusa ai,nima tare na ganku,sai kije ki tambayeta ai” daga haka taci gaba da aikinta,shuru daada tayi,don bata da sauran ta cewa,sai kuma ta juya ta fice daga dakin sukuku,yuuma taja qaramin tsaki,sun dauka ita din sakarai ce da zata biyewa shirmensu daga ita har fureran?,kallonsu kawai takeyi amma tasan halin kowa.

    A hanya fureran keta sumbatu ita kadai,Allah yasa dai kada yuuma taja mata lokaci ko kuma taqi zuwa da ita

“Idanma taqi idanuna zan murje na tafi gembu,nayi musu kwance kwance har sai na samo kwatancen gidan,don ko da tsiya koda arziqi saina fanshe wahalata,ato” da wannan tunanin ta koma gida hankalinta kwance.

Tunda hajiya munubiya ta tafi take ta juya maganganun da sukayi da ita,ranta ke mata wani irin ciwo da suya,sadakarta aka bayar shine abu mafi ciwo da qona rai a wajenta,musamman da hajiya munubiyan ta gaya mata dukka familyn dr khalid akko kallon da suke mata kenan,zuwa yanzun ta soma gasgata cewa amma da anni basa qaunarta,don ta lura da wani kulawa da soyayya ta musamman da suke nunawa maimunatun tun zuwan da sukayi a shekaran jiya,sannan abubuwan da suka afkun da yadda aka turata kitchen hado masa abinci maimunatu na zaune, bayan itace qasanta,ta fita daraja ta fita mulki da kudi,babu ko tantama akwai abinda aka kitsa a shigarta kafin ta fito

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button