GURBIN IDO

GURBIN IDO 7

“Allah ne kadai yasan me tayi mata,kila ko yau ta dana halin uwarta ne” saidai babu ko mutum daya a cikinsu da ya isa ya tukari innar da sunan ceton maimunatu,kowanne irin hukunci ko horo kuwa zatayi mata.

A gadarance gajen ta fito daga dakin,tsaf da ita cikin kwalliyar kayan saqi,wanda kusan ko da yaushe cikin canza mata su innar take,idanun gajen sun kumbura sunyi jazur,abinda.ya bayyana har saman fuskarta,da alama kuka tasha ta qoshi.

Tsaye tayi saman kan maimunatu tana hura hanci tare da harare harare

“Daga kanki ki kalleta…..tayi kama da sa’arki?” Inna ta fada cikin hargagi,koda ciwon mutuwa maimunatun takeji a jikinta ya zame mata dole ta kalli gaje kamar yadda inna ta buqata,idan kuwa ta saba hakan wani sabon tashin hankalin ne,da qyar ta daga kanta ta dubi gaje,suna hada idanu gajen ta sanya qafa ta haureta cike da baqinciki da kuma jin haushin maimunatun,tasa hannu ta dafe wajen saboda radadi da zafin da ya ziyarceta

“Shegiya munafuka,ni zaki ha’inta,ashe yaron dana ganki dashi rannan ibrahimu ne?,to idan bakisan waye ibrahimu ba bari na gaya miki,shi din alqawarin gaje ne,bashi da matar aure sai gaje kiji na gaya miki,kusantar inda yake kuma shine babban kuskure da zaki aikatawa rayuwarki,wallahi wallahi kinjin na rantse miki,kome kike taqama dashi baki isa ki shiga tsakanin tsohon alqawari ba…..kukan da kika saka gaje yau sai kinyi mafiyinsa,ki bata haquri!” Inna ta fada tana kai mata harbi da qafa,ta sameta kuwa a gwiwarta wadda ta bugu sosai,tana dafe da wajen,cikin tsananin azaba tana dafe da gwiwarta ta fara baiwa gaje haquri,wadda keta qunci,tana jin babu abinda maimunatu zatayi mata ta huce haushin kula mata Ibrahim da tayi,tsahon wanne lokaci sukayi suna tare da ibrahim din?,tunda hatta da mutanen gari sun san da haka,baya ga haka kuma ace har sai da daadarsa tazo da kanta don yiwa tufkar hanci sannan sukasan da batun,lallai maimunatun ta cika cikakkiyar makira kuma macijin sari ka noqe kamar yadda innarta tasha fada mata.

     "A'ah,lafiya?,me yake faruwa?" Muryar jauro ta ratsa kunnensu,abinda ya sanyasu waiwayowa gaba dayansu,duk da cewa innar bata so dawowarsa yanzu ba amma sai ta dake

“Meye hakane?,me ya faru?” Ya sake tambaya yana kallon gaje kafin ya maida dubansa ga maimunatu dake zube a qasa,hakan ya baiwa gaje damar sulalewa zuwa dakonsu,tasan halin jauro tabbas yau cikin gidan ba za’a qarke lafiya ba

“Gata nan ka tambayeta maciyar amana” inna ta fada tana huci.

     Gabanta ya duqa yana kiran sunanta,ta daga kanta wande ta sokeshi tsakanin qafafuwanta tana duban ardo din,yanayin yadda yaga maimunatun ya tabbatar masa lallai ta daku,hatta da bakinta a kumbure yake,gefan fuskarta yayi kwanciyar jini da shacin bulala

“Wanne irin rashin imani ne wannan furera?” Jauro ya fada a mugun fusace yana miqewa tsaye

“Ita ya kamata ka yiwa wannan fadan bani ba,qanwar bayan gaje har ta iya hilatar maza tana binsu?,saboda rashin kintsi ta rasa wa zata bi sai ibrahimu?”

“Shine kikayi mata irin wannan dukan?,inda kuma kin nakastata fa?”

“Shikenan da kowa ya huta da ganin shegiyar fuskar dake daukan hankalin maza” cacar baki ce taso barkewa a tsakaninsu,ran jauro yayi mutuqar baci

“Waike wacce iriyar macace furera?,maimunatun zaki yiwa irin wannan dukan?,kowanne irin laifi ma tayi miki?,don kinga ina dauke kai ina barinki saboda kina nuna min kunfi kusa ko?”

“To dama meye naka a ciki?” Kai ya gyada cikin bacin rai,iskar data fara kadawa wadda ke tafe da dan yayyafi yasa jauro ya maida hankalinsa ga maimunatu

“Tashi ki shiga dakinku,Allah zai saka miki,a kusa ko a nesa,baya yafe zalunci” kasa miqewa tayi,ya tabbatar ba zata iya tashi ba,cikin muryar fushi ya qwalawa gaje kira.

      A tsorace ta qaraso tana raba ido hadi da matse hawaye,tsawa ya daka mata

“A’ah ya haka?,ka bita a sannu,rai aka bata mata fisabilillahi sannan ka bita da irin wanna tsawar?” Kallon banza ya watsa mata,yana ganin zallar son rai da son kai irin na innar

“Munafuka,kamata ki kaita daki” ya fadi yana zabga mata harara,da sauri ta zabura ta matso ta kama maimunatun,irin riqon tsaurin da tayi mata na mugunta yasa maimunatun cewa

“Wash hannuna”

“Sassauta mata riqon kafin nayo kanki na maimaita miki irin dukan da uwarki tayi mata”

“Dalili dame?,ke bi masharranciya a sannu ku rabu lafiya kada ta shafa miki jarfa ba gaira ba dalili” inna ta fada saboda tasan tsaf jauro zai aikata daga yadda ranshi yayi mummunan baci.

    Sakin maimunatu tayi sanda suka isa dakin,abinda ya sanyata ta buge gefan kanta,qauuuuu taji wani abu na yawo cikin kwanyarta,ya dafe wajen tana kiran sunan Allah,gaje na tsaye a kanta tana zuba mata harara

“Shegiya mayya,wallahi kikayi gangancin sake rabar ibrahim sai mun kasheki a gidan nan nida inna mun binneki,kuma mun kashe banza,tunda babu wanda zai tuhumemu” daga haka ga tsallaketa kamar zata takata,ta haure kan katifarta.

     Ta jima tana jinta a wata duniya ta daban,kowacce gaba ta jikinta ta zame mata kamar wani gyambo,da qyar take iya motsawa.

     Kiran sunanta da jauro yayi ya sanyata bude idanunta da qyar

“Tashi zan shigo” ya fada yana tsaye daga bakin qofar dakin,duk da yayyafin dake sauka har yanzu,jikinta taja ta miqe ta zauna sosai tana jingina da bango,ya dage labulen bayan ya shigo ya maqale shi sannan ya tsugunna daga gefe yana turo mata kwanon abincinsa

“Dauki kici maza diyam” sunan da ya kirata dashi yayi matuqar karya mata zuciya,ya tuna mata da tata daadarta,itace wadda ke kiranta da sunan,suna mafi soyuwa a gareta,fararen manyan idanunta suka cika da qwalla,tasa hannu a kasalance ta jawo kwanon gabanta ta fara ci.

   Wasa wasa sai gashi ta kusa tashi da abincin duk yawansa,ta riga ta saba ba kullum take samun abinci ba,idan ma ta samun to sau daya ne a rana,tana ci yana mata nasiha tare da kwantar mata da hankali,gaje na kwance tamkar mai barci,ranta ya baci sosai,shi babanta wai baya kishinta?,me yasa yafi nuna kulawarsa ga maimunatu fiye da ita diyar cikinsa?.

“Miyatti bappa” maimunatun ta fada a tausashe kanta a qasa cikin nuna jin dadin kulawar da ya bata

“Ba komai,kema diyata ce kamar yadda gaje take” kai ta jinjina,tana kin sauqi cikin ranta,ko babu komai yau din ba zata kwana da yunwar dake da take matuqar wahal da ita ba a duk dare.

     Har jauro ya juya ya fita maimunatu tana binsa da kallo,sai daya sauke labulen ya qarasa ficewa sannan ta sauke nannauyar aiiyar zuciya tana janye idanunta daga wajen,dai dai lokacin da gajee tayi caraf ta miqe zaune

“Munafuka algunguma,kamar a idanun inna akayi wallahi,Allah ya kaimu safiya” tsoro ne ya cika zuciyar maimunatu,saboda tasan tunda gajen ta fada sai ta aiwatar,idanunta fal da qwalla ta shiga roqon gajeen tayi haquri,maimakon ta amsa mata sai ta lullube kanta da mayafi tayi kwanciyarta gami da juyawa maimunatun baya.

Sai da dukka yawun bakinta ya dauke kan roqon gajee tayi haquri,daga qarshe dole ta haqura da roqon,ta rufe idanunta,hawayen da suka taru suka gangaro mata.

Wani wahalallen barci tayi mara dadi,saboda ko ina na jikinta ciwo yake mata,ko da tayi sallar asuba ma zaune tayi a wajen,saboda ciwon da jikin yake mata,inda ace shimfida ce mai laushi irin ta gaje wala’alla ta iya rabawa takwanta,amma shinfida irin tata da bata da maraba da tattauran dutse babu ta inda zata iya kwanciya taji dadi.

“Maimunatu!!!,ke maimunatu!!”kiran mafarautan da ya ratsa tsakiyar baccinta ya sanyata farkawa firgigit,inna ce tsaye a kanta,hannunta riqe da robar da yawancin lokuta suke tatsar nono a cikinta,duban maimunatun take kamar zata afka mata

“Yahudillo dirgul…..(zoki tafi kiwo)……”
“A ina?” Maganar jauro ta katse hargagin da inna ta fara yi mata,ratsowa yayi sanye da riga ‘yar shara da malfare a kansa,hannunsa riqe da baqar leda,bisa dukkan alamu fita zaiyi

“Daga yau…..har zuwa ranar da maimunatu zata warke babu ita babu zuwa kiwo,wallahi wallahi wallahi sau nawa kenan?”

“Tati(uku)” innar ta amsa masa tana riqe da qugunta tana kallonsa

“Idan naga akasin hakan zakisan waye ainihin jauro wanda ada can baki sanshi ba,wannan shine hukuncinki na irin dukan da kikayi mata”

“Wai dakata,wai me kake nufi ne?,ko kana yimin baqinciki ne da dukiyar dabbobin da Allah ya bani ne?,wanda dama an jima ana fada,ganin muna zaune shekara da shekaru tare yasa ban gasgata ba,amma ayanzu na fara ganin alamu ganin idona kuwa” dubanta yayi

“Ki bari sai zuwa sanda kika tara taki dukiyar ta halastacciyar hanya saiki gayamin haka” sosai maganar daya fada tayi mata ciwo,tana ganin jauro shi daya ne mutumin da yasan sirrinta yake kuma shirin xamar mata tarnaqi a rayuwa,wannan amsar da ya bata ta hautsinata,ta dinga jifansa da kalamai,wanda kalmarta ta qarshe ita ta sanya ya tsaya cak yana dubanta

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button