GURBIN IDO 7

07
Tun batayi nisa ba gaba daya qafafunta taji sun daddaure saboda tsakuyiyin da take takawa,wani gurin harda cabalbalin daya cakude da ruwa da qasa,tuni ta jima da sanin cewa ba qaramar rahama bane takalman a gareta,rashinsu a yan mintuna kadan yasa fa fara dandana kudarta,bata kuma san sanda zata sake mallakar wasu ba.
A hankali motarsu daada ke kutsawa rubibbiyar hanyar mai yawan gargada,kamar yadda sukazo a yanzunma su hudune,saidai yanzun akwai qarin saddam da zai musu rakiya,a hanyarsu ta zuwa ziyara qauyen dake kusa da rugar ummarun.
Cikin motar tattaunawa suke kan yadda gwamnati tayi banza da nuna halin ko in kula da jama’ar dake rayuwa a irin wadan nan muhallan,babu ruwa ba wuta babu hanya me kya bare azo ga maganar tsaro
“Subhanallah” salmanu driver ya fada yana taka burki sanda shanun suka fara keto burtalin xasu wuce,salmanu ya kalli agogon hannunsa yana cewa
“Aqalla sai sun kusa minti biyar ko takwas suna wucewa,shi yasa tun dazun nake sauri mu wuce kafin su iso”
“Wai daman kuna iya kula da dabbobi babu duka?” Laila ta fada cikin mamaki,idanunta nakan maimunatu dake koro shanun daga can baya
“Qalilan ne gaskiya,kiwo yana da wuya fa adda laila” maganar data ja hankalin daada,ta daga kanta zuwa ga sashen da maimunatu take.
Ido ta zuba mata sosai cike da mamaki da kuma burgewa,gaskiya sadam ya fada ba kowane ke iyawa ba,kula da dabba koda guda daya ne abune mai matuqar wahala,sai mutum me haqurin gaske da kuma tausayi,bare wadan nan da sun haura talatin,banda akuyoyi,yarinya qarama irin wannan me qananun shekaru,ita daya babu mataimaki,zata iya cewa bata taba ganin wannan ba,koda akwai din sai jarumar mace mai kamar maza,wadda taga jiya ta kuma ga yau.
Idanun maimunatu nakan motar sanda ya rage ita daya ce zata haura hanyar,idanunta cike fal da fargaba da tsoro,karo na biyu kenan da taga motar,amma sai take ga kamar abinda ya faru da ita shekarun baya zai sake faruwa da ita,sassanyar ajiyar zuciya ta saki sanda taga ta tsallaka,dai dai lokacin da anni ta sauke idanunta ga qafafuwan maimunatu,mamaki ya cikata ganin yadda take ratsa wajen da zallan qafarta ba takalmi.
Ta buda baki xatayi magana ta jiyo sautin maimaunatun
“Wayyo Allah” tayi maganar a matuqar jigace tana duqawa zuwa qasa tana duban tafin qafafunta
“Tsaya salmanu…..dubamin me ya samu yarinyar can” anni ta tsaida salmanu dake shirin tada motar,wajen suka kalla su duka,laila tayi kamar zatayi magana amma sai ta fasa kada qilu ta jawo bau,seat belt din jikinsa ya zare ya bude murfin motar ya fita,bai wuce minti daya ba ya dawo
“Kaya ce ta shige mata qafa,ta huda wajen sosai,amma naga ta zareta ma”
“Garin yaya?” Wajen da take salmanun yakalla
“Qafarta ce ba takalmi,dana tambayeta yana ina sai tace ya tsinke ne”
“Ina silifa din nan da nace a sakaminsu a mota?,daukomin daya a ciki” ta fadawa laila,daukowa laila tayi ta miqowa annin
“Bawa salmanu yakai mata ta saka” hannu salmanun ya saka ya karba ya juya yakoma indatake,zuwa sannan ta miqe tsaye bayan ta yagi wani ganye dake gefanta ta manna a wajen.
Daga kai tayi ta dubi salmanun sanda yake bata takalmin,sai taja baya kadan gami da girgiza kai alamun ba zata karba ba,abinda ya sanya salmanu dawowa inda anni ke zaune tana kallonsu
“Anni taqi karba fa,kamar bata yarda bane damu”
“Budeni” anni ta bashi umarni,sai ya zagayo ya bude mata qofar
“Anni,karkice zakiyi magana da ita,kaf fadin rugarmu babu wanda yake kulata” sadam ya fada,a mamakance anni ta kalleshi
“Saboda me?”
“Ban sani ba nima,amma tsoron mata magana akeyi” shuru anni tayi na wasu sakanni sannan ta zura qafafunta waje ba tare data sake bi ta batun saddam ba
Har maimunatun tayi taku daya biyu taji muryar anni
“Yarinya” cak ta tsaya,a tsorace ta waiwayo idanunta akan anni,tsoro ya sake kamata,don sam annin batayi zubin mutanensu ba.
“Yallijam” maimunatu ta fada a hankali ganin idanun annin har yanzu yana kanta
“Jam” anni ta maida mata tana kallonta tare da karantar yanayinta
“ya kike tafiya haka ba takalmi?” Qafarta ta kalla sannan ta kalla annin
“Sun tsinke ne daada” yadda ta kirata da girmamawa sai yasa anni ta saki murmushi
“Salmanu bata wadan nan ta saka,da hatsari wajen taka gurin nan haka” da fari kai maimunatu ta sake girgizawa kamar yadda ta yiwa salmanu,don batasan me zatacewa inna ba idan ta ganta da takalmin
“Na gode daada,zan qarasa a haka” haka kawai taji ta burgeta,akwai alamun tarbiyya da kamun kai me yawa tattare da ita
“Karki damu ki saka,idan ma kina tsoron fada ne a gida kice baquwa ce daga gidan bappa labaran ta baki” daga kai tayi sosai tana duban anni,idan ta canka dai dai fa kenam gidansu himu take nufi,ita a wa sa zata ambaci sunan gidan tace wani abu daga hannunsu ya fito zuwa gareta,a sanyaye ta karba takalman ta sakawa qafarta.
Cif da cif kuwa kamar an aunata,wasu irin slipper ne na danqo amma me garai garai dake nuna hoton flowers daga dukka jikin takalmin kaman tangaran,kallon qafar tata tayi ta sake kalla,sai ta daga kai a hankali tace
“Na gode sosai daada” duk kuwa da tana da yaqinin wannan takalmin idanunsa idanun inna ba rabonta bane,murmushi anni tayi
“Ba komai” sai ta juya maimunatun tana qara hanzari don ta taddo dabbobinta da sukayi gaba,tana kuma kiransu da wani irin salo da yasa anni ta bita da kallo.
"Anni....anni kenan,qaqale qaqalen mutane,tayiya jajibo jama'a ana zaune qalau" laila tayi 'ya qaramar mita ciki ciki,abinda yaja hankalin anni dake maida qafafunta cikin motar salmanu yana shirin rufe mata
“Me kike cewa ke kuma?”
“Bance komai ba”
“Oho miki,idan ma zagina kikayi kin zagi marwanu da Aishatu” idanu laila ta lumshe tana dafe goshinta,kafin tace wani abu wayarta dake kan cinyarta ta dauki sautin kida me dadi,saita daga wayar tana dubawa
“Ga marwanun nan” lailan ta fada tana hade rai tare da miqawa anni wayar
“Kin fada dai dai ai,sunan ubanki kenan” ta amsata tana warce wayar daketa harbawa da sunan super dad,ta shafa ta kara a kunnenta.
“Sai da salma ta gargadeni kan tafiyar nan,ashe ni zan karba gashin” bata daddara ba dai ta sake yin qorafin murya can cikin maqoshi,saidai babu yadda za’ayi anni taji,saboda tayi nisa a waya da shalelen dan nata.
Sai da tayi duk wani abu daya zame mata al’ada idan ta dawo da dabbobin daga kiwo sannan ta kira sunan innar,saidai babu ita ba motsinta,dole ta fara takawa zuwa cikin gidan,qirjinta yanata dukan uku uku,don batasan me zai biyo baya game da takalmin qafarta ba.
Daga qofar dakin innar ta tsaya
“Miwarti ɗilaulake inna(na dawo daga kiwo inna)” shuru taji,hakan yasa ta sake maimaitawa
“Dalla malama matsa ki bamu waje,kinxo kinata yiwa mutane hayaniya aka” muryar gaje ta fito daga cikin dakin,da alama itace kwance a dakin,wanda dama kusan aikinta kenan ko da yaushe,taci ta sha ta kwanta.
A sanyaye ta juya don barin wajen,dai dai sanda innar ta fito daga makewaye dauke da buta,sam bata lura da yanayin da fuskarta ke ciki ba
“Miwar…….” Ragowar kalmar ta tsaya mata a maqoshi,sakamakon wani zazzafan mari daya sauka a kuncinta hagu da dama,a take ta gigice,ta dafe dukka kuncin nata da tafukan hannayenta tana kallon inna,wadda ta taka gefan wani qaramin rumbu dake daura da ita,take tashin hankali ya bayyana muraran saman fuskar maimunatu,tunda taga ta doshi wajen tasan me zata dauko.
Tsumammiyar bulala ce,wadda ta debi shekaru ana azabtar da ita da bulalar,yadda ta tsani mutuwar ta haka tabtsani bulala,wannan ne dalilin da yasanya take dukka iya bakin qoqarinta taga bata aikata wani laifi da bulalar zata taba lafiyarta ba,zata iya cewa tabon da bulalar ta bar mata a gadon bayanta ba zaya lissafu ba.
Kusan daukewa numfashinta yayi sanda innar ta ware dukka qarfinta ta zuba mata ita,kafin daga bisani qarfin dukan ya sanyata ta sulale ta duqe a wajen,tun tana iya roqarta tare da bata haquri har bakinta ya mutu,duk da batasan me ta aikatawa innar ba,sai data gamsu don kanta da yawan dukan data yi mata sannan ta tsaya tana maida numfashi
“Gaje….gaje zo nan” ta qwalawa gaje dake daki abinta kira,gajen da duk yawan dukan da akewa maimunatun,duk magiyar da takewa innar bai sanyata ta koda leqo ba,hatta da sassan dake maqotaka dasu dukka kowacce ta leqo tana tsaye tana kallo,wasunsu suna qus qus a junansu tare da tir da dabi’a da halayen inna,wasu kuma suna fadin