AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 83-84

 ??82 and 83??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Afham yana kuka yace “yanzu ameelah matar aurece amma tabarni na fara sonta”

Umma tana kuka tayi saurin katsesa dacewa ” tabbas matar aurece, kaga wannan shine mijinta, ta nuna hilal”

Afham yakara fashewa da kuka, nadama ta bayyana a fuskarsa karara yana cewa ” kaicona, dana kasa fahimtar iyayena, mesukamun amma nakasa bin umarninsu”, jikinsa yafara ja yayi yana yunkurin tashi,

A daidai lokacin likitansa yashigo dakin, yayi sauri zuwa gurin afham ya zaunar dashi yana cewa ” ina kuma zakaje, ai kafar taka bata isah takawaba”

Afham ya janye hannunsa daga rikon likitan yace ” kabarni naje gurinsa yakarasa kasheni, wlh banga amfanin rayuwata ba” yana nuna hilal da dan yatsa yana kuka,

likitan ya kalli hilal cike da mamaki yana cewa “to ai wannan shine ya kadeka, kuma shiya kawoka asibitin nan a lokacin daya kawoka bakamasan inda kakeba, kakoga da ace yaso kasheka da tuni ya kasheka”

Wani irin kuka mai kara ya kubucewa afham, tabbas yasan wannan ba komai bane face iftila i, ko ince kaddara, yayi nadama sosai akan abinda ya aikatawa iyayensa,

Abban ameelah yagagara yin kuka edonsa suncika da kwallah, da sauri yafita yakoma dakin da ameelah take,

Afham yayi nadama sosai, yaso abarshi yaje gida amma likitan sa yahanashi, tare dacemasa sai yayi kwana ukku kafin yatafi,

Umma taja hilal sukabar dakin da afham yake suka dawo dakin da ameelah take,

ran umma yabace sosai dashigowar su dakin da ameelah take tafara masifa ” wlh ameelah kin wahalar da hilal, kin hanashi samun natsuwa a gidan sa, takara daga murya tana cewa “Daman Allah baya hukunta Azzalumi da laifi mai sauki sai wadda yasan baxai iya dauka bah, ta juya gefen hilal, a lokacin yadaina kuka amma zuciyarsa cike da kuna, umma tace ” karka kuskura kakara barin ameelah takoma Gidan ka tun kafin ta farfado ka saketah”

Hilal yadago kansa da sauri yace ” a a ummana ai baa yanke hukunci cikin bacin rai kibarta tafarka, inason nasan meyasa taci amanata”

umma tayi saurin cewa ” wani irin kanaso kasani ai kasani kawai bata sonka ne”

Hilal yamike tsaye yanaji ajikinsa bazai iya sakin ameelah ba, har yanzu yana sonta, “ummana kiyi hkr tafarfado duk wani hukunci daya dace a yanke sai a aiwatar”

Jin kalamansa yasa ran umma yakabace tsaki kawai taja, sannan tajuya takamo hannun hajna sukar dakin, hilal yanata kiran sunanta amma taki saurarensa,

Suna fita daga asibin suka tare napep suka koma gida..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button