GURBIN IDO 20
Da mamaki fatima ke satar kallon yaa khalid din,shi da baya yiwa mace kallo uku amma yau gashi ya kafe idanunsa akan maimunatu?,sai daya fuskanci fatiman na kallonsa sannan yajanye idanun nasa ya kuma bata rai yana komawa ga batunsu shida annin,saidai lokaci lokaci yana satar kallon ta.
Iya tafiya ta tafi dashi,duk da bata qarasa kalar macen da yakeson aure ba,amma fa hada komai da komai,special care kawai zata samu ta wasu bangarori ta yiwa mata fintikau.
“Nidai bansan me kakeson maidani ba khalid,wannan jewar fa ta isheni,nidai a barni,ciwo ai ba mutuwa ba,idan lokaci kuma yayi dole na tafi” anni tayi statement din qarshe tana miqewa tsaye da zummar tafiya,bayan maimunatu taqi cin abincin da aka kawo mata,sam ba zata iya ba,tana jinta ne duk a daure saboda kallon data fuskanci saurayin yana ritsata dashi,wai shin kam haka samarin family dinsu suke ko kuwa su din su biyun daga garesu ne?.
Shi ya musu tattaki har zuwa bakin motar da sunan yiwa anni rakiya,fiye da rabin hankalinsa yana kan maimunatun,duk da yana yine yana basarwa har motarsu ta daga.
Yayi tunanin da sun yafi shikenan,saidai kuma kasa nutsuwa zuciyarsa tayi,har sai da yakai kansa gida dr marwan,ya kuma sakeyin ido biyu da.maimunatu,tun daga sannan abun ya zame masa kamar wani jarrabi,duk bayan kwana biyu daga office yake zartowa nan din,baya barin gidan sai bayan sallar isha’i.
*Karfe shida suka dawo daga islamiyya,tana sanye da babban hijabinta da ya saukar mata har qasan qafafunta,kalar blue black,abinda yasa yayi matuqar haskata tare da yi mata kyau,tana rungume da qur’aninta a qirji,laila na gefanta tana amsa waya.
Suna sallama a falon sukayi idanu biyu dashi,qirjinta yayi mugun faduwa,taja da baya kamar zata koma sai kuma ta kasa,ganin ya ganta sarai,cikin zuciyarta bata son haduwarta dashi,saboda kallon da yake tsareta dashi da kuma sanyata cikin lamuransa da yawa,har fiye dasu laila da suke jininsa.
A hankali ta biyo bayan laila kamar me tsoron wani abu zai iya kamata,tana jin laila na masa sannu da zuwa sai itama tabi sahunta,ta kuma sulale da niyyar wucewa dakinta,saidai ya tsayar da ita da tambayoyi kan karatunta,abinda ya bawa laila damar wucewa ta barsu su daya a wajen.
Sallamar hisham daga bakin qofa ya ja hankalinsu duka,suka hada idanu da dukka su biyun,take fara’ar dake saman fuskarsa ta bace bat,ya fara shigowa falon cikin rashin walwala yana faman shan qamshi.
Kowa a cikinsu cikakken matashi ne mai jin kansa,wanda ya hada komai da komai,musabaha sukayi da juna kowa yana dauke wuta,ba kamar yadda suka saba ba,har zuwa sannan kan maimunatu yana qasa,ta yiwa hisham sannu da zuwa,maimakon ya amsa,sai ya koma da baya ya zauna cikin daya daga cikin kujerun falon yana cewa
“Je kitchen ki kawomin ruwa” a hankali ta tashi tana jin wani nauyi na raguwa daga cikin zuciyarta,zamanta a wajen tana jinta ne kamar cikin wani matsatstsen keji ne da babu sakewa.
Shuru ne ya biyo baya a falon,hisham na danne danne a wayarsa,khalid kuma yana kallon news,kowanne da tunanin da yake a ransa game da dan uwansa,ba tun yau ba duka sun tsargu da juna,sun kuma fahimci mawuyaci ne idan basiu tarayya akan wani abu guda ba.
Ruwan ta kawo masa hade da cup,ya dauki gorar ruwan yana cewa
“Ba daga islamiyya kike ba?” Kai ta gyada masa
“Bita ce ta kamaceki ba ki zauna kina surutun banza ba…wuce daki ki ajjiye qur’anin hannunki” cikin jin kai da isa khalid ya gyara zamansa sosai yana kuma dubansa kai tsaye
“Dakata mana hisham?,wanne irin nonsense ne zaka same mu tare sannan kace ta wuce ciki?…. please kada ka shiga hurumin da ba naka ba” wani kallo hisham ya watsawa khalid sannan ya saki murmushi
“Nonsense?……hmmmm,dani da kai za’a samu wanda ya dace a gayawa hakan,wuce maimunatu tun raina bai fara baci ba”
“Ba zata wuce ba!” Khalid ya fada a tsawace,dai dai sanda anni ke qarasowa falon,ta bisu da kallo cikin mamakin yanayin data taras dasu.
To fa masu karatu,khalid dinne ko hisham?,ko kuma ja’afar?,waye zaiyi wining?,muje zuwa yanzu aka fara wasan
[