GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Hayaniyar shigowarsu Kamila yasashi bud’e idanunshi,aiko suka shigo sunata zuba surutunsu, sunata mishi tambaye- tambaye.Shigowar Musaddiq yasa suka koma tsakar gida suna wasannin su,yadaki kafad’ar shi”kai malam tashi da ALLAH magana nazo muyi. Uhun ina jinka.Musaddiq yabishi da kallo”Julaibib ka nemi a’isha kawarsu Sudaida mana tunda dama ta nuna tana sanka kaine baka bada goyon baya,tana da hankali kuma ko su Baba idan sukaji ita kake so za suji da…yatari numfashinshi a hasale “bata min a matsayin matar aure ba,dan haka akai kasuwa”.Yakalle shi da mad’aukakin mamaki”To me yayi zafi da har idanu za suci wuta haka? Tagyada kai “To yayi,indai har a’isha bata maka a matsayin matar aure ba to ashe gulmace da kai,kana kuma kallan mata za kuma ka iya za6a,amma da zarar magana ta tashi sai kace ba sa gabanka,to kuma harsu Baba sai sunji zancen nan.

Yanunashi da yatsa”Idan kai zaka min zaman auran ai sai in aureta.Yamaida idanun shi ya rufe, shi wai ma wacece wata a’isha?Wasu lokutan dai Sudaida tana fad’a mishi”a’isha tace tana gaisuwa”ko kuma a’isha tace kaza da kaza game kai,sai dai bazai iya tuno me take fad’a d’inba, dan ba itace a gaban shiba,shi dai bai san tana sanshi ba,dan ko Sudaida bata ta6a fad’a mishi wai a’isha tana san shiba, kila Musaddiq d’inne kawai yake san had’awa.

Sallar a zahar Julaibib yayi yagama azkar d’inshi sannan yafito daga masallacin makarantar,yau ba ayi wani karatun kirkiba saboda Inter-House ya kusa,ga dalibai nan sunyi rukuni rukuni na irin abinda suke so, suke dad’a yin gwaji (practice)yajingina da bishiyar giginya tare da rungume hannayanshi a kirji yana kallan Sudaida yadda take d’aga mulmulallan bak’in k’arfen discus da yadda take jefashi cikin k’warewa da nishad’i a bokan wasanta suna mata tafi wasu suna mata ihu dan tanayi yadda yakamata.Yayi murmushi yatuna lokacin da yake makaranta yayi wasannin kala kala,wasan kwallo ne bai ta6,a burgeshi ba wannan sai Musaddiq,saboda kwazanshi a fannin wasannin shine yarik’e shugaban wasanni na lokacinsu (Game Prefect) yakalli Khausar sune yan Javelin, Nasmat kuma ana bangaran Long jump. Yabar jikin bishiyar yana tafiyarshi cikin natsuwa har yaje Staff-Quater zai kar6i wasu littafai a wajan Mr Julius.

K’arfe uku tanayi yasake komawa filin wasannin da Nasmat yafara cin karo yace”Ke idan ba zaku tafi gida bane ni kunga tafiyata.Dan ALLAH kajiramu barin kirasu tayi cikin filin da dan gudunta.

A mota suka sameshi ya musu wannann rikitaccen kallan nashi Sudaida tabud’e baki za tayi magana yanu nata da yatsa”kul naji bakinki.Tad’an harareshi ta zauna tana turo baki gaba.Yaja tsaki”kunje kun shagala da wasanni ko sallar azahar ma baku yiba ga la’asar ta kusa,kufa kuna da ka’ida da bambanci tsakanin ku da wad’anda dama basu san kome ba sai duniyar, wallahi idan lokacin sallah yayi banga mutum a masallaci ba gobe…yayi kwafa, Nasmat tace”shi fa wannan Game Master muguntar shi har tafi ta Discipline Master.Ke tafi can shi ai ba makaho bane yana ganin k’atan masallaci ai a makarantar,na kuma tabbata da kun fad’a mishi sallah za kuyi bazai hana kuba,ai kowa ya san duk inda musulmi yake ba a rabashi da sallah,sai dai in sallarce bata dame shiba…Yaya d’ansarai… Yatari numfashin ta”ke ba nace kar inji bakin kiba?Tasunkwui da kai”wannan mutumin wallahi yanada matsala,tafad’a a zuci,tad’anja tsaki. Nasmat takalleta”ke Sudaida tun d’azu kiketa k’unk’uni abin harda jan tsaki ke da wa? Shiru ma amsace.

A k’ofar gidansu yatsaida motar bai k’arasa dasu gidansu kamar yadda yasaba ba,yakashe motar yafito yashige gida.Sudaida itama tabud’e bangarenta tafito tana masifa”aikin banza sammakon gaida makiyi,aiko ba a motarka zamu dawo gida.

Aminu yana hangota yafara dariya”ke fa Sudaida naga alama raguwa za a yi.Ta turo baki gaba “Yaya Aminu me nayi to? Kinga fuskarki kuwa?Gaskiya yunwar makaranta ba ta dad’i har na tuna lokacin da mukayi makaranta a Bauchi.Yad’an kalleta kinsan yau me su Mama sukayi a gidan? Tagirgiza kai “Tuwon shinkafa miyar shuwaka”Sai kawai tad’ora hannayenta aka”Wayyo ALLAH! Ni gaskiya yau ana ta 6ata min rai.Suwaye suketa 6ata miki rai?Takaryar da kai gefen dama ta marairaice “Yaya d’ansarai da su Mama,wallahi gidan Hajiya zan tafi ina canja kaya,dan bazan mutu da yunwaba.Yamik’a mata wasu nannad’ad’d’un carbon paper,Top-bond,babban pensir HB dawasu k’ananan tarkacen zane-zanenshi(Artistry Euipment) to tafi min dasu gida,yanzu haka Bakin Gogi zan tafi wani aikin signboard zanyi.Tasa hannu biyu takar6a “Yaya Aminu ALLAH yatsare.Amin Sudaida suka daga hannayensu suna ma juna adabo,sukayi murmushi sannan kowa yajuya yacigaba da tafiyarshi.

…Dare da rana suna aiki tuk’uru a kanmu,to muma kamata yayi mu zage dantse muyi aiki tuk’uru a cikinsu.Ubangijinmu kabamu rabo me amfani fid-dunya wal aakhirah.

21 Rabi’a Thani 1441
18 December 2019

We Ibrahim’ Daughters ????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na shida.

Da yammacin juma’a jikokin Hajiya sun cika gidan,tun daga zaure za ka fara jiyo hayaniyarsu sun tasata a gaba da shak’iyanci. Sudaida da Nasmat suma suka shigo,suna k’are mata kallo tasha had’ad’d’an leshin auduga ja da k’ananan fararan duwatsu,wuya,hannayenta, da d’an kunnanta na zinare sai d’aukar idanu sukeyi. Suka kalli juna suka k’yalk’yale da dariya”Hajiya manya wannan irin cakarewar k’uda a gefen gyambo?Inji Nasmat. Sudaida tagyad’a kai “Gaskiya kin had’u saura had’uwarki da ALLAH, wannnan k’ure adaka haka?To dawalakin goro a miya,bazawarin tane zai iso da yammacin nan. Gaba d’ayansu suka kuma k’yalk’yalewa da dariya, abinda yahanasu jin abinda Hajiyar take fad’a.

Aminu yashigo sai suka sa ihu da tafi “Yehhh… Gashinan, gashinan shine bazawarin data k’urema adaka.Yakama ha6a???? wai wai wai, ai kowa ya san Hajiya ba dani take yiba,dan ta san ni bazan juri al’alarta na bani bani kamar mak’ogwaro kullum a bashi ba,bani da wannan hak’urin,kusa idanu anjima kad’an za ku ganshi. Khausar tace Alkasim ne.Aminu yace gajan hak’urine dake koma wanene za ku ganshi. Yamatsa wajan Hajiyar suna maganarsu.

Sudaida tafara shak’o k’amshin turarenshi da iska takad’o mata kafin tayi magana yashigo yana musu wannnan rikitaccen kallan na shi”ku wallahi kun cika hayagaga bud’ar kan karya,sai kusama mutum ciwon kai.Sudaida da dama takejin haushinshi tace”sai dai dama can mutum da ciwon kanshi yashigo,kace kawai a baka magani za kasha. Suka k’yalk’yale da dariya.

Nasmat tace”su autan Inna manya, kace kawai kazo tad’i wajan Hajiya kuma katarar mun tare inda za ka zauna.Sudaida tad’anja tsaki tana mishi kallan sama da k’asa yana cikin fararan kaya yayi shar dashi”Kuma wai haka zai zo hannu rabbana”Yatsareta da idanun shi”ke yarinyar nan wai meye damuwarki da ni ne? Yanunata da yatsa”za fa kisha na jaki,idan baki daina shiga harka ta ba.Ta turo baki gaba”Indai aka k’i jininka ko ruwa kafad’a sai a ce ka tada k’ura,ni kad’ai nayi magana?Ni kamayar marainiyar wayon ka ko?Tahaye gadan Hajiya tana k’unk’uni. Hajiya tace”kai Julaibib yi tafiyar ka anjima sai kadawo muyi hirar mu cikin dad’in rai,lokacin duk sun kama gabansu.Yayi murmushi yana kallan Sudaida data juya musu baya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button