
Ta tausasa murya”Aunt basakut (kiyi hak’uri)Kuka bazai dawo da Bobby ba”I know it’s hurt, but you’ve to bear it,since you already know that sooner or later each and every one we will go back to our creator…tacigaba da rarrashinta har tayi shiru amma bata yadda ta mishi addu’a ba dan musulunci ya haramta hakan ga duk wanda ya mutu bai yadda da manzancin Manzon ALLAH Sallallahu alaihi wa’ahlihi wasallam ba.Rahab taji dad’in kalaman Ummi sosai “Thank you very much my dear Ummi for this condolence.Sukayi sallama.
Sunyi shirin tafiya Umrah a can zasuyi azumin ramadana,d’aya ga wata kuwa jirginsu ya d’aga zuwa k’asa me tsark’i,garin Manzon ALLAH me safa me marwa,garin dabino da ruwan zamzam… Ruwan zamzam me tarin albarka da duk buk’atar da kashashi zata biya Insha-ALLAH.
Dabinon ajwa sukaci da tataccen ruwan inibi da tuffa,bayan angama kiran sallar magriba, shi da Ummi suka kalli juna suna murmushi yad’aga hannayenshi sama dan wannan lokacin amsa addu’a ne kafin a tada sallah”Ya ALLAH bayinka da aka kashe bada hakkin suba a ko ina suke a doron duniya al’ummar Manzon ALLAH! Ubangijinmu albarka wannan rana,albarkan wannan d’aki na ka me alfarma ka yafe musu!Ya Ubangijinmu mahaliccin kowa da kome jinin nan nasu daya zuba a doron k’asa,kasa yazama sanadi na samun d’aukaka da darajarsu!Ya Ubangijinmu kasa hakan yazama sandin shigarsu darul-karamah (Aljannah) Jannatul firdausss al’a’ala.
“Ya Ubangiji!Miyagun da suke ma al’ummar manzonka kisan gillan nan idan wad’anda za su shiryune to ALLAH na rok’ek’a kashiryar dasu, idan kuma 6atattune abadan Ila yaumil k’iyamah… ALLAH! Kai ka haliccemu gaba d’aya, kuma gareka zamu koma gaba d’aya mun bar kome a hannunka kamana maganinsu.Ya Ubangiji! Muda mukayi saura a raye da imani to ka k’ara inganta mana imanin,idan kuma ka tashi kar6an rayukanmu muna maka magiya da sunayenka mafiya kyau,daraja da d’aukaka to ka kar6i rayukan namu muna masu imani,ranar rarrabe tsakanin k’arya da gaskiya, ranar da kud’i da Ya’ya basu da tasiri sai dai wanda yazo da ayyuka nagari…!ALLAH kahad’a fuskokinmu a darul-karamahhh…
Ya ALLAH!Me saukar da littafi,me gaggawan sakamako!Ka karya k’ungiyoyin abokan gaba.Ya ALLAH!Ka karyasu,ka girgiza su…!!!
Ummi dake gefenshi itama ta d’aga hannayenta sama tana amsawa da”amin Julaib… Aminnn ya rabbi… Aminnn… K’arshe.
Kome yayi farko tabbasss yana da k’arshe.Mu Ya’yan Ibrahim Godiya muke ma ALLAH marashin k’arshe daya nufemu yau da kammala rubuta labarin Julaibib Abdullahi d’ansarai ZAKARAN GWAJIN DAFI.
19 Rajab 1441
13 March 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs
Saudat Ibrahim Yahaya????kisa ranki a inuwa kamar kin mari uwar Soja…Mu Ya’yan Ibrahim zamu rakaki gidan d’ansarai har d’akin-shak’atawa ki zauna kisha bak’in shayi…sai ki tambayeshi baki da baki dan wanga batu????gaskiya ba damu ba gaad’a da fatalwa????
Muhad’u a sabon littafinmu????
Dasabon gini…
A Facebook:
Ibrahim’s Daughters Novels.
Insha-ALLAH.
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!!!
Baba Aminu Inuwa Ibrahim(Wambai)
Jiya Alhamis ALLAH yamishi rasuwa…yan uwa kutayamu rok’a mishi gafarar Ubangiji,jinyar da akayi yasa k’arshen wahalar kenan????????
ALLAH YAJIK’ANSHI!
ALLAH YABASHI TABBATA!????
YAU JUMA’A AKA KAISHI GIDANSHI NA GASKIYA… D’AKI A CIKIN K’ASA! SHIKENAN FA RAYUWAR????
Alhamdulillahi alakullu halin Wa’a’uzu billahi min amali ahalin nar.
Subhanakallahumma wabihamdika ashhadu anla’ila ha’illa’anta astaqfiruka wa’atubu ilaika.