GURBIN IDO

GURBIN IDO 15

15

Dawowa cikin labari

Tafiyar awanni biyu suka qara suka shigo garin gombe,a lokacin anata sallar la’asar,wasu masallatan ma sun idar.

Slow da motar ta fara yi sanda suka qaraso unguwar suka fara gangarowa faffadan layin gidan dr marwan din ya sanya maimunatu farkawa,ta zauna sosai tana murza idanunta tare da kallon sabuwar duniyar da rayuwa ta kawota,murmushi anni tayi

“Lallai kinsha barci maimunatu,harma kin fini jimawa” murmushi tayi cikin jin kunya ta sadda kanta,itama anni murmushin tayi tana maida dubanta ga qofar gidan da suka fara harin tsaiwa

“Marwan dinma yana nan ashe” ta fada tana leqe fa window

“Eh ga motarsa nan,harda baqin motoci ma” hayatu ya amsa mata

“Marwanu marwanu na jama’a,hutun qarshen satin ma shi ba samu yake ba”

“Wallahi haj anni,ai aljanna kawai ta ragewa alhj,amma yana samun yabo da shaida me kyau” kanta ta jinjina cikin jin dadi,ita kanta ta sani,matuqar dai aljanna qasan qafar uwa take,to babu abinda zai hanata dagewa marwanu ya shige.

Kakaf hankalin maimunatu yana ga hanya sanda motarsu take shigewa cikin tangamemen gidan,ba laifi tana da dan sanin rayuwar dadi ‘yar mitsitsiya,amma komawarta rugar ummaru ya sake maidata baqauya sosai,don haka ta dinga bin gidan da kallo cikin mamaki su anni,ya akayi su dake rayuwa a guri irin wannan suka iya zuwa rugarsu har sukayi sati guda?,lallai su din nagartattu ne wadanda basu maida duniya a bakin komai ba.

Kafin hayatu ya budewa anni qofa ta fito wajen ya fara cika da mutane,mafi akasarinsu ma’aikatan gidan ne maza da mata,kowa na mata sannu da zuwa tare da qoqarin nuna kulawarsa a gareta,abinda zai nuna maka irin girma matsayi da kuma muhimmancin da take dashi.

Waiwayawa tayi ga maimunatu wadda ke rabe bayan murfin motar da suka fito a ciki,cikin tsoro,kamar xaka ce mata ket ta zura da gudu,sannan ta dubi daya daga cikin ma’aikatan,babba ce aqalla zatayi shekara arba’in da takwas,kuma da alama ita din ta hannun daman anni ce nesa ba kusa ba

“Tabawa riqo min baquwar nan ki shiga min da ita ta qofar baya” ta fadawa tabawan qasa qasa,gyada kanta tayi sannan ta juya inda anni tayi mata ishara,tunda tayi mata magana ta haka tasan cewa wala’alla abune na sirri bataso kowa da kowa ya sani.

      Murmushi tabawa ta sake mata sannan ta kama hannunta,ko ba komai maimunatun taji ta sake da tabawa farat daya,saboda yadda ta kama hannunta babu kyama ko alamun kyara ko kuma tsangawa,tana biye da ita har sanda duka bulla wani tangamemen falo,falo ne daya wadata da dukkan nau'in kayan alatu na rayuwa,rukunin kujeru biyu ne a cikinsa saboda girmansa,kowanne color dinsu daban,akwai qofofi a ciki dake nuna alamun dakunan bacci ne,sai wata gajerar siririyar hanya wadda kitchen yake a ciki.

       Kitchen ta wuce da ita,wanda maimunatu ga bishi da kallo cike da mamaki,farat daya ta gane kitchen ne,duk da na ainihin gidansu na gembu bai kama koda qafar wannan ba

“Tsaya ina zuwa” tabawa ta fada sannan ta juya ta fita,bata yi koda minti daya cikakke ba ta dawo,tana murmushi ta dubi maimunatu

“Kiyi haquri ko,na barki a tsaye,muje na nuna miki dakinki” kai ta gyada kawai tana maida mata martanin murmushinta,a salube kuma tabi bayanta.

Dakin yafi kusa da kitchen din gidan,don shi daya ne area din,babban dakine da aka shimfideshi da tiles marbles baqaqe masu dishi dishin light blue a jikinsa,yana dauke da babban gado madubu da wardrobe ta jikin bango,gurin ajjiye takalma,da manya bedside guda biyu masu dauke da bedside lamp,tun daga curtains zuwa dan qaramin carpet din dake malale a gaban gadon duka light blue ne,abinda ya qarawa dakin haske da kuma kyau.

“Anni tace nan ne dakinki,ki zauna ki huta sosai,sannan ki fadi abinda kikeso kici,ga bandaki can koda wata buqata zata kamaki,tace zata kiraki idan ta gama” kai maimunatu ta gyada,jikinta a sanyaye,tana ganin kamar taxo inda bai cancanci tayi rayuwa dasu ba,tako ina mutanen nan sunfi qarfinta sun kuma wuce tunaninta,yanzu wannan dakin shi za’a bata a matsayin dakin kwananta?,ita a wa?.

“Me zakici?” Tabawa ta sake maimaitawa idanunta akan maimunatu tana nazarinta,da sassanyar muryarta tace

“Ba komai,banajin yunwa,bamu dade da cin abinci ba” gaskiyarta kuma ta fada,cikinta ya riga da ya zama mara space sosai da bazai iya daukan wani abincin ba bayan awanni biyu,yunwa ta zamar mata jiki

“Shikenan,amma idan kinji kina da buqata,ga waya can ki daga ki kira kitchen,za’a kawo miki duk abinda kike buqata” kai kawai ta sake gyadawa bawai don ta fahimci yadda zatayi kiran ba,sai taga tabawan ta qarasa wajen da qullin kayanta suke tana niyyar dauka

“Kaya na ne” daga kai tayi ta dubeta,murmushi tayi mata sannan tace

“Anni ce ta bada umarnin a daukesu,za’a kawo miki wasu kayan da xakiyi amfani dasu” bata son rabuwa da kayan,kayan suna d matuqar amfani da kuma tarihi a wajenta

“Don Allah ki cewa anni tabarmin su,ina so” fasa dukan tayi,sai ta amsa mata da to,ta juya ta fita a dakin sannan taja mata qofar ta rufe

A nutse ta gama qarewa dakin kallo kusfa kusfa,daga nan inda take zaune tana iya jiyo maganganun mutane sama sama,saidai kuma bata iya rabewa da abinda suke fada.

Daga can bangaren anni kuwa sannu da zuwa jikokinta suke ta shigowa sunayi mata,duk da cewa ba kasafai take wannan wasan dasu ba,amma kuma su din basu qyaleta ba,duk da zafin da take dashi.

Fitowar annin kenan daga wanka bayan ta fito tana zaune a qasa,ta miqe qafafunta da sukayi mata nauyi da kuma tsami saboda zaman mota,man zafi take qoqarin shafawa tabawa ta shigo dakin,dauke da wani qaramin flask din silver da cup guda daya,gefe ta zauna anni ta daga kai ta dubeta

“Sannu tabawa”

“Yauwa hajiya anni” ta amsa mata tana murmushi tare da qoqarin bude flask din ta zuba mata abinda yake ciki,dan yamutsa fuska tayi

“Dakata mana tabawa,yaa daga dawowata zaku hau duramin magani?,ba wani abu me galmi galmi sai magani kamar bugagga?” Dan danne dariyarta tabawa tayi,ita din ba baquwar hutsun anni bace,ta riga data saba da hakan tsahon shekara goma sha

“Ammi ce tace shi xa’a fada baki”

“Ta rasa abun arziqin da zata yimin sai wannan?”

“Abu me galmi galmin yana hanya ai anni,ita da kanta ta karba girkin abinda zakici idan zaki dawo,yanzu haka a kitchen na barta” sai a sannan annin ta saki fuska

“Allah sarkiAishatu,badai qoqari ba….ba daga nan ba” ta fadi tana miqa hannu tare da karbar maganin da tabawa ta zuba matan tana kurba a hankali,ita kanta tana son maganin,saboda yana saurin warware mata gajiya daga jikinta.

       Kurba uku tayi aka turo qofar dakin hadi da sallama,matashiya ce sanye da rigar material da aka yiwa budadden dinki,kanta yane da mayafi plain daya dace sosai da kayan jikin nata,tabawa ce ta amsa sallamar tata tana dubanta

“Ina kika shiga tun dazu ga aikinki can an dade da gamashi?” Sai data zauna gefan gadon annin ta yage mayafin kanta sannan tace

“Bari kawai baba tabawa,ai na baje zanci dadi kawai aka kirani daga makaranta nazo ga lecturernmu da yace bazai samu shigo ba ya shigo,mugu ne mutumin nan na qarshe,shi yasa ba shiri na tashi na tafi”

Murmushi tayi

“Ai gashi can a ajjiye”

“Yauwa baaba tabawa…..godiya nake” waiwayawa tayi zuwa ga anni tana murmushi

“Anninmu ta mutunci……barka da sauka,kun dawo lafiya?”

“Lafiya garas na dawo,gashi ma kin ganewa idonki?” Dariyar dake cin salma ta danne,don tasan anni na ciki da ita,domin kuwa ita ya khalid(shine babban jika a wajen anni ta danta na biyu me bin dr marwan)yace ta shirya ta rakata amma ta kawo nata uzurin bata je ba

“Amma nafi kowa jin dadi a gidan nan,Allah da bakya nan duka gidan babu dadi,ai bansan yau zaku dawo ba don munafurci laila bata gayamin ba,da na saka an siyo miki nama a wani suya sport nan bayanmu me shegen dadin tsiya……”

“Ke…..kiyi ta kanki,wato ga kuriya ko?,to ta Allah ba taki ba,bana so” fuska tadanyi qoqarin canzawa,duk a qoqarinta nason gamsar da anni duk da dariyar daketa taso mata,saboda tana da buqata wajen yayansu ja’afar,kuma ta tabbatar da zarar annin ta saka baki anyi an gama

“Allah anni da gaske nake,kar kiso kiji yadda duk naji……”

“Ki rabawa aishatu da marwanu biyar biyar…..”annin ta fada tana danqara mata daquwa,wanda babu shiri salma ta miqe ta zari jakarta tana cewa

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button