GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
Godiya ta tabbata ga Ubangijinmu daya halicci alk’alami, yasanar da bawa abinda bai saniba.
Salati da aminci da d’aukaka su k’ara tabbata ga farin jakada,babba d’an Abdullah Muhammadu-Sadiqul-amin,da alayenshi da sahabban shi da wad’anda ke kan tafarkinshi har zuwa ranar rarrabe tsak’anin k’arya da gaskiya (Alk’iyama).
Godiya ta musamman ga Umar Dalha.Dakai muka kai ga gaci.
Kima:-
Kimarku muke gani Katsinawan Dukko d’ak’in kara,mun gaisheku gaisuwar kima, musamman Maskawan k’aramar hukumar Funtua da ahalin Muhammadu Me-ruwa dana Tankon Marka anan BCG,dana garin Gadagau.

Dan tunawa da:-
Gwanarmu a duniyar marubuta littafan Hausa.
Marubuciyar ????
{Dare ga mai rabo…}
Halima Abdullahi (Amma).

My One & Only Aminu A.Baba.

Lovely Sister Badi’atu Ibrahim.

Son Aliyu Yahya Namadi.

Little peerless Ali Yahya Namadi (Malam Garga)

Ubangijinmu ya kyautata makwancinku????????

Sadaukarwa:-
Ga d’aukacin Hausawa da Fulani…musamman Ya’yan Ibrahim ako ina kuke a fad’in duniya…????

…GWAJIN DAFI ????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na d’aya.

A kwance yake cikin damuwa, hawayen da suka cika idanunshi suka fara zubowa ta gefe da gefen fuskar shi suna gangarawa jikin matashin daya d’ora kai,a haka bacci ya d’aukeshi.Da sallama tashiga dak’in,kwanan abincin tabud’e, yananan yadda tazubashi, ALLAH ma yasa ya bud’e ya ga abinda yake ciki,da sanyin jiki tad’ago tana kallanshi,bacci 6arawo kamar yadda ake fad’a,to da alama saceshi yayi,tagirgiza kai cikin tsantsar k’aunarshi da tausayin halin da yake ciki,komai yana nan rad’am kamar yan awannin da suka shud’ene abin yafaru.Tausayin shi yadad’a mamayar zuciyar ta,dak’yar tamik’e daga tsugunan zuwa d’akin-girki tad’ora musu abincin rana.Bata koma dak’in ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar azahar daga mabambantan masallantan unguwa.

“Julaib… Julaib… Julaib…
Cikin natsuwa take kiranshi.Dak’yar yabud’e idanunshi da sukayi jawur saboda damuwa ga kuma bacci me nauyi daya kamasu.Tad’anyi murmushi”yi hak’uri na katse maka bacci lokacin sallah ne yayi.Yabita da kallo kamar bai fahimci abinda tafad’a ba.Tabud’e baki zata sake magana sai kuma tayi shiru tawuce dan sauke nata faralin.
Yana dawowa daga masllaci takawo mishi abinci “Ta kalleshi,barka da dawowa” a zuba maka yanzu ne?”shiruma amsace. Yad’auke kai daga kallan da take mishi.Da sigar rarrashi tazauna agefenshi”Julaib… Kayi hak’uri,zama da yunwa ba shine mafita ba,ba shine zai magance damuwar zuciyarka ba,zama da yunwa k’ara dagula maka lissafi kawai zaiyi, Dan ALLAH Julaib kadaure kaci kome k’ank’antar shi zai samar maka da natsuwa, natsuwarce kuma zata ba ka dama na tsayawa kai da fata wajan yawaita addu’a agaresu.Tazuba mishi faten waken dayaji kayan had’i k’amshinshi yagauraye d’akin.”Dan ALLAH kadaure kaci, tamik’a mishi farantin amma yak’i kar6a, tabishi da kallo tana murmushi “To abaki zan ba ka? Tad’ibo a cokali indai hakan kake so ni a wajena abune me sauk’in gaske,takai cokalin tsakanin la66anshi na sama dana k’asa”Haaa bud’e bakin ka kaci kayan k’arin lafiya da gina jiki.

Dakata haka malama!
Yajuyo da 6acin rai me yawa a tashi fuskar yana mata wani irin kallo data kasa fassarawa”ni na ce miki inajin yunwane?Ko nasafe ban ciba amma kin sake dafo wani saboda almubazzaranci?Tabud’e baki zatayi magana yayi saurin katseta”Keee! Kwashe kayanki ki fita bana san hayaniya.!Yahaye gado kanshi na mishi wani irin matsanancin ciwo kamar ana buga mishi guduma.
Tabishi da kallo cikin mad’aukakin mamaki,tsawon zamansu da duk halin-ko-inkulan dayake mata tana mishi uzuri,akwai damuwa me yawa atare dashi,to amma yau itace rana ta farko daya 6ata mata rai,cikin raunin murya dake shirin fashewa da kuka tace”Julaib… Hawaye masu d’umi suka zubo mata sharrr… Julaib…dama na san baka so na,to yau na dad’a tabbatar da hakan,na zama maka matsala ko?Adole kake zaune dani ko? Tasauke numfashi toh, ai ALLAH yanaji yana kuma gani na yi iya iyawata dan kawar da damuwar zuciyarka amma hak’ata bata tadda ruwaba,na sani za fi da rad’ad’in da kakeji bazai ta6a barin zuciyarkaba matuk’ar kana numfashi a doran k’asa, to amma ya kamata ka sassautama ranka,”Shekaru uku ba kwanaki uku bane”A shekara kwanaki d’ari uku da sittin muke dashi,to kwanakinnan sun ninka kansu har sau uku,kaga kwanaki dubu d’aya da tamin,kwanakin da sukayi a mace kenan”kukan mutuwa baya dawo da matacce”kasama ma zuciyar ka salama kayi rayuwa kamar yadda kowani d’an Adam me numfashi a doron k’asa yake yinta.
Julaib…to wai me yasa baka jin tausayina na mace me raunine?Tasake binshi da kallo sai kuma ta gyad’a kai,saboda kawai baka so na?To shikenan amma ina so kasani ni har kwanan gobe ina k’aunarka duk da bana samun irin kulawar data dace,ni na yadda da abu daya,aure bautar Ubangijjne dan haka zan cigaba da dauriya dan nima kamar yadda Abbana yafad’a min”ina kwad’ayin babban rabo a gidan gaskiya(Darul-karamah)ni zan sauke nauyin dake kaina,amma tunda ba ka san ganina,ba ka san abincina,ba ka san hayaniya da duk wata kulawa tawa to ko Insha-ALLAH zan kiyaye, zan killace kaina a d’akina,amma fa k’ofata a bud’e take ina maraba dakai,a duk lokackin dakake da buk’atar tallafina kasanar dani kai tsaye,ni kuma zan baka tallafi irin wacce tadace da buk’atarka, karambani ne dai bazan kuma ba tunda kai ba a maka gwaninta…
Tajuya da gudu zuwa d’akinta, gado tafad’a tana wani irin kuka, kukan data kasayi agabanshi hawayen sharrr…sharrr…suke zubowa, tad’aga hannayen ta sama”Ya ALLAH kataimaki mijinah…kayaye kunci da damuwar zuciyarshi, kamaye hakan da natsuwa…Ya ALLAH Ju..Jul.. Julaib..d’in…sauran kalaman suka mak’ale saboda kukan yaci k’arfinta,takifa fuskarta a jikin matashin hawayen nacigaba da zubowa.
Kalamanta sun sanyaya mishi jiki, yarintse idanunshi da k’arfi yana jin kanshi kamar zai rabe gida biyu,”Wayyo ALLAH nah?!Yafad’a a wahalce yasa tafukan hanneyen shi yak’ank’ame kan,jijiyoyin wajan sun fito rad’am kamar shatin bulala suna kuma harbawa da k’arfin gaske. “Wai…Wayyoh ALLAH…!Sai yafara fad’in “Babu tsimi babu dabara sai ta Ubangijjnmu.wucewar wasu dak’ik’u ciwon kan yad’an sarara mishi…sai kuma zuciyarshi tafara tunatar dashi.
“Iyayanta sun maka halacci, sun maka karamci,sun taimakeka a lokacin da kake buk’atar taimakon,lokacin da ba ka da kowa ba ka da komai, lokacin da ba ka san a wace duniyar kakeba.
Ruqayya matarka tana sanka tana k’aunarka,ka ga haka,ka kuma san da haka tun ganin farko daka mata bayan ka bud’e idanunka tsawan kwanaki,makonni da watanni a wata duniya daba zaka bada labarin wani abu guda d’aya na cikin taba,idanunka da ita suka fara yin tozali,haba Julaibib wannan ba halin girma bane,dan halal ai baya manta alheri,sai dai me halin kaji”Ci ka goge baki”abinda yake damunka bai shafe taba,ba ita takar zomo ba bai kamata ta d’auki rataya ba…
Kai musulmi ne kayi imani da k’addara kuma yana daga cikin cikar musulunci, wannan al’amarik’addararrene tun daga lauhul-mahfus.. Zuciyar shi tacigaba da tunatar dashi. Yasauke numfashi da ajiyar zuciya, k’irjinshi ya mishi nauyi yana kuma mishi suya,yahad’iye wani zazzafan abu kamar garwashin wutan da aka bad’e shi da dakakken barkono d’an munci.
Yamik’e zaune dak’yar sannan yaziraro k’afafunshi k’asa zaije ya rarrashi Ruqayya dan yana jiyo sautin kukanta, amma jirin dake shirin kaishi k’asa yasa yakoma yazauna ranshi ba dad’i…Yanzu ace mahaifin Ruqayya yashigo,ya zaiji idan yajiyo kukanta?Tabbasss ko bai nuna ba amma bazaiji dad’iba,gaskiya iyayanta sun maka karamci fa.Yajijjiga kai cikin gamsuwa,sai yamaida tafukan hannayenshi yarufe fuskarshi cikin tunanin rayuwarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Zonkwa ne shalkwatar (Headquater) k’aramar hukumar Zangon-Kataf d’in kudancin Jahar Kaduna.Babban garine matattarar jama’ar sauran jahohin Nigeria da sauran yankunan nahiyarmu ta Africa,mutanan Zonkwa wayayyun mutane ne saboda masu ilmine,babban abun sha’awar,yadda ake zaune lafiya duk da tarin bambance bambance ta fuskar addini da al’adu,ga kuma k’asar noma me albarka.Manyan yaran wannan yanki guda biyu ne Kaje(Kajawa)amma bayan yak’in Zangon-Kataf sai suka zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Bajju.
Baranzan da matarshi Zamburan sune asalin tushen Kaje,su d’in mafarautane da suka taso daga yankin Bauchi da Jos,ance saboda sunk’i kar6an jihadin d’anfodio.ance kafin su k’araso nan, matarshi Zamburan da wasu daga cikin tawagarshi sun mutu,amma ita Zamburan ta mutune a garin Forest sai sukazo suka kafa sansaninsu a saman dutse suna kiran wajan da Kufai(Kufayi) kamar yadda akasan maguzawa nayi a can bayan gari, amma yanzu gine gine ne masu ban sha’awa awajan na sarkinsu (Agwam Bajju) hausawa masu yawan fatauci suna zuwa harkar cinikayya irin ta da,ta bani gishiri in baka manda a tsakaninsu,ga zaman lafiya, zaman lafiyar da tasa idan sun shigo cikin gari talla sai da kayayyaki kamarsu citta,daddawa,zuma dasauran dangogin su,indai kuna shiri kukace kuna son yarsu ko d’ansu to ko Insha-ALLAH zasu baku sun kuma zama naku har abadan duniya,lokaci zuwa lokaci idan sun shigo cikin gari za suzo suganku, kuma zaku kaisu wajansu lokaci zuwa lokaci.ALLAH Alhakimu sunk’i musulunci,amma sun bama musulmai kyautar mutum sukutum da guda,sun kuma san musulunci da sallar za suyi,sai su taso su girma suna musulmai,d’aya daga cikin k’ananan yaran da suka taso a cikin musulunci yar asalin k’auyan Narom ce…Itace Khadijatul-kubra inda wasu bayin ALLAH mutanan Daura su suka nuna soyayyarsu gareta mahaifanta kuma suka yadda suka bar musu ita,Bintan Daura tazama uwa a wajanta,mijinta Garban k’aura yazama uba a wajanta, tagirma suka mata aure itama ta hayayyafa d’aya daga cikin ya’yan data haifa itace kakarsu Sudaida tawajan uwa,kuma shi Abubakar (Garban k’aura) aikin d’an sanda yakawo shi garin Zonkwa shekaru masu yawa,suka zauna a gidan Amasaye itace kakar,kakarsu Sudaida ta wajan uwa.
Asalin wad’anda aka tarar a k’waryar cikin garin Zonkwa Fulanine masu kiwon shanu,da mutane suka fara yawaita sai suka tashi suka dad’a nausawa cikin daji kamar dai yadda al’adarsu take, dan shanunsu su samu wadatacciyar ciyawa da ruwan sha,ba tare da sun takurama wani ba,shima kuma bai takura musu dasu da shanun suba,Ance adai-dai wajan da aka tarar da Fulani makiyayannan anan wajan aka gina musu k’aton masallacinsu na Juma’a kuma masallaci na farko a garin,kusa dashi aka gina gida da Limamin da masarautar Zazzau ta turo musu dan yadinga musu limanci,yana kuma karantar dasu addini.
Ibrahim Nabarandi asalin Bakatsine ne masu yawan fatauci,bayan tashin Fulanin nan shine yak’afa cikin garin Zonkwa,gidanshi babban gida ne kun dai san zamanin da daba siyan fili a ke yiba kai zaka shaci yadda yamaka kayi gininka, shine yazama Sarkin hausawa,duk wani bak’o a gidanshi yake sauka kafin a bashi muhallin zama.Manyan zauruka(soraye) irin nada sun kai goma anan duk wani bak’o indai namiji ne zaiyi zamanshi,mata kuma akwai d’akuna a cikin gida da aka gina musamman saboda irinsu,suna mishi kirari shi Ibrahim Nabarandi da:

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button