GURBIN IDO

GURBIN IDO 14

14

Sanda aka gama musabaqar suna tsaye a jikin motar dr marwan(abbi) suna jiransa yayi kiransu,ya hadasu da mahaifin shaheeda da ita kanta shahidar suka gaisa,irin dadin da shaheeda taji ba qarami bane ganin cewa akwai sanayya tsakanin mahaifinta da nashi,ko meye zai dan zo mata da sauqi,ba kamar ace babu komai tsakaninsu ba,kwata kwata bata nuna wannan farincikin a fili ba saboda kamun kai da kuma tsira da mutunci.

Babu jimawa shaheeda ta ziyarci gidan dr marwan,nan da nan ta saba da mafi yawa na jama’ar gidan,tayi amfani da hikima da kuma hankalinta da wayo ta shiga jikin anni da amma mahaifiyar ja’afar sosai,a lokacin jaafar tuni sun koma hutunsu,bata damu ba tasan tana da target a kansa komai dadewa,baka isa kace son ja’afar take ba,don ko zancansa bata taba yi ba bare ka kawo hakan cikin ranka,saidai a hikimace ta gama karantar dabi’unsa daga hirarsa dake bakin ‘yan uwansa,da kuma yawan ambatonsa da anni takeyi,ta gama gane abinda yakeso da wanda bayaso,ta haddacesu tsaf bisa kanta.

Sanda suka dawo hutu sun samu shaheeda a gidan,don tuni ta maida gidan wajen zuwanta,sun kuma saba sosai ta zama kamar ‘yar gida,da yawa suna cewa saboda gidansu duka maza ne shi yasa tafison gidan baba dr kamar yadda take kiransa,don nata ‘yan uwan duka maza ne,ita daya ce mace.

Eh tabbas,zamanta a gidan na mata dadi,saboda tana da abokan hira sosai ba kamar gidansu ba,saidai nata plan din ja’afar ne,boyayyen sirrinta da babu wanda ya sani,tayi qoqari matuqa wajen ganin ta janyo hankalinsa kanta cikin hikima da basira,ba tare da shi kansa ta bari ya fahimci komai ba,komai na ja’afar din dabanne,ita ke kula da wasu abubuwa nasa.

Da farko bai farga ba,saboda sam hankalinsa bashi a wajen,mma daga bisani ya soma fahimtarta,ya kira qanwarsa nadiya,ita yake nema idan yana buqatar wani abu da anni ko su amma basu iya ba ko ba zasu iya ba,wadda tasu tafi zuwa daya saboda kamanceceniyar da kuma nutsuwarta,ya yanka mata warning akan ta cire shaheeda akan duka sabgarsa sai idan shine ya buqata.

Farko nadiya ta kasa gayawa shaheeda,sai ita da kanta ta fahimta,ta kuma yiwa nadiya maganar,bata boye mata ba ta gaya mata,tun daga ranar shaheeda ta fita a sabgarsa gaba daya,duk wani abu da ya shafeshi ta fita a ciki,koda zaune take a wajen yazo zata tattara tabar wajen,hakanan abu idan ya dangaceshi komai yadda ta iya babu ita a ciki,abun yana cinta a rai,tana jin ciwo amma ta danne zuciyar tata,mutum ce mai yawan addu’a,maimakon damuwa ta rinjayeta,saita rinjayar da addu’a,takan hana idanunta barci ta tashi cikin dare ta gayawa Allah damuwarta.

Sannu a hankali shima ya fara noticing canzawarta,sai ya fara jin damuwa a kanta cikin zuciyarsa,shi da kansa ya dinga mamakin kansa,damuwa for what?,akan wata mace?,sannu sannu Allah ya fara matsa zuciyarsa,sai ga ja’afar da kansa ya fara nema shaheeda tayi masa wasu abubuwan,kamar kalolin girke girken da take masa a baya,amma fur sai ta murje idonta taqiyi,duk da yadda zuciyarta kan buga,taji babu dadi amma haka take mazewa.

Rana ta uku daya aika tace ace bata da lpy taqiyi zuciya tazo masa iya wuya,yana zaune a sannan yana duba saqonnin da yake samu daga companies na jiragen sama dakeson yin aiki tare dashi,zare laptop din yayi daga saman qafarsa ya ajjiyeta gefe ya miqe ya fice.

A dakinsu nadeeya ya samesu zaune an kafa majalisar hira,tana ta dariya tana dariya harda riqe ciki,Har kowa yayi shuru bata ankara ba,sai da taga hankalin kowa ya karkata ga qofa,sun kuma saka nutsuwa a jikinsu sannan ta ankara,tayi hanzarin jawo dankwalinta ta rufe lallausar sumarta ta fulani,gabanta na wani irin faduwa saboda zallar kwarjinin da yayi mata,tana jin kamar zaman ma ba zata iya ba.

Bata ji yace musu komai ba amma sai taga kowace ta fara miqewa tana fita a dakin,ganin sunata ficewa ba tare da tasan dalili ba sai itama ta miqe tayi joining dinsu.

Nadeeya ce qarshe sai ita,nadiya na fita ya matsa yayi blocking qofar gaba daya da jikinsa yana kallonta da idanunsa da suke fasa mata zuciya,tayi baya kadan ta kuma sauke kanta qas,don ba zata iya jurewa kallonsa ba,ta fara lanqwasa yatsunta,tana son tace ya matsa mata itama ta fita amma kuma tasan cewa tayi kadan ta iya fadin hakan.

“Baki da kunya ko?” Ya fada a taqaice kamar me ciwon baki,abinda yasa babu shiri ta daga kanta ta kalleshi,sai kuma ta sake saukarwa saboda idonsa yana kanta

“Ni sa’anki ne da zan dinga aikowa kiyimin abu kina rejecting,bakisan ba kowa nake sawa yayi mun abu ba?” Sosai maganar tasa tayi mata dadi,wani abu ya tsarga mata,gefe daya kuma rauni ya kama zuciyarta har ya sanya qwalla silalowa daga idanun nata tare da kalmar

“Kayi haquri” shuru na sakanni yayi kafin ya sauke hannayensa ya juya ya fara ficewa daga dakin,sai ta bishi da kallo har yabar wajen.

      Kwata kwata ji tayi bataji dadi ba,cikin ranta kuma tana tsoron kada fa ta barar da damarta,a sukwane tayi kitchen ta fara hada masa abinda ya buqata a daxun,tana tsaka da aikin su safina suka shigo

“Me yayi miki?,me ya faru?” Tambayar da suka dinga mata kenan

“Ba abinda yayimin” ta amsa musu hankalinta na ga girkinta

“To wannan abincin fa?,naga bamu jima da gama cin abinci ba” safina ta fada tana bude tukunyar

“Na yaa ja’afar ne” amsar daya sanyasu kallon kallo a junansu,suka fara kuma tsegumin anya kuwa?,bata bi ta kansu ba,itadai burinta ta gama ta kai masa.

Sanda khadim yakai masa dawowa dashi akayi,yace bayaso,abinda yasa hankalinta ya tashi sosai,ta kuma boye ta dinga kuka,washegari ta hada kayanta tace zataje,duk da kwanakin da takeyi basu cika ba.

Kwana biyu rak a tsakani ya karanci bata gidan,yayi kaman ya share amma sai yaji ya kasa,ya kira nadeeya ta tambayeta,bata boye masa ba ta gaya masa duk abinda ta sani,ya sallameta,sannan yayi shuru shi daya yana tunani,rashin cin abinda ta aiko masa ne ya kawo faruwar hakan?,washegari sai ya tsinci kansa da shiryawa ya tafi gidan daukota,babu ko rakiyar jabir.

Suman zaune tayi sanda akace mata ja’afar ne na gidan baaba dr,bai shigo ba ya dai aiko da gaisuwa wajen ummanta,sannan yace a gaya mata ta fito su tafi,saqon da ya bata mamaki,haka ta shirya kayanta ta biyoshi.

Cikin motar kamar bashi ba,har ta fara cire hope,saboda ko uffan bata hadasu ba,sai da suka kusa gida sannan ya magantu

“Idan kika sake wannan kuskurem sai na hukuntaki” ta fahimci da qaramar magana yake isar da saqo me yawa,maganarsa guda daya idan ka fassarata taka dauki.ma’anoni.masu yawa

“Kayi haquri” tace dashi,yaji dadi cikin ransa na yadda take da sauqin kai,saidai ko ka fuskarsa haka bai nuna ba.

Wasa wasa sai shaheeda ta karbe komai nasa cikin gidan,nan da nan kowa ya fara daukan haske,duk da cewa shi gogan yana jin dadin hidimarta sosai saboda ya yadda da tsaftar ta da qwarewarta wajen girki,sannan yana jinta a ransa wanda yafi ta’allaqa hakan da sabo,amma babu wata maganar soyayya data taba gittawa tsakaninsu.

Tsarin gidansu shaheeda daga candy mahaifinta bashi da ra’ayi barin diyarsa mace ta qara gaba,sai kuma gashi guda daya ce macen da Allah ya bashi,a lokacin shaheeda tayi candy,mahaifinta ya tasamma aurar da ita,dr marwan na samun labari ya nemawa ja’afar bisa shawarar anni,saboda qoqarin da taga shaheeda nayi a kansa,da kuma yadda ta karabceshi tsaf,tamkar ita ta haifeshi.

Kowa yayi tunanin za’a samu matsala sanda ja’afar yaji an nema masa auren shaheeda,sai gashi bai wani damu ba,hasalima kusancin dake tsakaninsu ne ya sake daduwa,hakanan itama ta sake qara qaimi wajen kula dashi,abinda yake matuqar yi masa dadi a rai,duk da dan uban miskilancinsa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button