GURBIN IDO

GURBIN IDO 15

“Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki tsohuwa me ran qarfe” tayi waje,annin bata barta ba ta dora mata

“Sannan kada uban wanda ya sake saka tabawa aiki cikin gidan nan na gaya muku,ba me aikin kowa bace ehe……” Murmushi tabawan tayi bayan ficwwar salman

“Ba wani abu bane hajiya anni,koda aikin gidan nan duka zai dawo kaina indai zan iya zan yishi,keda iyalinki ai kunfi qarfin komai a wajena” kofin maganin ta ajjiye gefe

“Na sani,amma ace duk ma’aikatan dake gidan basu ishesu ba?,ubansu ya lalata su ya dauko masu aiki ya zube musu kamar ba diya mata ba da gobensu a gidan aure zata samesu?,kiga yarinya batasan ta zagi jikinta tayi aiki gidan aurenta ba?,shi yasa suke wayar gari qazamai,ko cikakken tuwo basu iya yiwa miji da zaici kamar ya cire yatsunsa ba……haka yaranmu na karkara suke?” Kai tabawa ta kada tana murmushi

“Sha wuya ne ai wadan nan” furucin na tabawa ya tuna mata da maimunatu

“Kwarai da gaske kuwa,kin tunamin ma,akwai maganar da nakeso muyi dake tabawa” anni ta fada tana gyara zama,tabawa bame aiki anni ke kallonta ba,yar uwa take kallonta kuma abokiyar shawara,bama ita daya ba,kusan duk wanda ya girma ya tashi a gidan kallon kaka yakewa tabawa,mutum ce ita me tsananin mutunci da kuma dattako,bata aikin komai ma cikin gidan,saidai idan anni na buqatar wani abun da sun riga sun saba tabawan kadai keyi,duk da akwai masu aiki sosai cikin gidan

“Kinga yarinyar dana sanya ki kaita ciki ai ko?”

“Qwarai kuwa haj anni” tabawa ta fada tana bawa anni dukka hankalinta

“Yarinyar kyakkyawa sosai,saidai akwai alamunrashin sukuni a tattare da ita da kuma wahala” kai anni ta gyada

“Bama alamu bane,akwaisu” a nutse ta bawa tabawa labarin maimunatu,tare da qudurinta a kanta,labarin da yayi matuqar sanyaya jikin tabawan,tare da saka mata tausayin maimunatu me yawa cikin ranta

“Kiyi nufin alkhairi sosai hajiya anni,kuma dama halinki wannan,Allah ya baki nasara akan hakan,yasan kuma iya bakin matsalar ce,yasa ta zamto masa haske cikin rayuwarsa”

“Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu”anni ta fada tana jin dadin yadda tabawa ta fuskanceta

“Amma kuma wani hanzari ba gudu ba.…..”

“Uhmmm,ina jinki tabawa”

“Kinsan akwai matuqar banbanci da tazara me yawa tsakanin manya(sunan da takan kira ja’afar dashi,saboda sunan babban malamin da yaci,kuma wasu sukan kirashi da sunan) da ita yarinyar?,kinsan kuma hali da dabi’ar yaran zamani,musamman shi daya keta qasashe da dama,yaga kuma mata iri iri,inajin kamar idan akace za’a bashi yarinyar nan a haka zai zama da matsala” murmushi anni tayi

“A hakan zaa bashi ita ba kuma a hakan za’a bashi ba” cikin rashin fahimta tabawa ta kalli anni don bata gane hausar ba

“Abinda nake nufi shine,inaso ki kulamin da duk abinda zata ci ta kuma sha,nasan ba lallai a yanzu ta farat daya ta dauki cimarmu ta iya sakin jiki taci yadda ya kamata ba,sannan ki kulamin da tsaftarta ki jata a jiki a kiyi mata duk abinda ya kamata,sauran abubuwan zanyi magana da salamatu,abinda ya samu zuwa sanda zai zo gida shikenan,zan bashi ita a haka,shi nakeso ya qarasa rainonta,kinsan hikimar yin hakan?” Kai tabawa ta girgiza tana duban anni

“Inaso ne yasan ciwonta,yasan dadi da kuma wuyarta,yadda bazai riqeta sakwa sakwa ba,sa’annan inason ya ginata kan tsari da dabi’ar da yakeso,ya dabi’anceta a yadda yakeson matarsa ta kasance,hakan shi zai bada damar da zata shiga zuciyarsa fiye da marigaiya shahida,don shahida tazo da tarbiyyar ta da kuma dabi’unta ne daga gida,ita kuma wannan shi zai saitata a yadda yakeso,zata kasance ne kan tsarin da duk yaso” sosai tunani da hangen anni ya yiwa tabawa dai dai,kuma hikimarta tayi mata,ta sha alwashin lallai zata yiwa annin duk abinda ta buqata,don tana cikin mutane na gaba gaba da takejin ciwo da zafin yadda har yanzu suka kasa shawo kan matsalar manya,tana jinsa kamar danta,don tun yana qarami take a gidan,da ita akayi rainonsa.

     "Dubamin ita tabawa,ki duba ma'ajiyar kayan nan da aka dinka wancan watan ki ciccire mata wadanda zasu yi mata dai dai,inason ta fito muci abinci da ita anjima kadan"

“To an gama haj anni” tabawa ta fada tana miqewa.

       Tana shirin fita a dakin sallamarsa cikin muryar dake cike da tarin nutsuwa da kuma haske na ilimi da dattako ta ratsa falon,dr marwan ne,sanye yake da lafiyayyar shadda ruwan qasa dinkin babbar riga 'yar ciki da wandonta,kansa kuwa hula ce da ba'a iya hangota saboda fari qal din rawanin dake nade a kansa,idanunsa sanye yake da farin gilashi dake qara masa qarfin gani,akwai cikakken gemu a fuskarsa wanda furfura ta fara yiwa ado ta gauraya da baqin dake jiki.

    A girmame tayi maaa sannu da shigowa sannan ta juya ta fita a dakin,shi kuma ya sanya kai dakin mahaifiyar tasa,bakinsa dauke da sallama.

      Fuska a sake ta amsa sallamar tata,sannan ta janye qafafunta don ya samu wajen zama saman lallausan carpet din da take kai,don qasa ne wajen zamansa duk sanda yazo gaidata.

       "Kun sha hanya anni" ya furta bayan sun gama gaisawa da tambayar mutanen data baro.

“Wlh marwanu,amma alhmdlh,gamu a gida”

“Mun godewa Allah” ya fada yana murmushi

“inata zuba idanu na zaci baku qaraso ba,har ina shirin kiran jibril”

“Mun iso marwanu,kana tare da baqi lokacin…..na iso da baquwar yarinya ma”

“Eh tabbas,muna tare da ministern ilimi ne,batun da nakeso mu tattauna kenan dake akai” kai ta jinjina

“Nima akwai batun da xamu tattauna din,amma kamar lokaci bazai bamu dama ba,naga an kusa sallar magariba,inaga idan aka idar da sallar isha’i sai mu zauna”

“Eh hakan yayi anni,Allah ya nuna mana”

“Ameen…..amma kunyi waya da jabiru ne?” Dan dubanta yayi

“Sai da ya sanar miki kenan?”

“Kana da wadda ta fini ne marwanu?” Qas yayi da kansa

“Babu anni,amma banason tashin hankalinki ne ko kadan”

“Ja’afaru rayuwata ne,Allah ne ya doramin qaunarsa cikin dukka jikokina,idan har an aka fara boyen matsalar ja’afar saboda kada na shiga damuwa to kuwa ba’a kyautamin ba,zanyi dukkanin me yiwuwa ne don naga rayuwar jaafar ta daidaita kamar yadda take a baya”

“In sha Allah ba zata sake faruwa ba,kuma maganar da nakeso muyi din tana da alaqa da jaafar din”

“Allah yasa alkhairi”

“Khairan in sha Allah” ya amsa mata

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button