BABU SO HAUSA NOVELGURBIN IDO

GURBIN IDO 6

06

    "Alhmdlh" anni ta furta sanda motocin suka faka a qofar ginin gidan bappa labaran,mahaifi ga ibrahim,qafafunta ta zuro qasa tana fadin

“Hasbiyallahu la’ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim” kana tayi bismilla ta yunqura,gaba daya qafafuwanta sun riqe,jikin tsufa ga kuma zaman mota

“Salmanu ku jirani,idan mun gama gaisawa inajin tare daku zamu fita can cikin gari na duba masauki” cewar matashiyar,dakatawa da tafiyar da anni keyi ta waiwayo tana yamutsa fuska

“Laila….me naji kina fada?,au dama ba rakiyar Allah da ma’aiki kika yimin ba?” Shaf ta manta da annin tana jinta,fuska tadan kwabe

“Kuma me nayi anni?,duk wannan dawainiyar?,ina cewa flight zamu bi kikace kefa sai mota,amma ban fasa rakoki ba”

“Yo rakiyar banza da wofi?,tunda ba zaki iya kwana a gidan ramatu ba” hannayenta laila ta hade waje daya

“Shikenan,zan kwana abar maganar” don sarai ta sani mitar annin ba abu bane me kyau ko dadi ba,duk da hakan taci gaba da takawa zuwa cikin gidan tana ci gaba da mitar,ta dauke kanta tana sake ajiyar zuciya,idanunta na sauka ga yaran da suka fara baibayesu suna kallonsu,sannan ta dubi su salmanu

“Kuyi tafiyarku kawai,amma ina buqatar ruwan sha”

“Akwai ai za’a samu” yahaya ya amsa mata,sai ta juya tana bin bayan anni zuwa cikin gidan.

Dai dai lokacin da yuuma ke qoqarin daura alwalar sallar magariba,wadd ta saba duk lokacin da tayi girki ta kammala,tana hadawa da alwalarta sanna ta wuce daki.

Cikin mamaki ta ajjiye butar data gama zubawa ruwa ta waiwayo da hanzari jin muryar annin

“Yafendo?,yafendo yau kuma ni kika tuna?” Yuuma ta fada cikin madaukakin farincikin da ya kasa boyuwa a fuskarta,kana ta kasa jiran qarasowa anni,ta taka da kanta ta cimmata a tsakiyar gidan

“Nice rahama,yau dai Allah ya qaddara ganawarmu,kimin aikin gafara” anni ta fada tana kama hannun yuuma,murmushi ya kuncewa yuuman,ta shiga marabtarsu,dai dai sanda aka fara shigowa da kayan amfani na abinci,wanda ya zamewa anni kamar ibada duk sanda zata ziyarcesu,takan sauke musu kayan abincin da sai su kusa shekara basu qare ba,mota biyu takeyi,daya ta kayan abinci,daya kuma wadda zata taho a cikinta.

Hajiya maryama wadda ake kira da anni,tamkar uwa take a wajen yuuma,saboda da ita da mahaifiyar yuuman ‘yan mata zarr suke,’ya’yan yaya ne(namiji) da ‘ya’yan qanwa,kakanninsu daya,a turance ake cewa(cousins),tun zamanin yammatanci akwai shaquwa sosai tsakanin anni da mahaifiyar yuuma,uwa uba sunansu daya,maryam da maryam,kakan yuuma asali dama bafullacene,mazaunun ruga,koda ya tashi aurar da diyarsa maryam saita auri jinsinsu,mahaifiyar yuuma a ruga tayi aurenta kamar yadda ta taso a nan,yayin da daya maryam din anni tayi aure cikin gari itama kamar yadda ta rayu a nan,saidai duk da hakan zumuncinsu bai yanke ba,duk sanda dama ta samu suna ziyartar juna su da ‘ya’yansu,har zuwa sanda suka fara tara zuri’a,rayuwar mahaifiyar yuuma batayi tsaho ba Allah ya karbi abarsa,a sannan duka duka yuuma din bata wuce shekara sha biyar ba a duniya,sosai anni taso ta riqe yuuma ta kuma aurawa danta na fari,saidai kuma mahaifin yuuma yaqi bada ita,saboda ita daya ce ‘ya mace a wajensa,dole ta haqura,taci gaba da kulawa da ramatu(yuuma) da kai mata ziyara har zuwa sanda aka aurar da ita ga bappa labaran,ita ta yiwa yuuma komai kamar diyar cikinta,saboda ita dinma Allah bai bata diya mace ba,sai maza da take dasu guda hudu.

Tun daga sannan takan ziyarci yuuma akai akai,ramatu yuuma ta zama ‘yar gata,batayi kukan rashin mahaifiya ba ko kadan,saboda anni ta tsare mata komai,bata da matsala ta kowanne fanni na rayuwa,tun daga sutura zuwa cima,ko yaushe anni naka hanya wajen yo mata aike koda bata zo ba.

Sanda shekaru suka fara tafiya yuuma bata haihu ba hankalin anni ya tashi,ta kashe kudi sosai akayita duba yuuma,saidai ba wata damuwa data nuna wadda zata hanata haihuwa bare a maganceta,daga qarshe anni taso fita da ita waje,don tana cikin sukunin rayuwa sosai annin,dukka yaranta ba wanda bai zama wani ba cikin garinsu na gombe amma yuuma tace ta barwa Allah,kome za’ayi idan haka Allah yaso ganinta ba wanda ya isa ya canza mata qaddararta,hakanan dole anni ta haqura,da kanta yuuma ta baiwa bappa labaran shawaran qaro aure,da farko yaqi amma ta matsa ganin cewa shi ba abinda ya nuna bazai iya haihuwa ba,bai kamata ta rageshi ba,daga bisani ya haqura,ya laluba ya zabo karimatu mahaifiyar himu,sanda tazo gidan itama sai data shekara biyu sannan ta samu cikin Ibrahim,bayan ta haifeshin ma sai daya kusa shekara bakwai ta haifa safiya sannan xubaida,sai auta sadam.

Ramatu macace mai tsananin haquri da hangen nesa,ita kanta fureran tasan da haka,shi yasa itama take qoqarin kiyaye wasu abubuwan kada ta shiga haqqinta da yawa,saidai kuma Allah ya jarabceta da son ‘ya’ya,sam bata iya yiwa kowa kara a kansu,tun daga sanda bappa yace zai dauki ibrahim ko safiya ya baiwa yuuma daadar himu ta runtse ido ta dunga diga rashin mutunci sai yuuma ta sake kiyayewa,kyautatawa da nuna kulawa da duk uwa zata yiwa danta idan ya ratso tsakaninta dasu tana musu,ta daukesu kamar yaranta,amma ta kiyaye duk wani abu da tasan zai bata ranta ko yaja musu cece kuce da furera,abunda yasa xaman nasu ya sake dadi kenan,zaman lafiya kuma ya wanzu tsakaninsu,duk da wani lokacin daadan himu kan dan taba,amma hausawa sukace idan kace wargi waje yake samu,kuma sai bango ya tsage qadangare ke samun qofar shiga,dole itama wasu abubuwan fureran ke kiyayewa.

Fadin irin murnar da yuuman a yau ta tsinci kanta ma bata bakine,saboda anni tadan kwan biyu batazo mata ba,ba kasafai yuuma ke zuwa wajen anni ba,saboda bappan mutum ne mai kulle sosai,itama anni bata zafafawa saboda tasan ya tsarewa diyarta komai,yayi mata riqo na amana bai barta ta wulaqanta ba,sannan ita annin a yanzu babu nauyin kowa a kanta,sakamakon mijinta ya kwan biyu da rasuwa,don haka kafin ma yuuma taje ita taje mata.

Yuuma bata dubi dare daya fara yi ba,haka ta tashi takanas ta yiwa anni sabon girki,cikin cimarsu ta fulani da tasan annin tafi so,a ranar kusan raba dare sukayi suna hira,sai gab da zasu kwanta anni tace da ita

“Wajen fa labaran nazo…..”

“Lafiya yapendo?”

“Lafiya qalau ramatu,shanu nake da buqata zan qara cikin gidan gona ta,wancan yaron hamdan naso aikowa,naga zai batan lokaci nace gwara nayi tattaki nazo da kaina” murmushi yuuma tayi,tasan dramer din anni da jikokinta sarai,takan gani idan taje musu,annin irin matan nan ne da basa daukan raini,bata da haquri akan abinda tasan kan gaskiyarta take,amma tana da matuqar kirki da kuma tausayi

“Aiko dai bappansu gaba daya dabbobinsa na garin yayi kudu dasu,kwana goma yace zaiyi ya dawo kinga muna ta zuba idanu shuru,amma naji suna waya da himu yace nan da jibi ko gata zai dawo,saidai ko ki tsimayeshi,cikin rugar nan nasan zai duba miki irin wadanda kikeso din”

“Kash…..kuma sai da nayi wannan tunanin,amma bari mu gani,Allah yasa ya dawo kafin na wuce,don kwana uku zanyi,ranar litinin zan koma ga likitan qafata abuja”

“Har abuja anni?” Yuuma ta fada tana kama baki,baki anni ta tabe

“Ina zaman zamana rigimammen yaron nan ya hadani da zirga zirga,duk kusan qarshen wata sai yasa an sakani a jirgi ba gaira ba dalili na tafi ganinsa,nace ya canzamin ya kafe,wai duk nigeri shine lamba daya…..kijimin qarya ramatu” anni ta qarashe fada tana yatsina fuska da tabe baki.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button