
Kasham dasuke zaune a benci ita da wasu malaman suna hirarsu ta k’walamamata kira tayafito ta da hannu.Sudaida tadanja tsaki”nifa wannan malamar tana neman shigarmin hanci da k’udundune. Suka sake kyalkyale da dariya”kila yanzu ne zata hukunta ki a bainan-nasi.Dammm…zuciyarta tabuga tsoro ya baibaye ta, kuma kila hakane,ba mamaki tajuyo maganganun sune tunda dama ba a hankali sakayi taba.Bata kulasuba tamik’e tana Istirja’i.
Ga ni tafad’a cikin ladabi “dole gyad’a tai mai idan tak’i tasha matsa”Kasham tabita da kallo,haka kawai taji tana santa,tunda k’anwar masoyin tane.Lidiya tace”meye haka kuma?Kin kira yarinya kin tasata a gaba da kallo kamar wata magiji.Tasauke gwauran numfashi, tasa hannu a jaka ta zaro kud’in dabata k’irgaba tamik’a mata”ungo kije kisai abinda kike so. Sudaida tabita da kallan tsoro da mamaki kamar yadda sauran malaman sukayi “to da wace hujjar nasara zaiyi hawan k’aho?
“Kar6a mana Sudaida.
Tajuya ba tare data kar6a ba”bar abinki nima ina da nawa.Lidiya tadaka mata tsawa”ke k’aramar mara kunya dawo.Sai kawai tasa gudu.Tayi kwafa zamu had’u dake gobe aji.Kasham tahad’a tafukan hannayenta”Dan ALLAH Lidiya karki daketa dan bata miki kome ba.How dare you Kasham kice bata min kome ba ni sa’ar wasan tace dazan kirata tak’i zuwa?Saboda ita kanwar wancan me shegen girman kan tsiyan?To niba ruwana abu kazan uban ta zanci.Haushi yakama Kasham sai kawai tace”ai ko abu kazan uban ta yafi k’arfinki har abadan duniya.Cikin tafasar zuciya Lidiya tanuna kanta da yatsanta”Kasham ni kikema wannan rashin mutuncin saboda wasu tsinannun hausawa?Ban miki wani rashin mutunci ba, magana kikayi ni kuma na baki amsa.Banda shiga sharo ba shanu ina ruwanki da ita?Ko ke kika kirata? Kome tamin ni naja,idan naga dama in mata hukunci,idan naga dama in k’yaleta bai shafeki ba”wannan sa kai a uku ne takaban siriki.
Suka farar cacar baki malamai suka shiga tsakani daga nan taran yawatse dan an koma aji. Takoma Staff-Room dan bata da darasi a kowani aji har a tashi sai kuma gobe.Tabishi da kallo cikin harara dan kwana biyu taje yajin aiki akanshi, duk yadda takejin san shi ba ta kulashi sai dai tayita kallanshi.Tamaida kanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana wata kisima a zuci “Julaibib kyakkyawane”Melanin beauty”tayi nazarin shi dakyau baya san hayani,wani abun ba wulak’anci yake mataba haka halinshi yake bashi da yawan magana,tana so ta aureshi tahaifi yarinya me irin kwantaccen gashinshi, tana san Julaibib ta rasa ya zatayi da rayuwarta”Ciwon so” data san inda zata nemo maganin shi tasha ta warke daga san d’an Sarai ne?
“Oh my God!, ta dunk’ule hannu ta naushi iska”
Dasauri tamik’e zuwa wajanshi d’ansarai takira sunanshi.Yad’ago yakalleta yacigaba da abinda yake yi,sai ta rasa me zatace…Dan ALLAH bani aran correction pen. Yaciroshi a aljihun gaban rigarshi daya soke yamik’a mata.Tashafi hannunshi sannan ta kar6a “nagode idan nagama zan kawo maka.Yagirgiza kai “Kirik’e kawai.To nagode,tasa ajaka dama neman magana ne itama tanada nata fa.
Duk ranar alhamis suke House Assembly, wani ikon ALLAH sai akasa Kasham da Julaibib a house d’aya,Sudaida ma anan take. Kasham a matsayinta na sabuwar malama ita tafara musu bayanin kanta da yar nasiha,sai malamai biyu duk yan TP sai Julaibib cik’on na hud’unsu.Cikin natsuwa yake musu bayani sannan yad’ora da nasiha a kan su dage da karatu ba kawai sai lokacin jarabawa ko za ai wata kaci-kaci da muhawaraba, kullum Ku zama masu nazari da bincike da tambayar duk abinda baku ganeba, da wanda baku saniba da hakane ake samun ilmi me yawa,ita k’wak’walwa d’an Adam ne yake cikata da aiki,idan kuma baiyi hakan ba to ita zata cika mishi da abubuwa na shirme wanda bazai amfaneshi akaran kanshiba,bare har al’umma ta amfana,ina fata zaku dad’a sa k’wazo duk da nasan kunayi amma Ku k’ara, ina kuma fata zaku zama masu amana kamar yadda sunan gidan na ku yake “Amana House.
D’alibai suka d’auki tafi.a’isha da take bayan Sudaida tace”Amma gaskiya ina san Yayanki Sudaida,yanayinshi me sanyine,sukayi murmushi.Mr Julius shugaban house d’in shima yatafa mishi,yau bani da abin fad’a.Yanuna Julaibib da yatsa”This great teacher of ours has said all”.Yad’an bubbuga kafad’arshi sukayi murmushi,sannan yakalli d’aliban yad’an motsa kafad’arshi”shikenan you can go back to your classes” duk suka watse.
Maimun yakawo musu ziyarar bazata ranar juma’a da yamma,sun kuma ji dad’in haka sunata ba juna labarin makarantun da aka turasu har Maimun yasako mishi maganar Kasham…Yayi kamar badashi yakeyi ba.Zuwacan kuma yagirgiza kai”ni fa ba zanyi abinda zai zama min matsala ba,aure ba abin wasa bane, ba kuma yin auran ne yadameni ba,a ah samun matar data dace dani me mutunci da mutunta kai.Kasan ALLAH Julaibib Kasham tana sanka,wannan soyayyar da take maka zaisa tamaka biyayya tabi umarninka.Yagirgiza kai”Kyaleta kawai Maimun. Maimun bai kuma maganarba suka cigaba da hirar data shafesu har Musaddiq yafito suka tafi k’wadago neman halali.
Baranzan yajuya yana kallanta”Ke wai meye damuwarki ne?Wani haushin shi takeji gwamma tabar mishi d’akin dan batayi maraba da zuwan shiba,idan tazauna za ayi d’anyan aikine dan shima bashi da mutunci idan yana 6acin rai.A fusace tajuya zata fita,caraf taji yarik’o dantsen hannunta kamar zai k’aryata.
Tarinse idanu dan azaba. Yasunkuya akan fuskarta”sai kin fad’a min da uban wa kika fara soyayya da har kike guduna? Sake min hannu.Yasake rik’eta tamau.Sai fa kin fad’amin da uban wa kika fara soyayyah? Haushinshi yadad’a ninkuwa a zuciyarta Kawai sai tace da”Ubanka…bata gama rufe baki ba taji saukan mari hagu da dama,idanunshi suka kad’a jawur”za kimin rashin mutuncine?Uba na sa’ankine?Yafad’a da karfi cikin tashin hankali da alama allurar soja ta motsa.Uba na ko? Tagyad’a kai duk da a zabar rik’on data keji.Kikace eh? Yashak’eta,manyan idanunta suka fir-firto numfashinta yazo wuya,yasake kifa mata mari hagu da dama,sai da taga wasu k’ananan taurari sun tarwatse, gefen bakinta ya fashe,ji da ganinta suka d’auke na wucin gadi..
Wannene abin so?… A tari fitsari a wanke zawo?
18 Rabi’a Thani 1441
15 December 2019
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin ????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na biyar.
Dak’yar aka 6an6areta a hannunshi bayan tasha wahalar duniya.Yarafff… Tafad’a gado tana wani irin tarin wahala tana fuzgo numfashin ta dayake k’ok’arin kufcewa.Shima ya fuzge daga rik’eshin da akayi ana ta bashi hak’uri,yayi kanta,aka sake rik’eshi
Lidiya tashigo da gudunta dan bata san abinda ke faruwa ba yanzu aka kai mata rahoto”haba Baranzan kazama namiji mana, jarumin namiji me kwanan daji irinka me zai sa katsaya fad’a da mace?Kasham fa kwana biyu bata da lafiya ya kamata kamata uzuri.Anki a mata uzurin wa tafad’a ma bata da lafiya? Yabita da kallo tana kwance sambal,gashin kanta a hargitse kuma ta rame ba haka yasan Beauty d’inshi yar gayu ba.To kitashi muje asibiti. Shiruma amsace.Yad’ibo wasu damin kud’i yaba Lidiya wai tarakata asibiti ta tabbata an dubata ankuma bata magani me kyau.Tagyad’a kai tare da sara mishi “Yes sir tabuga k’afar damanta a k’asa.