GURBIN IDO

GURBIN IDO 61-65

“Allah ya nuna mana,amma bana gida ma,muna lagos,kuma banga alamun dawowarmu ba” dariya sosai afra ta sake

“Wannan abu yayi min dadi,tsuntsun soyayyar ya fara sauka kenan,honeymoon aka tafi ne?” Kamar tana gabanta saita saki harara

“A’ah milkmoon aka tafi,tare fa muka tafi da amna,harda su fatima”

“To sai me?,bikin magaji zai hana na magajiya ne?,amna ina ruwanta?,zatafi kowa son a bawa daddynta kulawa,fatima kuwa na tabbatar saidai ta tayaki,kuma nasan ba daki daya kuke ba,kidai zauna garin kallon ruwa kwado yayi miki qafa”

“Mtsweew,Allah ya shiryeki afrah,gwara hajja tayi miki aure ta huta”

“Wallahi ko gwara a aurar dani a huta,idan ba haka ba…….”

“Ba’a kunne na zaki qarasa wannan zancan naki ba,ya girmi kunnuwana” saita datse wayar tana dariya.

        A hankali ta aje wayar a gefanta

ki tsaya dai kallon ruwa kwado yayi miki qafa,wai me yasa kowa maganarsa kan ja’afar ne,kowa kusan abinda yake fadi mata kenan idan irin wannan zancan ya hadusu,sai ta sauke ajiyar zuciya,idanuwanta na hango mata kalar soyayyar jabir da fatima,wata irin soyayya me nuna zallar kulawa da kuma shaquwa,ita kanta abun yana burgeta,sau tari idan ya kirata bayan ya fita tunda yawancin lokutta suna tare,sai tayi kasaqe tana sauraren kalar hirarsu,ta fahimci ita kanta fatiman ta gano kalar zamansu,don wani lokaci ta taba cewa da ita

“Shi namiji da kike gani,babu abu mai sauqi wajen sarrafawa irinsa,sau tari dama suke nema ko jira ka basu,mijinki ko?,hmmmmmm,astagfirullah,soyayyarsu ta dabance,duk sanda suka tashi nunawa mace soyayya za’a sha mamaki,saidai suna da wani irin aji da kamewa,wanda zaisa ki gaza fahimtar inda suka dosa” ajiyar zuciya ta sauke tana gyara kwanciyar rub da cikin da tayi saman kujerun falon,amna na daki tana bacci,dama a ciki suke kwana ita da ita,shi ya canjesu a falon.

          Qarar security na jikin qofar taji,kafin kuma ta ankara an murda handle din an turo qofar,sai ta daga kai da sauri don ganin wanda ya shigo din,saboda ta san wannan ba shine lokacin dawowarsu ba,zata iya cewa tun zuwansu tsahon kwanaki takwas yau,sau uku kawai suka hadu ita dashi,tana qunshe a daki sanda zai fita,kafin ya dawo ta tattare tayi kwanciyar barci abinta.

       Tun kafin ya saki handle din idanunsa ke manne a kanta,wata gown ce a jikinta ta wani material maras nauyi,wannan yasa kwanciyar rub da cikin da tayi ya bayyana mazaunai da qugunta sosai.

        A hankali idanuwansa suka kai kai,ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na zubawa,sai ya juya ya maida qofar ya rufeta,sannan ya soma takowa cikin dakin bakinsa dauke da sallama.

    Tuni ta miqe ta zauna kanta a qasa tana wasa da yatsun hannunta,itakam dawowarsa a yanzun kamar takura ce a wajenta,dole saidai ta koma daki tayita zama

“Sannu da zuwa” ta fada a hankali tana miqewa tsaye duk da bataji ya amsa ba,taku biyu tayi taga ya babbake gaba daya hanyar wucewarta,idanuwansa a kanta,yau din kallonta tsakiyar idanuwanta yake kansa tsaye,ya karkatar da wuyansa gefe daya yana son hukuntata da idanun kamar yadda ya saba

“Am…zan zan wuce” ta fadi muryarta nadan rawa,saboda jiki da zuciyarta da taji sun fara amsawa

“Idan naqi fa?” Ya amsa mata yana hade fuskarsa,mamaki amsar da ya bata ta bata,sai ta dan tsuke bakinta kadan kafin ta sakeshi,idanuwansa suka kai kai,ya sake jin wani abu na sauka a dukka sassan jikinsa,yana kuma gauraya da gajiyar daya kwaso,idan yace pink lips dinta basa burgeshi yayi qarya,qara taku uku yayi qwarara sai gashi a gabanta jikinsu na gogayya waje daya,kafin ta qara wani tunani ya sanya hannuwansa ta baya ya dorasu saman mazaunanta,take a kuma lokaci guda kowanne numfashinsa ya fara barazanar daukewa na wucin gadi,namiji ne shi tsayayye,ita kuwa mace mai rauni,wannan yasa fa gaza tsaiwa a muhallinta ta fada jikinsa gaba daya,kafin ta samu ta fusgo numfashin nata,ta fara qoqarin raba jikinta da nashi,amma tayi latti,don ya zagaye bayanta da hannuwan nasa gaba daya.

        Ji yake kamar an jan jininsa da na'urar lantarki mara zafi,wani irin shock yakeji sosai,gudun zuciyarsa ya fara rawa

“Hope ba da irin wannan kayan kike fita ba?” Yayi maganar yana dagata daga jikinsa,muryarsa na wani irin fusga,kamar zata narke a wajen haka takeji,kanta a qasa ta gyada masa kai,fiye da rabin hankalinta yana kan qofar daki,kada amna ta fito,ilai kuwa sai ga qaran qofan bude dakin,ba tare daya juya sashen ba yaja da baya ya sulale saman kujera

“Hadamin ruwan wanka” ya bata umarni karo na farko kenan,don da kansa yake hadawar.

       Kamar qafafunta ba zasu iya daukanta ba haka ta jasu tayi ciki,amna kuma ta fito tana masa sannu da zuwa,a jikin bangon toilet ta jingina bayanta bayan ta kunna ruwan tana jiran na dumi ya sauko,kowanne sashe na jikinta ya zama week,wai me yasa?,me yasa irin hakan ke faruwa da ita?,tuno irin wani sassanyan qamshi gami da laushin daya ratsa fatarta tayi lokacin da ta isa ga jikinsa,kawai sai ta goye hannayenta aqirji tana matse jikinta waje guda kamar me jin sanyi.

       Ta gama hadawa ta juyo ta kama handle din da nufin bude qofar sai aka rigata shigowa,ja'afar dinne,sanye da trouser dinsa da fara qal din singlet dinsa kamar ba'a sanyawa jiki ita,ya cika qofar ya kuma taho gaba daya,so babu wani space da zata rabeshi ta fice,dole ta janye da baya har ya shigo,idanuwanta na kallon qasa,don ba zata iya kallonshi a haka ba,tsoro yake bata,gaba daya dantsensa wasu irin muscles ne dake nuna yadda ya qware wajen motsa jiki da kuma daga qarfe,daga hannuwansa zuwa qirjinsa duka sun bayyana albarkatun gargasar dake tattare da wajen.

     Ta dauka zai janye mata ne,sai taji ya maida qofar ya rufe,ya kuma fara zare singlet din da tayi saura a jikinsa,da saurinta ta qara gaba tana yunqurin bude bandakin,saidai ya saka lock a jiki,ta saka hannunta zata murza ta bude,ta tsinci husky voice dinsa na mata gargadi

“Karki sake ki budeni,am taking bath” tashin hankali,sai taja da baya ta sake jingina da bangon zuciyarta na wani irin bugawa cike da tsoro,to wanka zaiyi itama wankan akace masa zatayi?,tsoro ya sake kamata ganin yana zare trouser din jikinsa,ta rasa a wanne side zata tsaya ba tare da taga kominsa ba?, kowanne sashe na bandakin glass ne da zai baka damar ganin abinda ke faruwa a kowanne bangare da bandakin,kota juya ma gabanta glass ne,idan kuma tace shi zata fuskanta ba?,inaa,ba zata iya tsaiwa gabansa bama,sai ta runtse idanuwanta gaba daya hawaye na taruwa cikin idanun nata.

      Rufe idanuwan nata ya bashi damar kallonta son ransa,ba abinda yake fuskarsa irin qirjinta dake cike sosai,ya kuma zauna ta cikin rigar saboda wata tattarar roba da aka yi mata daga sama, qaramin murmushi na gefan baki ya sake sanda ya fidda trouser din saboda yadda yaga ta cuno baki gaba,komai nata akwai childishness a ciki,some times ba abinda take tuna masa illa lokacin amarcinsu irin wannan shida shaheeda,tana tuna masa abubuwa masu yawa tattare da ita,ko a yanzun sai yake gani kaman ita dince.

     Rataye trouser din yayi,pants na maza ne kawai ya rage a jikinsa

“Miqomin sponge” kamar ya mata tsawa a tsakiyar kanta haka taji,ta yaya zata iya bude idanuwanta ta kalleshi a haka?,sake maimaita mata yayi,sai ta fara tattakawa a hankali tana lalube ba tare data bude idanunta ba,qaramin murmushi ya qwace masa ganin ta saba hanya,tana ta lalube har arean da yake tsaye,sai ya zuba mata ido ya rabu da ita,baice mata komai ba har zuwa sanda ta damqi hannunsa.

      Saki taso yi da sauri amma cikin zafin nama ya riqeta,ya kuma janyota cikin jikinsa gaba daya,yayi mata rumfa da yalwataccen qirjinsa,ya kuma lullubeta da tattausar fatarsa,matseta yayi sosai cikin jikinsa wani numfashi mai nauyi yana qwace masa ba tare da ya shirya ba,wani irin body contact ya samu da ita irin wanda bai taba ba,tudun mazaunanta ya taba sashe mafi kima a jikinsa.

      Rasa abinda zatayi yasa gaba daya ta qanqameshi ta cusa kanta cikin qirjinsa bayan ya juyo da ita suna facing juna,hawayen da take boyewa suka sauka suka fara ratsa gargasarsa suka tadda fatarsa,dagata yayi kadan daga jikinsa yana duban fuskarta daya danyi jaa,ya lumshe idanuwansa da suka fara sauya kala saboda wani abu data harbawa kowanne sashe na jikinsa,siraran lips dinta na motsawa a hankali,sai ya sanya fuskarta a tsakiyar tafin hannunsa yana ci gaba da kallon labbanta,baya jin yau zai iya skipping komai da komai,for now yana jin komai nasa yana developing,kamar ana dawo da old version ne na ja'afar daya dade da bacewa wasu shekarun baya da suka shude.

         Shi kansa baisan yadda akayi ba ya tsinciki labbansa saban nata,yadda ya zacesu haka ya samesu,da wani irin dumi da kuma sulbi don bazaice taushi ba,abinda ya sake tabashi kenan sosai,ya kuma haukatashi sai yayi amfani da harshensa ya buda bakinta sannan ya zura harshen a ciki.

         Wasu irin hot kisses daya jima da kashesu a duniyarsa ya dinga bata,ciki da wajen bakinta ba inda bai tsotse ba,da zafi zafinsa yake aiwatar da komai,zafin da ya bayyana har cikin fitar numfashinsa dake sauka saman hancinta,take kuma shaqarsa zuwa huhunta,tana fiddo masa da nata numfashin shima yana aikawa nasa huhun,abinda ya sake haifar musu da wanu irin dimuwa gaba dayansu,gaba daya ta gama rudewa,jikinta duka ya dauki rawa kamar wadda zazzabi ya kama,wani irin baqon yanayi ne da batasan dashi ba,bata kuma taba kawowa zai risketa ba,ta sanya hannunta itama gaba daya ta kama kansa ta riqe tana son janyeshi daga fuskarta,saidai bata da wannan qarfin,ta rasa yadda zata rabashi da kanta kamar ma sake shige mata yake,kawai saita saki hawayenta suka soma zuba sosai.

       Danshinsu ya taba fuskarsa,ya kuma sanya a hankali komai ya fara sakinsa,ya zare bakinsa a hankali,yana kuma dawowa cikin hayyacinsa,a nan ya tuna me ya aikata?,tsananin qarfin hali irin na namiji sai ya hade fuskarsa bayan ya janyeta still yana dubanta

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 63

Ta ja tsaki ya kusa sau goma sanda ta koma sassan nata,batasan abunda yasa abinda unaisa tayi matan yayi mata zafi sosai a ranta ba,bedroom dinta ta fara qoqarin gyarawa,sai ga amna ta turo qofa ta shigo,ta waiwayo tana dubanta,sai taga ran yarinyar a hade tana tura baki

“Lafiya amnee?”

“Waccan antyn mana,wai don ta kirani banje ba shine ta harareni” sakin duvet din da take take ninkewa tayi ta kama hannunta

“Manta kawai,ke da zaku tafi da daddy,kullum kuna tare?,me zai dameki” murmushi ta sauke

“Yauwa yace kizo” sakin hannun amnan tayi, kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa,batason wasu abubuwan su dinga faruwa gaban idanun yarinyar,yarinya ce mai wayo sosai,akwai abubuwan da ba zata manta dasu ba idan suka farun.

       Closet dinta ta bude ta ciro madaidaicin blue black din hijab ta zira ba tare da ta fidda hular kanta ba,ta kama hannun amnan suka fito.

       Suna fitowa ta hangi unaisan a zaune,ta dora qafa daya kan daya tana girgiza su,da biyu tayi wannan zaman,tanason ta sanya idanu a gidan game da takun kowa,gefanta breakfast dinta ne da bayin nata suka yi suka kuma jere mata.

      Mummunar faduwa gabanta yayi sanda taga maimunatu ta kama stairs din tana hawa,suna hira kuma tartar da amna abinsu,miqewa tsaye tayi,tayi kamar zata bisu take wata zuciyarta ta tsawatar mata

“Karkiyi,ba girmanki bane” sai ta koma da baya a hankali ta zauna, zuciyarta na mata wani irin suya,dole yarinyar ta samu zarrar tsayawa ta maida mata magana,tunda har ta samu darajar hawa sassan ja’afar din,kai tsaye har haka?,ja’afar fa?,tasan ba qaramin abu bane mai sauqi ace ka samu irin wannan damar daga gareshi,damar data dade tana nemanta,wataqil ma sunsan juna sani irin na ma’aurata

“Kai qarya ne,ba zata taba iya dauke wannan qaton ba,duka duka nawa take?,yaushe qashinta yayi qwari,ni na razana na janye bare ita?” Wannan tunanin ya rage mata tashin hankalin data shiga,sai ta koma ta zauna tana jiran taga saukowarsu.

         A bakin dining ta sameshi a tsaye,da alama shima ya gama dukka shirinsa,shirt da trouser ne a jikinsa na kamfanin armani,sai qafarsa dake saye cikin wani rufaffen takalmi na fata slip on,me wani irin qawataccen ado,batasan yadda kayan maza suke ba,amma ita kanta takalmin ya tafi da ita,kayan sun dace dashi sosai,sun kuma fitar da qirar sa sosai wadda suit ke yawan boyewa,kana dubansa zakasan yana shiga gym sosai,short sleeve shirt din ta bayyana baiwar gargasar dake dukka hannuwansa masu tarin yawa.

       Da ita dashi dukka tare suka dauke kansu,dukkansu suna basarwa,saidai cikin jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa,baisan ko baiwa bace,ko ta musamman ce a cikin mata?,duk sanda tatashi a barci sai fuskarta tayi wani fresh,idanuwanta suke garai garai su kuma fito ba.

     Cikin kayan abincin data kawo masa ne yake shan tea,ta tako a hankali tana basarwa,qamshin turarensa daya cika falon yana kada mata hankali

“Ina kwana?” Ta fada da muryarta da ko da yaushe take tuna masa da mafarkinsa,ko a yanzun ma sai daya ji tsigar jikinsa ta tashi

“Kin manta da qa’idata kenan?” Ya fada yana dire cup din hannunsa saman table din,hadi da qoqarin zaro wayarsa da tayi qara na alamun shigowar saqo,kai ta daga kadan ta dubeshi sanda yake kallon fuskar wayar,fuskar nan a dinke tsaf kamar bai taba dariya ba,abinda yasa girarsa guda biyun dake da wani irin shape dake burgeta sukayi kaman zasu hade da juna,sai ta kau da kai tsigar jikinta na zubawa,bata gane me yake nufi ba,kafin ta sake cewa wani abu kuwa yace

“Minti ashirin ya rage mana mu wuce,bakiyi wanka ba?” Idanu tadan fitar tana kallonsa,ta sake gazawa jure kallon nasa kamar ko yaushe

“In…..” Ta bude baki da niyyar tambaya,amma sai ya katseta

“Don kince baki zuwa,sai nabi umarninki,ni dake waye a sama?” Take ta fara abinda ya tsana din,wato hada ruwan hawaye akan fuskarta,ta kuma fara girgiza kanta,murya a karye kamar qaramar yarinya qasa da shekarun su amna ta fara magana

“Kayi haquri,zan rasa makaranta,mun kusa komawa” idanunsa ya kafeta dasu,baisan me yasa yakejin haushi yana kamashi ba idan tayi zancan makarantar nan ba,wato makarantarta tafi komai?,zai tuna mata idan ta manta,matar aure ce ita,mijinta ya kamata ya juyata bawai tunanin komawa makaranta ba,ya kamata taji wani abu a jikinta da zai dinga tunasar da ita tana da igiyar wani,yaga kaman ta shagalta bata tuna haka.

    Kanta yana qasa tana qoqarin tsaida hawayenta,don haka batasan ya iso inda take ba,har sai da turarensa ya shaida mata.

     Kanta ta daga a hankali,sai tayi yunqurinja da baya da sauri saboda rage kusancin dake tsakaninsu,saidai kuma tuni ya kaima hannunta cafka,ya kuwa damqeta da kyau saman duwatsun hannunta.

      Tare suka kai dubansu shi da ita kan duwatsun,a hankali ya sakar mata hannu,sai kuma yayi mata qofar rago,taku daya idan ta qara da niyyar yin gaba ko baya to zata tsinciki kanta kane kane ne a faffadan qirjinsa

“Wipe these tears…..,daga yau kika na sake magana kikamin kuka ko na sake umarni kikamin musu,Allah….Allah…biyu ko?,kalli ki gani” ya fada yana ranqwafowa dai dai fuskarta,kan yin musun yayi magana,don haka ta daga kan nata kamar yadda ya buqata,saida numfashinta ya kusa daukewa sanda taga irin kusa da kusan da sukayi,suka fara musayar numfashinsu me dumi,wani abu ya tsarga cikin jikinsa,fararen idanuwanta suka sauke masa wata irin kasala,sai ya daga hannunsa ya dora yatsuntsa guda biyu saman lips dinsa

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button