
“Kasham…yakira sunan ta.Tad’ago tana mishi kallan k’auna me cike da shauk’i,wallahi kasancewar su a tare,sai ta jita garas…kamar ba ita bace a mawuyacin hali d’azu ba.
Haba Kasham kina mace me kima, amma ace kema kina k’arama sama hazo?(shan taba) abin nan ya bani mamaki fa,ga ki da ilmi kina kuma ganin abinda su masu yin tabar suke rubutawa ajikin kwalin”Mashaya taba suna iya mutuwa da k’uruciyarsu”haba Kasham meye amfanin shan taba sigari ne?Kina sane da “nicotine”gubar dake cikin taba ba karamin jazama hunhu matsala yakeyi ba.Dan ALLAH… Yahad’a tafukan hannayen shi ????alamar magiya kamar yadda take mishi “Ki daina shan taba sigari dan babu kome a cikinshi sai illah.
Wata irin k’auna da soyayyarshi ta dad’a mamaye zuciyarta”Oh God…ALLAH kamallaka min wannan bawa na ka.Tajijjiga kai “shikenan d’an Sarai nagode,na kuma maka alkawari ko muna tare ko bama tare, na sha taba na k’arshe a rayuwata,daga yau d’in nan na barta har abadan duniya.Yad’an saki fuska”yauwa Kasham.Ungwai bu gangan(Kasham nagode sosai) dakika kar6i nasiha ta.Tad’an zaro idanun ta”kaii dama kana jin yarenmu?Saita kyalkyale da dariya dai dai da dawowar Lidiya da roban ruwa swan.Sai kuma tayi saroro cikin mad’aukakin mamaki “wannan me shegen girman kan dama d’azu takira?Lallai hankali ke gani ba idanu gululuba.Shima mik’ewa yayi bai sake magana ba yajuya yayi tafiyarshi.
Tadinga binshi da idanunta har sai da yayi nisa ya6ace ma ganinta sannan tamik’e tsaye itama tana yar dariya,wallahi wani irin nishadi ta tsinci kanta a ciki, takad’a kai” ALLAH dai yakai damo ga harawa ko bai ciba yayi burgima.Dama duk tunanin rabuwa dashi ne yajaza mata 6acin ran daya sa ta dinga k’arama sama hazo na rashin hayyaci.
Lidiya taja dogon tsaki “mahaukaciya kawai, ya gama zaginki ke kuma kamar wata wawuya kina jin dad’i.Wani murmushin yasake su6uce mata”karki d’auki alhaki dan d’ansarai bai ta6a zagina ba,bare kuma yau da yamin nasiha,na kuma kar6eta da hannu biyu. Lidiya ta jefeta da ruwan swan d’in rubbish girl.Dasauri tacafe ruwan tana dariya”kanki akeji Lidiya…
Haka nafi so an cema makaho je ka ka gani.
23 Rabi’a Thani 1441
20 December 2019
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na bakwai.
Kasan mafarkin danayi daren jiya kuwa? Musaddiq yagirgiza kai.Wai Julaibib ne da Kasham suke kiwon shanu a wani k’aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi.Musaddiq yakyalkyale da dariya”d’ansarai fulani ka koma har matarka take taya ka kiwo saboda tsabar k’auna?Musaddiq da Maimun d’in da yayi mafarkin suka kalleshi yana zuba d’anyan na’a na’a, d’anyan citta da ya’yan algarib a ruwan shayin da yake dafa musu,zuman da suke shan shayi ya k’are,sai yazuba sikari d’an kad’an dan dukkansu basa san zak’i,yamaida murfin tukunyar yarufe,yayi kamar baiji abinda suke fad’a ba.
“Julaibib.
Maimun yakirashi.Yajuyo da saurinshi yana amsawa”na’am.Bakaji abinda nafad’a bane? Shiruma amsace.Yad’auki wasu kud’i a saman tebur yamik’a ma Musaddiq “Malam tashi ka kar6o mana biredi.
Cikin natsuwa yake tafiya dawowar shi kenan daga gidansu a’isha amma cikin rashin sa a yatarar wai sunyi tafiya,ya dai barma Nasir sallahu idan ta dawo yazo yafad’a mishi.Sudaida tana hangoshi tafara murmushi dan ta kwana biyu bata ganshiba,jiya da akace ya zo, taje ta gaisheshi bata jeba.
“Yaya d’ansarai sannu da zuwa…
Iskar data d’ibo tama bai kalla ba bare yasan ALLAH yayi ruwan tsiranta.Ita da Sinan d’in daya ke shirin yimishi sallama suka bishi da kallo har yashige cikin gidan.Sinan yakad’a kai”Julaibib sai a hankali.Suka gama hirar su sukayi sallama.
A d’akin-girki ta tarar da Mama.Mama tace yauwa d’auki abincin nan ki kaima d’ansarai.Haushinshi takeji ta turo baki gaba”Mama shi yace miki yana jin yunwa?Mama tabita da kallan mamaki,sannan tamata dak’uwa gidan ku”Sai yace yana jin yunwa za a bashi abinci a gidan nan?Ke wace irin yarinyace?Jiyama danace kiji ki gaisheshi ashe ko bakije ba,saida zai tafi yake tambayar ki sai Sagir ne yace kina d’akinku kin kulle k’ofa.Sa an kine d’ansarai? Tad’auki abincin tabar Mama na mata addu’ar shiriya.Dak’yar tayi sallama dan tasan idan ma bata yiba,sai ya korata ta yishi.Ko kallanta bai yiba har ta ajiye abincin tajuya.
Umma tashigo d’akin- shak’atawar dan lokacin da yashigo tana sallar.Yagaisheta cikin girmamawa.Tayi murmushi”d’an Sarai yaro ne me hankali, yasan ya kamata sosai”Karatu ya k’are sai jiran sakamako ko?To Ubangiji yabada abinda ake nema.Yad’an shafa kwantaccen bak’in gashin kanshi.”amin ya rabbi Umma”. Tamik’e to bakaci abincin ba?Yakalli kwanon abincin”ai ni ban san ni takawo ma ba,dan a jiyewa tayi tafita.Kai kawai tagyad’a tafita.
Tana cin na ta abincin Umma tasa meta batace kome ba hannunta kawai ta damk’o,rik’on data matane yasa tasan cewa lallai bana wasa bane”Umma me nayi?Bakiyi kome ba ko?Sai tafara tirjewa dan wallahi idan ta yadda Umma takaita d’akinta to na jaki zata sha ba kad’an ba dan Umma ba sauk’i,shi yasama ba ta wani wasa dasu akwaita da zafi,sam ba ta d’aukar rashin kunya shi yasa kowa yake shakkarta a gidan,yana yinsu ba d’aya bane da Mama,da wasu lokutan suke maida ita kamar wata kakarsu,sai tazo ta tsawatar musu suke daina wani abun.
Umma dan girman ALLAH kiyi hak’uri na tuba nabi ALLAH na biki,kiyi ha…saukan marin yasa sauran kalaman suka mak’ale. Idanunta suka ciko da k’wallan wuya, dan marin ya ratsata yadda yakamata.Tasa ihu Mama dan girman ALLANMU zo ki ceceni,wayyo ALLAH! Ke…!Umma tace tana kallanta cikin zaro idanu “rufemin baki ke mara kunya ko?Ai ina jinku da Mama a d’akin-girki..Umma dan darajar Annabi Muhammadu kiyi hak’uri…. Mama wai kina inane?!
Mama tak’araso wajan da saurinta”a ah to me tamiki kuma?Ni tama laifi dama jira nake Musaddiq yashigo in fad’a mishi.Sudaida kuka takeyi da gaskiyar ta ita dai aba Umma hak’uri dan idan ba itace da bakin ta,tace ta hak’ura ba to lallai sai tayi dukan nan ko kuma ta had’a ka da Adnan shima kwallan shege a wajan iya ba da na jaki.Mama takan cemishi “Sarki zalimu dan dai ba ya’yanka bane,baka san zafin suba shi yasa kake musu wannan dukan na rashin tausayi.Sai yayi dariya “ai ko su d’in ne haka zan musu indai sukace baza su bi abinda zan fad’a musu ba wallahi.Dak’yar takwace Sudaida a hannun Umma.Sudaida tace” nagode”to amma Mama kibata hak’uri.Tagyad’a kai”ai zata hak’ura ne.Umma tace”na rantse da girman ALLAH zan hak’ura ne kawai idan taje takaima d’ansarai ruwan sha,tamatsa da abincin gabanshi, takuma gaisheshi tabashi hak’urin dangwarar da abincin da akace takai mishi.Idan ba haka ba tayi d’as d’as d’as da yan yatsunta ta shige d’aki.
Duk yadda taso dakewa idan zata shiga d’akin abin yaci tura.Cikin kuka tayi sallama.Yad’ago yana kallanta ta ajiye ruwan ta d’auko abincin,wani haushinshi yacika mata zuciya saboda shi aka so a bata na jaki,da Mama ba tanan a yadda ran Umma ya6aci ba k’aramar wahala zata shaba,shi ba a ganin abinda yakema mutane na halin-ko-inkula sai ita?Dak’yar tace”Ina wuni…wani sabon kuka ya kufce mata wai har hak’uri sai tabashi? Yaya…kayi hak’uri… Tausayinta yaka mashi koma menene yasan Umma ce ta sata wannan ban hak’urin.Nayi hak’uri Sudaida ai dama baki min kome ba,to zuba min abincin kad’an, tadauki faranti tazuba ta mik’a mishi.Yayi bismillah yafara ci.