GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lallai zasu tattauna cikin tsanaki,ai yana da ilmi zai kuma fahimci zama da auren zai fi mishi fiye da yak’arasa rayuwar a haka,tsananin martaba aure irin na bahaushe yasa kome tsufan mutum sai kaga yayi auren koda kuwa irin na butane kamar yadda suke fad’a.

Wata d’aya bayan nan Julaibib yana zaune a d’akin-shakatawar gidan shi yana kallan kwanukan abincin da Misbahu ya ajiye,duk da yabar gidan amma kullum ta ALLAH basa gajiya sau ukun nan sai an kawo mishi abinci, yanzu idan yace a daina kawo mishi bai san yadda zasu fassara al’amarin ba, abu d’aya zaisa a daina kawo mishi wannan abincin shine suga macen aure a gidan,shi kuma bayajin wani aure a ranshi,jiya ma abinda Maimun yagama fad’a mishi kenan wai da yana da ‘ya mace da tuni ya aura mishi ita”Julaibib yayi murmushi”haba farfesa gwamma da ALLAH ma yasa baka da ita ‘yar tawa zan aura?Ya jijjiga kai”ai hakan shine dai-dai taci karanta ba babbaka.

Ranar Juma’a bayan an sakko daga masallaci Julaibib ya tsaya suna gaisawa da Alhaji Salim,yakalleshi maganar Iyali har yanzu dai shiru bakace kome ba,yad’an shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi”zan duba…ko kuma ma dai Alhaji kasamo min yar mutunci a unguwar nan tunda ka dad’e a unguwar ka san yar babban gida.

Alhaji Salim yayi murmushi”fad’uwa tazo dai-dai da zama,yakalli Julaibib “ka bani wuk’a da nama nagode,amma wani hanzari ba guduba idan kuma kaga yarinyar kaji bata kwanta maka ba fa?Ya amsa kai tsaye”zata kwanta min ko yaya take dan na san baza kamin za6en tumin dare ba, zan aureta zan kuma girmamata.

Alhaji Salim yasake kallanshi”yanzu me zakayi a gida?Yad’an motsa kafad’a”bakome.To zo muje gidana akwai maganar da zan fad’a maka suka shiga mota suka tafi.

Sai da suka gama cin abincin rana sannan Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa”Julaibib zan baka auren ‘ya ta Ummi kana son ta?Julaibib yaji wani irin yanayi na girma da nauyin Alhaji Salim,ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya wallahi,Ummi a yadda ya karanceta ai bata da wani aibu tana da natsuwa da hankali,gata da ilmi,kai ko da ace ballagazace a dai irin karamcin da Alhaji Salim yamishi to wallahi ba abinda zai hanashi auren ta “Insha-ALLAH kuma sai ya d’orata a kan hanyar dai-dai bare kuma a kauwamen ta take.Ya amsa cikin girmamawa”to Alhaji nagode ALLAH yasaka da alheri.

Yagyad’a kai”Julaibib ya kamata kasan wacece Ummi da kuma mahaifiyarta.Yayi shiru yana sauraro…Alhaji Salim yabashi labarin aurenshi da Sumayya,’yar data haifa mishi da kuma rasuwarta…Ni tun ranar daka farfad’o na tambayi sunan ka kace min Julaibib na gane ko wanene kai,da irin k’aunar da marigayiya take maka,dan haka Ummi yar wajen Sumayya(Kasham) ce,ita zan baka idan kaga kana sonta.Julaibib yabud’e idanu dan mamaki…zuciya da k’wak’walwarshi bangaren adana bayanai ta koma baya da gudu tana tariyo mishi kome daki-daki tun had’uwarsu ta farko da Kasham a Gidan-Waya ranar da sukaje yin registration… Har zuwa ranar data aiko mishi da wasik’a,ruwan zamzam,farin miski da dabinon ajwa da abinda tarubuta mishi”Musha ruwa lafiya…ranar azumin ashura tara ga watan farko na musulunci Muharram…Da abinda ta rubuta a k’arshen wasik’arta

Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)

Yayi shiru yana tasbihi a cikin zuciyarshi”ALLAH Alhakimu gwanin iya hakima, ALLAH buwayi gagara misali…Qudirarka da yawa take”ni Julaibib Abdullahi d’ansarai ni zan auri ‘yar da Sumayya ta haifa?Lallai ba wanda yasan abinda gobe zata haifar sai ALLAH,dan shi wallahi har ya manta da wata Kasham da Sumayya a rayuwarshi…A hankali mafarkan da ya dinga yi na shekara da shekaru suka dawo mishi wannan mafarki me ban mamaki da yarasa gane ma’anarshi

“Kasham da yake gani cikin shigar kayan fulani idan tayi magana sai kuma yaji muryar Sudaida.

Wannan yana nuna Sudaida matar shice,haka kuma zai auri wata kenan me alak’a da Kasham d’in?Gashi kuwa ya tabbata ‘yar data haifa a cikinta…kayan fulanin kuma yana nufin kenan Bafulatana ce?Yajijjiga kai”ko shakka babu tunda Alhaji Salim Iyayenshi Fulanine amma girman birni dan ko Iyayensu basuyi kiwon shanu ba bare kuma su… La’ilaha’illallah.

Sai yasake tuno ranar da Maimun yake fad’a ma Musaddiq mafarkin da yayi”Wai shi da Kasham ne suke kiwon shanu a wani k’aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi”Musaddiq yakyalkyale da dariya”d’ansarai fulani ka koma har matarka take tayaka kiwo saboda tsabar k’auna?A lokacin bai kula suba.Yayi ma Alhaji Salim godiya sosai,amma har yabar gidan bai daina mamakin wannan al’amarin ba.

Bayan tafiyarshi Ummi tashigo d’akin da sallama,ta zauna tana kallanshi”Abbana kace za muyi wata magana idan ka dawo daga masallaci, yana murmushi yace ban manta ba Ummi,ya san yana da yak’ini zata amince,sai yafara mata nasiha akan biyayya ga Ya’ya a wajen Iyayensu wajibine matuk’ar abinda suka zo dashi bai sa6ama shari’ar musulunciba,a hankali kuma yafara kambama halayenta na k’warai, ganin tana ta murmushin jin dad’i,sai ya maida abun zuga”ai na san baza ki bani kunya ba;baza ki watsa min k’asa a cikin idanu ba,ni a duniyar nan ban ta6a ganin yarinya me tsananin biyayya ga mahaifanta ba irinki,nima kinga shi yasa nake miki wata irin k’auna mumaiyiza(ta musamman)

Tagyad’a kai”tabbasss ta yadda Abbanta yana mata k’auna ta musamman d’in dan kome nata na musamman ne wallahi a wajen shi. Cikin d’oki tace”me kake so in maka ne Abbana? Yakalleta cikin kulawa”aure zan miki Ummi,kuma ni da kaina na za6ar miki mijin.Da sauri ta sunkwui da kai dan batayi tsammanin abinda zai fad’a kenan,tanajin wata irin kunya na lull6eta.

Yacigaba da magana “shekaru da yawa da suka wuce ina da labarin shi, mutumin kirkine… Kuma nima a yanzu nayi nazarin shi tsafff…naga hakan ganin idanuna,hasashena yana bani zai rik’eki da aminci da amana,burina kullum a kanki Ummi shine kiyi aure,kiyi bautar cikin aure tunda ibadane, ranar alk’iyama ki samu sakamako mafi kyau da daraja,kisamu shiga darul-karamah (aljannah) aljannarma ina miki kwad’ayin samun mad’aukakiya (firdausss)

Yayi shiru yana kallanta”Ummi kiyi magana mana ai ba auren dole zan miki ba,idan kina da za6inki na kuma bincika naga shima mutumin kirkine,toh shi zan aura miki,zan kuma ba wancan hak’uri na san zai fahimceni,tayi k’asa da murya cikin jin nauyinshi”Abbana ina fata in biku in muku biyayya a duk abinda kuka umarceni ko da bana so,zan tilastama kaina so,dan na san baza ku cuceniba,dan nima inaso agaba a bini,na san kuma sai na biku na samu albarkanku,nima zanga da kyau a rayuwata ta gaba.

Yayi lallausan murmushi yana yaba hangen nesan ta”toh kin yadda da za6in Abban naki koda mutumin me gemu da k’asumba cike da furfura kamar na Abbanki?Tasake sunkwui da kai”shi wallahi haka Abba yake magana wasu lokutan sai yaba ka kunya.

Haka rannan yace ma Mamansu wai tana ta wani shashshare shi,to shi gaskiya ya gaji da wannan shariyar,aure zai k’ara kuma sa’ar Ummi zai auro.Ita kuma ta galla mishi harara”dan ALLAH ka auro wacce bata kai Ummi bama.Sai yafara dariya yakalleta”ke Ummi ki zama shaida ai kinji abinda tace ko?Batayi magana ba,sai guduwa d’aki tayi ta barsu,yanzu ma tashi tayi yana kiranta amma bata dawo ba.Alhaji Salim yana da shak’uwa sosai tsakanin shi da Ya’yanshi,dan haka zaiyi wuya yafad’a musu abinda yake so na ayi ko abari kaga basubi umarnin na shiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button