GURBIN IDO

GURBIN IDO 61-65

       K'arfe tara da minti ashirin ta kammala komai harda break fast dinsu,ita dince kawai.batayi wanka ba,tun jiya bata ganshi ba,tana daki dai ya shigo sunyi magana da amna,kafin ta fito sun gama ya fita,kamar ta shareshi amma sai taga bai kamata ba,kodon diyarsa dake qaunarta,don haka ta dauki kwando ta shirya komai dai dai da yadda amnan zata iya dauka

“Muje na rakaki ki kaiwa daddy” daman zaman jira take,ta kuwa sauko da saurinta,maimunatu ta dauki kwandon suka fito tana tsokanar amna,kada dai ace daddy ya tafi ya barta,ta qyalqyale da dariya

“Daddy baya fadin alqawari fa ya saba anty” kai ya jinjina tana murmushin yadda yarinyar tasan halin mahaifinta,duk da shekarunta basufi hudu ba.

Daga second matattakala ta biyu ta tsaya ta miqa mata kwandon,sai ta tsaya tana duban amnan tana ci gaba da haurawa har takai qarshe sannan ta sauke idanunta daga kanta tana juyowa don barin wajen taje ta qarasa abinda batayi ba.

Waiwayowar da zatayi suka hada ido ta ita,sanye take cikin wanu straight leg trousers da shirt spaghetti hand,siriryar silver chain ne a wuyanta da qaramin dan kunne barima, qafarta high hill ne,fuskarta ta wadata da makeup sosai.

Kallon kallo suka yiwa junansu,sa’annan unaisan ta zarce da yima maimunatu kallon qurilla daga sama har qasa.

Wasu soft nigh gown ne a jikinta farare tas tas kamar ba dasu ta kwana ba, gashinta mai laushi da santsi nannade cikin wata hula me zubin shower cap,kwantacciyar qananun sumarta ta gaban goshinta zuwa qeya dukka ta fito ta sake qawata fuskarta kamar ba daga bacci ta tashi ba,jikinta na fidda qamshin turaren baccinta data jima da warewa musamman saboda bacci kamar yadda afra ta koya mata,fararen santala santala hannunta dukka a waje suke saboda yanayin hannun rigar dan qarami ne sosai, tsintsiyar hannunta cike suke da duwatsuntan nan asalin wadanda ta gada daga daadarta,ko sau daha bata taba sha’awaf ciresu daga hannunta ba,sai suka kuma sake mata kyau suka haske farar fatarta dake luwai luwai fes kuma jajir da ita,kullum duwatsun kamar sake gogesu akeyi saboda sheqin da sukeyi,qafarta wani farin slippers ne mai taushi da aka yiwa wani adon gashi gashi daga sama.

Da qyar unaisa ta hadiye wani abu me tauri,haushi sosai ya cikata ganin yadda maimunatun tayi gaggawar dauke idanunta daga kanta tayi gaba kamar batasan wacece ita din ba.

“Agwai” ta kirayeta da sunan da tasan zai bata ranta,sai tayi kamar bata jita ba ta sakeyin gaba

“Hey dake nake magana” nan ma shuru,taci gaba da takawa zuwa sassanta,zuciya ta ingiza unaisan,sai tayi saurin takawa ta kuwa sha gabanta

“Don baki da kunya kina ji ina miki magana?,wato kin samu sake saboda kina zaton kin hada miji dani ko?,mijin da kike hoto a wajensa?,ba kowan kowa bace ke illa ‘yar qauye mazauniyar riga,ki kiyayeni wallah,bakisan wacece unaisa ba,diya ga ministern ilimi” wani kallo maimunatu ta watsa mata,karon farko tun zuwanta gombe da taji wani ya bata mata rai,har ran nata ya sosu har haka

“Duk da nike bafulatana amma ban taba daukar tallan nono ba har kawo rana irin ta yau,kiwo kuwa wannan ado ne ga dukka cikakken bafulatani,koda ma ace nayi tallan nono ai ba aibu bane ba kuma gazawa bace,saboda dan halak baya manta tushe,tushiya kuwa masomin dukka wata daawa ce da tayi tsiro ta fito al’umma ke kallonta……” Daga wannan ta kewaye unaisa ta qarasa shigewa falonta ta kuma rufe qofar ta abinta,take unaisa ta sake hasala,sai ta juya zuwa stairs din ja:afar,sai kuma ta sake ja ta tsaya,idan ta hau tace masa me?,kada mutuncin ta ya zube a idanunsa,bari,zatayi dealing da yarinyar a cikin gidan da kanta,dole tayi.laushi,kuma dole tayi mata biyayya,badai tafiya zaya yi ya barsu ba su biyun a gidan ba?.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 64

Da murmushi suka dubi juna ita da fatiman,ta bata hannu sukayi musabaha sannan suka fara gaisawa,fatima na matsa mata gefenta ta zauna,amna na saman qafafunta.

Cikin mintunan da sukayi suna jiran lokacin tashinsu ta sake sabawa sosai da fatima,kamar su dauki shekaru tare,tana da sauqin qai da kuma yawan hira,ta dauki maimunatu kamar mate dinta,duk da ta bata aqalla shekaru uku,don ita ta rufa shekara ashirin,wannan yasa maimunatu ta sake sosai,suka shiga hira da fatiman,suna baiwa juna labarin makaranta,duk da fatiman ta gama secondary school,yanzun haka tana 200level ne.

Tare da fatiman suka shiga jirgin,sai itama ta duba jikin boarding pass dinta kamar yadda taga fatima tayi ta laluba seat number dinta.

A hankali take dubawa har ta iso gurin,tuni daya kujerar wadda ita ke bakin window me ita yana zaune akai,saita juya tana duban inda su fatima ke zaune,ita da amna ne seat number dinsu daya, jabir kuma da ja’afar wadanda seats daya ne suka rabasu,batasan tsarin jirgi ba,tunda ba sabawa tayi da shiga ba,don haka ta zame qaraman jakar dake kafadarta ta zauna saman kujerar bakinta dauke da bismillah.

A hankali ya waiwayo yana dubanta,matashin saurayine wanda duka duka bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba,kana kallonsa zakasan wayewa da hutu sun ratsashi,unexpected ya ganta a kusa dashi,sai ya tashi ya zauna sosai idanuwansa a kanta,duk yadda yaso basarwa amma ya gaza,cikin muryarsa dake nuna zallan iyayi yace

“Sannu ‘yammata” a hankali ta waiwaya ta kalleshi,sai ta dauke kanta tayi gyaran murya kawai ba tare da tace komai ba, shima sai yayi shurun,amma kuma lokaci lokaci yana waiwayowa ya kalleta,saidai ta basar,ta kuma tsuke fuskarta da kyau,kamar yadda ko sau daya bata waiwaya ta dubeshi ba.

     Tunda ta zauna a seat dinta ya fuskanci wanda yake abokin xamanta hankalinsa ya gaza kwanciya,kunnuwansa naga jabir ne dake ta masa bayanin wasu receipt da suka biya kudin wasu clearance a wajen custom's,saidai dukka hankalinsa yana kanta.

     A hankali yaji kamar ana matsa zuciyarsa sanda ya fahimci saurayin yana yawan juyawa yana kallonta,ya dinga qoqarin dannewa da kuma kauda hankalinsa amma sai ya gaza,agogon hannunsa ya daga ya kalla,akwai awa kusan biyu a gaba kafin jirginsu ya sauka a lagos,sai yaja wani dogon tsaki,abinda yaja hankalin jabir kenan,sai a sannan ya fahimci bama fahimtar bayanin nasa yake ba,yakai idanuwansa inda ja'afar din ke kallo,sai a lokacin ya gane abinda ke faruwa,cikin taqaitaccen lokaci jabir ya qare masa kallo,hatta zamansa bai zauna properly ba,kamar wanda taushin kujerar bai masa ba,amma da alama duka bai fuskanci hakan ba shi.

      Gimtse dariyar dake son qwace masa yayi,ya buda baki zaiyi magana dai dai lokacin ja'afar din ya dunqule hannunsa ya buga a hannun kujerar da yake kai

“It can’t” ya fadi yana miqewa zumbur,ya taka a hankali ya fito daga inda yake ya nufi wajensu.

       Cikinsu ba wanda yasan da wanzuwar tasa a wajen,dai dai sanda saurayin ke qoqarin miqa mata tissue ganin ta rufe bakinta atishawa nason fita,ido hudu sukayi da ja'afar dake tsaye a kansu,ya goye hannuwansa a qirjinsa ya zuba masa wannan idanun nasa dake saurin ladabtar da kowa,wasu kibiyoyi da baisan suna fita a idanunsa ba nata spark.

         Sosai kallon da yake masa ya dakeshi ya kuma yi masa kwarjini,sai ya janye tissue din bakinsa na subucewa da cewa

“Lafiya?” Cikin fargaba tare da tunanin qila matar aure ce kenan,tunanin da baizo ransa ba sai a lokacin,maganar da yayin tasa maimunatu daga kanta,suka hada ido,sai ya mata inkiyar ta tashi,yayi gaba,ta miqe tana sake saqala jakarta ta biyo bayansa.

       Kafin su iso jabir har ya miqe yabar mususeat din,dariya kaman zata kasheshi,ya koma inda ta taso din,saidai koda hakan shima ya taya J dinsa kishin da yaketa qaryata kansa bashi yakeyi ba,ya dubi matashin

“Ku dinga hankali da matan mutane” ya fada yana jifansa da wani kallo me kama da harara,don shi din dama yafi ja’afar magana.

Shi daya ya dinga quncin rai,yaja tsaki yafi a qirga,ita dai bata dashi komai ba,har awannin da suka rage musu ya cika jirgi yayi landing a lagos cunkus dakin tsumma.

Motar kamfaninsa ta nan lagos ce tazo daukarsu wadda aka tanadar masa saboda irin haka dama sauran mamyan baqi da sukeyi daga qasashen waje abokan kasuwancinsu,already jabir ya musu booking na dakuna a daya daga cikin five star hotels,wanda kuma yafi kusa da inda sukazo duba ayyukansu,ciki da falo ya kamawa su ja’afar saboda amna,shi da fatinsa kuma single room.

To tun saukarsu lagos basu samu zama sosai ba,idan motar company tazo ta saukesu tun safe sai dare,wannan ya bawa su maimunatu damar yawo sosai cikin garin lagos,jabir yasa wata motar daga company musamman take zuwa duk sanda suka gama shirinsu ta daukesu tayita zagayawa dasu guraren shaqawatawa kala daban daban,ya tura musu enough kudi ta account din fatima,ga kuma bandir da J ya ajjiye mata itama,basu da wata matsala ta komai,duk yadda maimunatun tayi tsammanin ba zataji dadin tafiyar ba sai abun yazo mata akasin hakan,taji dadin garin fiye da zatonta,sunyi yawo sosai,hakanan fatima ta musu siyayya mai yawan gaske,musamman maimunatu da batazo da wasu kayan ba,saidai kuma ita fatiman kusan duka qananun kaya ne siyayyar nata,sai sakakku da zata iya fita dasu cikin gari,don haka maimunatu ta ware kowanne jaka daban,wandancan da takejin ba zata iya fita dasu ba,da kuma wadanda zata iya sakawa.

Duk yadda garin ke mata dadi amma bata mance da lissafin lokacin komawarsu makaranta ba,sunyi waya da afrah itama tana sake tuna mata

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button