GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kurum Ishshi Bazinzira(Akwai kud’i sosai, na rantse miki da ALLAH)

Yanuna mata aljihunshi yaushe kike so muje Kasham Hotel muci ubansu?Da kud’i da maciji maganinsu kisa”sai yamik’a mata abinda ya nannad’e a warraping sheet.kallanshi tayi kamar bata gane abinda yake nufi.Yagyada kai “yes take it’s yours…ta d’auke kai daga kallan da yake mata,ta san Champagne ne,to ita da ne zai bata Champagne taji ya burgeta ya mata gwaninta, cikin jin fushi tace” baa na so.Kamar ya bakya so? Mutumin na ki nefa?Tagalla mishi harara”so bloody what?To hell with it.Ba na sha,bazan k’ara sha ba,dan haka karka k’ara kawo min.Beauty… Tad’auki agogonta na fata tana d’aurawa kana da lokacin 6atawa amma ba da Kasham ba,tayi tafiyarta.Yayi murmushi yakai d’aki ya ajiye mata, ya san za ta sha yanzu dai ranta a 6ace ne, ko me yasame ta haka oho yad’an motsa kafad’a shima yajuya.

A waje suka had’u da Lidiya yake fad’a mata abubuwan da Beauty take mishi sunyi yawa fa,she bai gane me yashiga k’wak’walwar taba.Takad’a kai cikin takaici “Ranar wanka ba a 6oye cibi…dan haka ta k’yank’yasa mishi abinda ke faruwa. Yajijjiga kai “lallai biri yayi kama da mutum”To yanzu kina nufin cikin gari ta tafi wajan shi?Ko shakka babu,abin takaicin kuma nama na jan kare sai shishshigi da k’wala kai a faranti amma ba kwarjini.

Oh damme.Yadunk’ule hannu ya naushi iska ran maza ya 6aci, allurar soja ta motsa.Ya kalli Lidiya za muyi magana anjima? Tagyad’a kai “shikenan.

Yashiga mota ya zauna yana sauraran wakar”Who let the dogs out..ya kunna taba yana zuk’a, amma zuciyarshi k’ara tafarfasa take yi idan ya tuna duk abinda Beauty take mishi wai saboda wani filthy stupid bahaushe d’an cikin gari ne.Yadinga tuna beautiful life d’in da sukayi,suna matukar son juna,kuma Beauty kome na ta daban ne,musamman shi da take son shi tana bashi kome da yake so cikin dad’in rai,bayan alakoro har gyara take k’ara mishi.Wata soyayyarta ta dad’a tsumashi sai kawai yaja motar dama cikin gari za shi yabiya kud’in k’ofafin da yace a mishi na dank’areren gidan da yake gina ma Beauty ita da kids d’in da za ta haifa mishi.

Yana tsaye a Mak’era suna magana da me aikin k’ofofin kawai ya hango ta goye a bayan wani me mashin sunata dariya. Ranshi in yayi dubi ya 6aci zuciyar shi ta raya mishi wannan ne tsinannan bahaushen da take bi cikin gari,sun gama abinda za suyi yanzu kuma zai maida ita gida.Lallai yau za a yi ta sai yashige mota yabi bayansu sai dai kash… Kafin yak’arasa har me mashin d’in ya sauketa ya k’ara gaba dan Samaru zai wuce shi yasa Baranzan bai ganshi ba.

A tsakar gida yasame ta, ta d’ora k’afa d’aya akan d’aya tana cin k’osan rogo tana wata yatsina kamar dole a ka mata sai ta ci.

Beauty daga ina kike?Yayi tambayar cikin d’aga murya da tashin hankali.Itafa Baranzan ko k’aunar ganinshi ba tayi dan haka tajuyo cikin jin haushin tambayar da wanda yayi ta”daga Inda ka aikeni mana. Yanuna ta da yatsa”ke! Kar ki min rashin kunya fa, manufuka kawai,ba daga wajan tsinannan bahaushen nan kike ba?Tayi lallausan murmushin tura haushi “Thank God tunda ma ka sani,wani abu ne? Tamishi tambayar cikin wani malalacin kallo sannan tacigaba da cin k’osan rogon ta hankali kwance tana wakar “Hail Mary mother of Jesus.

Bazato taji saukan mari hagu da dama yafara zaginta ta uwa ta uba ya kaima k’osan kutifo ya tarwatse a tsakar gidan, hannayenta dafe da kuncinta idanunta sun kad’a jawur suna fitar da hawayen azaba. Hakan bai mishi ba kawai yasa hannu ya zaro belt d’in daya d’aure k’ugunshi yadinga labtarta har sai da ya tsistsinke ya jefar yana huci”ke dan abu kazan uban ki har kin isa kiyi soyayya da wani bayan munyi alk’awarin aure dake?Ina raye da raina da lafiya ta?Bazinzira (na rantse da ALLAH)idan kika kuma zuwa wajanshi abinda zan miki sai yafi wannan stupid,rubbish girl.Yagaji dan kanshi yayi shiru yajuya zai bar gidan.Dak’yar tamik’e dan ma zuciyarta ta bushene amma yadda tasha na jakin nan ai ko d’aga yatsa baza ta iyaba,tasha gabanshi”har ka gama kenan?Tagyada kai tare da had’e tafukan hannayenta.

“Ungwai bu gan gang (Nagode sosai)

Amma ka sani daga yau,yanzu d’in nan na gama soyayya da kai “I jilt”har abadan duniya.Wani kuka ya kufce mata amma bakinta bai mutuba, cikin kukan tanuna mishi d’akin ta shiga ka kwashe kayan sawanka da duk wani abu daka san na kane kabar mana gida.

Jikinshi yayi sanyi”wai an jefi kaza da gishiri”bai ta6a tunanin haka ba”haba Beauty yayi d’an murmushi “It sound phony,to ma me yayi zafi ne da har idanu za suci wuta haka? Me yayi zafi? Ta tambayeshi cikin tashin Hankali. To meye ma bai tafasa har ya k’one ba bare wani zafi? Bana son ka Baranzan, kuma ko ban auri d’an Sarai ba kai dai na gama soyayyah dakai,tad’aga murya cikin kuka haka ake soyayyah?Haka ake nuna soyayyah? Kai baka iya kome ba sai duka? Julaibib ya nuna baya so na kai har yagaji yafad’a min inyi hak’uri shi dai bazai aure ni ba, yana nuna ina damunshi,duk abinda nake mishi baya so d’in amma dai-dai da rana d’aya bai ta6a d’aga hannun shi yace zai mareni ba sai kai,tanuna shi da yatsa sai kai me ik’irarin kana so na, kana so muyi aure in haifa maka Ya’ya,a haka ne zamu zauna zaman auran for better for worst till death due part us?

Dukan da kamin ko Mamana da take da zafi bata ta6a min irin shiba tunda takawo ni doron duniya, tacire rigar ta,ta jefar tana nuna mishi wani k’aton tabo a kafad’arta”wannan ma tabon dukan kane wanda yariga ya zauna kenan har abadan duniya,kalli yadda ka farfasa min jiki?Tasake fashewa da kuka me cin rai,na rantse da ALLAH ta dankwali k’asa a d’an yatsanta ta la sa,na barka har abada kamar yadda na bar nonon uwata.Kai Baka da hankali baka san yadda zaka sace zuciyar mace ba, abinda ka iya shine ka kama mace ka yita duka kamar ka kama 6arawon da yayi fashi da makami da kakin soja a jikinshi da bindiga a hannunshi,wallahi ba ka iya kome ba,kaje ka koyo,sai kuma takoma sambatu Julaibib ya iya tafiya ta natsuwa,baya san hayaniya shi shigar shi kullum ta fararan kayane,ai kaima kasan ba me jure sa fararan kaya sai me tsabta na gaban kwatance”he is a gentle melanin beauty that I have never meet before.

Yarik’o ta kiyi hak’uri Beauty raina ne ya6aci zuciyata tana ta tafarfasa abinda yakaini ga zagi da dukanki kenan, na ka sa danne temper na amma ai kinsan ina sanki, zai rugumeta tayi wani ihu ta k’wace da k’arfin bala’i”tamishi kallan uku ahu”ALLAH sarki ai ban san haka zuciyar ta ka tayi ba,da dai naga tiriri yana fitowa ta kirjin kane to da na yadda, taja dogon tsaki “kai koma menene da menene wallahi ba wajan kuka na bane mutuwar uwar kishiya,ai kome yazo k’arshe.The game is over. Sunan wata wak’a.

Yajuya yayi tafiyarshi ai yasan tashi da Beauty bata 6aci sau nawa suna fad’a kuma su dawo su d’inke kamar wani abu bai faruba.Ran tane kawai ya6aci amma da zarar ta huce za su daidaita..

Bai koma gidan ba sai kwanciyar bacci sunje Kasham Hotel Kafanchan sunyi holewarsu da yan mata,yayi tatil da uwar laifi(giya) tamik’e da sauri dan saura kad’an yafad’o a jikinta,Itama ta kasa bacci ne dan gaba d’aya jikinta ya mata tsami dan ma an mata allura tasha magunguna,dak’yar ta canja kayan baccin ta da wando jeans da bakar rigar sanyi me hula tazuba k’ananan abubuwan da zata buk’ata a jaka tabar d’akin tana surutai”ai kin banza talaka ya girmi sarki idan ma kayi aman ka kai zakata gyara d’akin gobe da safe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button