
Bayan sun gama cin abincin dare.Alhaji Abdullahi yakalli Julaibib “d’ansarai na san ba abinda ke tsakaninka da wancan yarinyar amma duk da haka sai ka k’ara yin taka tsantsan,dan shaidan baya raina k’ofa,kai kace bazaka aure taba,ita kuma bata hak’ura ta daina bibiyarka ba.Kanemo mata kayi aure dan shine kwanciyar hankalinka damu kanmu,bana so kad’auki wani dogon lokaci ba tare da iyali ba.Yashafa kwantaccen bak’in gashin kanshi “Sannan ya amsa cikin ladabi.Amma cikin zuciyar shi inda kizo ke sak’ar wacece yake jin santa? Dammm…Zuciyar shi tabuga,yayi maza yakawar da tunaninta a,Yasauke gwauran numfashi ” Yau ake yin ta wai anyi da mutum ya ji”…
Hajiya takalli Sudaida da 6acin rai”Kai wannan yarinya da kafirin taurin kai take kamar mutanan farko,za ki d’auka kisha ko sai na sa6a miki? Ta turo baki gaba”ni fa wallahi na ji sauk’i”ke tafi can kinji sauk’i amma kwana biyu kina kwance?Ni na ta6a jin inda akayi haka? Baka da lafiya bazaka sha magani ba,baza a maka alluraba?To ko duk tsiyarki gobe sai kin tafi makaranta dan naga abun na ki “Tsiya ne d’inkin ludayi.
Ya shigo da sallama.Tabishi da kallo “Yaya Julaibib ina atilan dana ce kasiyo min”?Yayi kamar ba dashi take magana ba, yazauna a kujera suna gaisawa da Hajiya.Tad’anyi tsaki”ALLAH yasauwak’e maka wannan halin… Takauda kai daga kallan da take mishi tafara k’unk’uni saiga Sinan shima ya shigo”Tace yauwa Sinan kamar kasan ina mararin ganinka.Yagaishe da Hajiya tare da tambayar ya akaji da me jiki? A Alhamdulillahi ai taji sauk’i tunda har tana k’in shan magani, shekaran jiya da bata san inda kanta yake ba ai ina bata take kar6a tashanye ba musu ba gaddama.Sudaida ta turo baki gaba ni fa kaina ba inda yatafi yabarni muna tare har a k’abari.
Sinan yamatsa kusa da gadan da take kwance ta lullu6e jikinta da bargon Hajiya fuskarta kawai ta bari a bud’e.Yamata wani kallo”Sannu sarauniyar Sinan” tagyad’a kai cikin murmushi.Yafara mata magana k’asa-k’asa. Takyalkyale da dariya tad’an zaro idanunta”Kaiiii Sinan wallahi ba ruwana.Sai yamik’e tsaye daga sunkuyan da yayi a kusa da ita”Me zan kawo miki anjima”?Tad’an harari Julaibib caraf idanunsu yahad’u tadauke kai,sannan tad’an marairaice “atile”dame kuma?Sai kuma yaba kanshi amsa”da masoyin sarauniyar Sinan rake.Tayi murmushi” Wallahi nagode maka ba kad’an ba Sinan.Tad’aga hannu tana mishi adabo”adawo lafiya.
Filin wajan da malamai suke ajiye mashina da motoci taje,tad’are mashin d’in Shunkut dan yayi saiti da inda Julaibib yazauna a barandar d’akin malamai,tana kare mishi kallo…Tayi murmushi cikin sauke numfashi “Julaibib da ka san matsanan cin son danake maka wata kila daka ceci zuciya ta da take shirin yin gobara.
Holy ghost fire!
Lidiya tafad’a dan Kasham batama san tazo wajan ba.Akan wancan tsinannan bahaushen kina neman zama mahaukaciya”For Christ sake wai me yashiga k’wak’walwarkine? Lidiya kome zaki fad’a min indai akan son wancan bahaushen ne tamata nuni da inda yake zaune, to ina maraba dashi,kin sani tun ganin Julaibib a kuma kallanshi farko so da k’aunarshi suka mamaye zuciya ta,shi kanshi ya fad’a min uncountable times bazai aure niba and I don’t know why har yanzu nake jin kaunar shi deep down my heart”.
Tadafa kafad’arta ki tayani addu’a duk ranar da ALLAH yabani sa’a yashiga nan ta nuna tsakiyar tafin hannunta,yad’and’ani zak’i da gardin zuma ta,to wallahi na mishi katttt…kisan mummuk’e.Lidiya ta kyalkyale da dariya”gaskiya iska tana wahalar da me kayan kara,malama dame kama ake yin k’ota.Wancan me shegen girman kanne kike tunanin za ki yaudare shi?To yaushe ma yatsayi kulaki bare har hilarki tayi aiki akanshi? Wallahi kinga dai bana san shi amma na jinjina mishi ????zan kuma iya bada shaidarshi harkar mata baya yinta, dan da yanayi wallahi ko sau d’aya ne tun zuwanshi Gidan-Waya da mun sani,kema ai kin san mune idon gari a makarantar nan,wannan harkar sai sojanki Namamajo,ke dai kawai ALLAH yaganar dake,amma banda 6atan basira mutum yace baya sona to nima banga abinda zai sa ya kuma d’ad’ani da k’asaba tunda shi d’in ai ba mahad’in numfashi na bane,ko yaranmu d’aya dashi zan hak’ura in kyaleshi,bare wani hausawa me girman kan tsiya,shiba kowan kowaba dillalin kashi,kin sani ni nak’i jinin hausawa, ke ba hausawa kad’ai ba duk wani me sallah bana sanshi da inda k’arfin iko na rantse miki da ALLAH ba wasu tsinannun masu sallah dazasu zauna mana a gari.Taja tsaki fuskar nan tarine da 6acin rai ruwan kafircine zallah babu gauraye da haske da tausayi da Imani ko na sisin kwabo, jikar kajawace (Bajju) gaba da baya”bana san ma su sallah.Kuma ba yadda za kiyi dasu “sun zama kuturwar uwa dole a zauna dake.Kasham tabata amsa,sannan tasauko akan mashin d’in tawuce bayan aju-juwa da aka k’awata wajan da shuke-shuken filawowi masu ban sha’awa,tadinga bi tana tsinkosu kaloli mabambanta masu k’amshi tacika hannunta sannan tasa zaran ulu,ruwan hoda tadaure tawuce d’akin malamai zaman jiranshi.Dak’ik’a biyar da buga k’ararrawar canjin darasi sai ga shi yashigo,saida tabari ya zauna a kujerarshi yana hutawa ba ajin dazai kuma shiga sai gobe.Yakwantar da kanshi a jikin kujerar, idanunshi a rufe wani bacci me dad’i yafara shirin saceshi sai kawai yaji an shafa mishi wani abu a daidai hancinshi me wani irin k’amshin dad’i, yabud’e idanunshi da yanayin bacci har sun d’anyi ja.
Tamishi lallausan murmushinta “perceive the natural fragrance of this bounch of flowers.Tafurta hakan da wani salo irin na ta nayanga sannan tacire daga hancinshi ta d’ora mishi a saman tebur.Yakauda kai daga kallan da take mishi kamar kura taga nama.Wallahi yama rasa abinda zai ce mata.
Tayi k’asa da murya ganin wasu malaman sun fara sa musu na mujiya”ai nasan ban kyauta maka ba ko?Kai dai ba a maka gwaninta,d’an motsa kafada tayi “karka damu dani,kar kayi la’akari dacewa nice nakawo maka,tagirgiza kai kayi la’akari kawai da tarin amfanin da k’amshin furen filawa yake dashi ga d’an Adam.How I wish Jualiabib ka bani dama na nuna maka irin kaunar danake maka, tagirgiza kai cikin damuwa “How I wish ka tallafi zuciyata ka magance min damuwar cikinta…sai dai kash!Ban samu hakan ba,saboda baka san illar kaso a k’ikaba,tabbas daka san haka da baza kabari zuciyata tayi gobara ba.Tahad’a tafukan hannayenta alamar magiya “Don’t let the love that I have for you to go in vain please…!
Yad’ago yakalle ta,sai yaji wani abu ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar shi,har ya bud’e baki zayi magana sai kuma yagirgiza kai”a ah Julaibib daure kawai, maganin kar ayi to tun farko kar a fara”kawai sai yamik’e yabar d’akin.
Shunkut ya sunkuyo a fuskarta yana murmushi”Ke ki hak’ura dashi mana ai ba a soyayyah dole, yanuna kanshi da yatsarshi”ni d’in nan namiji ne duk abinda yake dashi namazan taka nima ina dashi,kiyadda kawai muyi soyayyah.A fusace ta tureshi”you fool! Dawa za kayi soyayyah Shunkut?Tayi d’as da yan yatsunta over my dead body.Tagalla mishi harara sannan taja mummunan tsaki”ruwa ai ba sa’an kwando bane”sai yajuya yana tafiya “Amma kuwa za kiyi 6atan 6akatantan…
A gajiye lik’is yashigo,gidan shiru dan Inna tana gidan Hajiya,yazauna yana hutawa, ya6alle botiren gaban farar rigarshi,yamaida kanshi jikin kujera tare da lumshe idanunshi sassanyar iskar bayan la’asar tana ratsashi. Mafarkan da kwana biyu nan yakeyi sun tsaya mishi a rai”Kasham yake gani cikin kyakkyawan kirar kalangunta,sanye da kayan fulani,gashinta yasha gyara ta tufkeshi a baya,amma kuma idan tayi magana muryar Sudaida yakeji”ya rasa kan wannan mafarki.