
Kafanchan ne garin dasu a’isha suka tafi. Babban gidane a Magiya Street me sassa guda bakwai sai dai a kulle suke da kwad’o saboda mutanan ciki ma’aikatane a garuruwa mabambanta,idan ana sha’ani ko sun samu hutun aikine za kaga gidan ya cika da jama’a. Sashin Kaka dana kusa da itane kawai koda yaushe a bud’e jama’a na kai kawo.
Gidan yayi shiru saboda sauran yaran gidan sun tafi makaranta sai kukan tsuntsaye da suke ta shawaginsu.”Hantsi ya dubi ludayi rana ta haska ko’ina. Hashim bacci yake so yayi amma wani nishad’d’d’an al’amari ya hanashi sak’at bare yabarshi yarintsa.
“Aishahhh…
Yafurta sunan a zuci sannan yabud’e idanunshi cikin agogon dake manne a bangon d’akin “goma da rabi na safiya.
Sai yamik’e, sashin Kaka yanufa Alhamdulillahi”yafad’a daya fara jiyo dariyar ta, hira sukeyi da Kaka.Yayi sallama sannan yad’aga labulan dak’in,caraf idanunsu yahad’u tace”Hum manya gatan wasa,akwana a hantse… Kaka ta 6alli goronta tajefa a baki sannan ta d’an harareshi”to kar dai kanka yayi girma dan tace haka. Yak’arasa shiga yazauna a d’aya kujerar suna fuskantar juna da a’isha.Shi dai a’isha tana burgeshi baya gajiya da kallanta da duk wani abu data keyi.Yamaida kallanshi ga Kaka saboda me kikace kar kaina yayi girma?Tace naga dai wannan kirarin kyawawa akema. Aisha tasa baki “yanzu Hashim yana da makusa nekaka?Aiko makaho yashafa wannan k’ayatacciyar fuskar zaice me kyauce. Yad’an motsa kafad’a”Ah to gane min hanya…wai yaushane tafiyar taki?Tawatsa hannaye”ganinan dai, amma ba wani dad’ewa zanyi ba, tare dasu Mama zamu tafi,kasan har yanzu bamuyi hutu ba, amma da zamana zanyi wallahi garin bai ishe niba.
Yagyara zama”Shikenan sai a miki babban gida kawai yadda zai dad’a burgeki,kidinga jin dad’in zama.Cikin rashin fahimta tayi yar dariya “Kaji Hashim fa babban gida sai kace wacce zata dawo da zamanta gaba d’aya? Yagyada kai”To menene a’isha dan kin dawo gaba d’aya? Ai kamar ba matsala bace garin da kike so ne,ga kuma mutanan da kike so.
Yakalli Kaka da take ta cin goronta “Ke dai kamar mayya haka kike da goro.Eh koma dai mecece ni ba daina ci zanyi ba ko kai kake siyomin?Ya yamutsa fuska”To da wacce hujjar nasara zaiyi hawan k’aho? Tamishi dak’uwa idan baka siyo ba ai ubanka zai siyo.Shi da Aisha suka d’aure fuska wai su an ta6a musu Iyaye. Hashim yace”a ah Kaka wasa kar yayi wasa a tsikari uwar miji fa.a’isha tagyad’a kai”gaskiya ne dan uba baifi uba ba “Kaka tafara tafa hannaye cikin sallallami.Sai suka kyalkyale da dariya.Ba shakka wuyanku ya isa yanka. Tad’auko carbi zata shaud’ama a’isha ALLAH yabata sa a tayi tsalle gefe”Tabbb yanzu dan ALLAH sai ki shaud’amin wannan k’irgin carbin na ki me siffar rodi?To dawo ki gani mana.Tagirgiza kai”a ah wallahi ai sai in kwanta jinya, suka gama mata shak’iyanci san ransu sannan suka fara hirar arzik’i.
Hashim yadad’a gyara zama sannan yakalli Kaka cikin natsuwa”Kaka gaskiyar magana nifa a’isha nake so ba wani 6oye-6oye dama karatune yahanani sak’at to yanzu kam sai dai godiyar Ubangiji an gama har kuma an samu abun yi basai maganar iyaliba? Kaka tad’aga hannayenta sama tanama ALLAH godiya”Ashe tuntuni dakake fad’in Aisha ce matarka na d’auka na k’uruciyane nan gaba idan aka maka zance za kayi tawaye?To masha-ALLAH,ALLAH yasanya alheri,naji dad’in wannan al’amari,dakan d’aka shik’an d’aka tankad’en bakin gado.
Hashim yayi yar dariya”Aiko dai ba wani tawaye da zanyi yakalli Aisha ta sunkwui da kai amma labarin zuciya a tambayi fuska murmushi takeyi.Kaka tamik’e zata shaud’a mata carbin”Munafuka ana zance auranta ta nemi waje ta zauna saboda rashin kunya irin na ya’yan yau.Tashige d’akin baccin Kaka da gudu dan wallahi bata manta dukan carbin Kaka ba akwai mugun zafi.
Hashim yayi murmushi Kakarmu ta kanmu ALLAH dai yabamu i taku.tsufa me amfani acikin hayyaci da tunani.To Amin Hashimu,amma ba abinda yake kawo tsufa me kyau me amfani sai aikin k’warai lokacin k’uruciya”tsohon banza daga yaran banza yafara”kurik’e karatun”Alqur’ani da sauran kyawawan dabi’u da halaye, kuyi gaskiya da adalci a kome,idan kuka d’ore a haka Insha-ALLAH babu ta6ewa a rayuwarku.
Iimi shine jigon rayuwa,shine abinda yake gyara d’an Adam,yagayara tunaninshi dan haka ku kara zage dantse da kwazo wajan nemanshi,Ilmi ko wani irine to yanada amfaninshi. ALLAH yama rayuwarku albarka. Amin Kaka.
Hashim da a’sha sai rawar kai sukeyi kamar k’adangaran gobara,daga ranar yakoma cin abincin darenshi a d’akin Kaka abinda da ba yayi sai can nisan dare sannan yake tafiya na shi d’akin wani lokacinma Kaka ce take korarshi yatafi yabasu waje za su kwanta. Kafin su a’isha subar garin Kafanchan sai da aka tsaida magana tana gama makarantar secondary za ayi bikinsu ba wata matsala da aka samu kasancewar su Ya’ya mazane kuma duk Kakace ta haifi Iyayan nasu. Shi kuma nan da nan yafara aikin ginin gidanshi a Zaria Street.
Kasham tana shafa ma faratanta jan farce (nail polish)ruwan k’asa,Baranzan yashigo cikin kakin soja. Suka kalli juna na wucewar wasu dak’ik’u.”Beauty ina kikaje tun d’azu nake ta jiranki?Kamar ba da ita yake magana ba,zuwan can kuma bayan ta shak’i iska ta baki ta hanci sannan tace kasuwa naje siyo wannnan tanuna mishi nail polish d’in.Yazauna”anjima zani Jos amma kwanaki uku zanyi,to na baki time kafin indawo ki shirya kayanki zamu wuce barrack.
Barrack kuma?Ta tambayeshi cikin mamaki”Eh barrack kin gama makaranta to zaman me za kiyi?Mutafi kafin lokacin auran mu yayi nafa gaji da zama ni kad’ai kingane ko?Bai jira amsawarta yajuya yayi tafiyarshi.Tabi bayanshi da harara lallai za ayita dan wallahi tayi rantsuwa ba wanda zata sake bi har takwana dashi indai ba d’ansarai ba,bata ga kuma wanda ya isa sata canja wannan ra’ayi na taba har abadan duniya.Ita ya ma sosa mata inda yake mata k’aik’ayine,cikin gari za taje wajan Julaibib ta kwana biyu bata ganshi azahiran ceba amma kullum dashi take kwana dashi take tashi a cikin zuciyarta.
Tacanja kayan jikinta da dogon buje na velvet bak’i sai rigar shirt checker me d’amewa ta yafa siririn bak’in mayafi a gyararren gashinta data mishi ponytail style,jaka da takalmanta masu tudu bak’ak’e,tasa wasu manyan d’ankunne masu kama da awarwaro suma bakak’e sai siririyar sark’ar rosery a wuyanta.
Kai tsaye tashiga shagon.Abdul yana zaune yana aikin gida da aka had’osu dashi daga makaranta a darasin tattali (Economics) tak’arema shagon kallo ya dad’a cika ba kamar kwanakin baya ba, za taso taga irin canjawar da d’ansarai yayi.Tadawo da kallanta ga Abdul “Kai d’an samari ina Julaibib d’in? Fuska a had’e ya amsa “Baya nan.Haushi take bashi ita ba wani abu za ta siyaba amma sai tazo tana damun mutane yad’anyi k’unk’uninshi.
Taja kujera tazauna tana mishi kallan nazari,wani murmushi ya su6uce mata “wai shima k’arami dashi ya iya had’e girar sama data k’asa,tana so ta mishi wasu tambayoyi game da Julaibib amma ta san ko tayi a banza talaka ya girmi sarki bazai bata amsaba”Kai k’aninshine? Uhh yace batare daya bud’e bakiba. “Ina Sudaida?Ya yamutsa fuska shifa baya san adameshi, dak’yar kamar me ciwon baki yace “Ta tafi makarantar allo.Bata sake tambayar shi kome ba ta dai gane wannan halin nasu na rashin san magana a jinin sune.Itama sai ta bud’e Ovation d’in hannunta tana dubawa amma rabin tunaninta na ga Julaibib da inda yatafi.