GURBIN IDO 56-60
“Bari na baki wani sirri guda daya,kinga wannan mijin naku,a gabanmu ya tashi,babu wani hali da dabi’arsa da bamu sani ba,bari kiji,indai kinaso ki tsira da mutunci da martabar ki,to karki ragawa kowa,ki tsaya a tsayenki sosai,ki nunawa kowa ke din daga madaukakin gida kika fito,shi kuma ja’afar,kada ki yarda ki bada kanki ta sauqi,mutum ne shi da ya tsani yaga ana nuna masa soyayya,ke ko matarsa data mutu wadda ya kusa zama mahaukaci a kanta ko nace yama zama…..don duka yake wani lokaci harda cizo idan ciwon ya motsa masa…..” tsoron da unaisa bata taba jinsa ba yanzu ya darsu a ranta,zancan da aketa fada wai wai yau sai gashi daga bakin matar qanin babansa
“Eh….Allah dai ya kiyayeku kawai ya tsare kada wata warana ya illataku…..ina gaya miki,ita kanta baqar wahala tasha a wajensa saboda nuna masa soyayya da tayi,to ki watsar dashi,kija girma da mutuncinki,ina gaya miki idan na rantse ko kaffara banyi,idan ya fahimci kedin babbace kuma me aji,da kansa zakiga yana shanshanarki,a nan zaki murza zarenki yadda kikeso” sanda ta yima anty talatu wannan bayanin cewa tayi
“Ban yarda da maganganun matar nan ba”
“Saboda me anty?,don me zata zo ta gayan qarya ko ta shiryamin zance?,bayan suna da alaqa dashi?,ita ba kishiyar babarsa ba bare nace qiyayya da kishi ya sanyata aikata haka ba,sannan ba mai jini a jiki bace bare nace sonshi take take shiryan gadar zare,hasalima ‘yarta daya kuma an sanya ranar aurenta,saura watanni biyu bikinta,bamu taba gamuwa ba sai ranar dana kai qararshi gaban anni, gida zata tafi amma saboda ni ta tsaya,da qyar ma nayi convincing dinta tazo gidana mukai wadan nan maganganun” wannan hasashen na unaisa ya sanya anty talatun itama hankalinta ya karkata
“Kuma gaskiya kika fadi,mu jarraba mu gani din”.
Ajiyar zuciya ta sauke tana komawa inda ta tashi dazun ta zauna,tana lissafa adadin kwanaki ko watanni idanma ta kama shekarar da zatayi kafin ja'afar yazo hannunta,tabbas zata tsaya akan kowa har sai sun fahimci girma da martabarta,amma batajin zata iya daukewa ja'afar qafa,babu tabbas.
[