
Yana tashi yaja doguwar hamma baki a bud’e yana mik’a tare da addu’ar”Our father who is in heaven,I love you thy name…bai k’arasa ba ganin ba Kasham kwance a gefe kamar yadda suka saba,yafito tsakar gida suka gaisawa da Babanta sannan ya tambaye shi ” Ina Beauty ne? Baban yace wai ba ta d’akin? Eh bata cikin.To bata kwana a gida ba ko kuma yanzu tafita.Kai yaushe kashigo?Baranzan yasa ke yin hamma”ba a gidan ta kwana ba ke nan, dan a d’akin nakwana yanzu natashi daga bacci,Baba barinje gida in dawo.To Baranzan a dawo lafiya(Oh???? mu Ya’yan Ibrahim ALLAH d’aya gari bamban.Abin da mamaki wai talaka da mata hud’u harda k’wark’wara amma me gari gwauro)
Sai yamma lik’is rana ta tafi tana shirin fad’uwa sannan Kasham ta koma gida,tafara masifa ganin bai d’auki ko tsinken sakacen shiba, a fusace tafara watso duk wani abu na shi tsakar gida ai na fad’a maka”I jilt.. Is over,Is totally over…na rantse da ALLAH zan mishi rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dani ba. Babanta yafito daga d’aki yana kallanta da kayan da take watsowa tsakar gida da mad’aukakin mammaki “Kasham me ya ta6a k’wak’walwarki haka?Ya za ki dinga watso mishi kaya tsakar gida?Cikin hayagaga…tad’aga mishi hannu”hey! Ba ruwanka ai tun jiya nace ya kwashe kome na shi.Yarik’o hannayenta “Baranzan da za ki aura kayan shine fa kike watsowa? Tak’wace”Baba ka kyaleni a cikin hayyacina nake ban sha giya ba bare kace tafad’a min ba gaskiya ba,soyayyarce kawai bazanyi ba,na fasa auren nashi,kuma na yi alk’awari ko na rasa mijin aure to da in auri Baranzan gwamma in mutu ba aure.Baza ki auri Baranzan ba to saboda me?Wa zaki aura? Saboda bana son shi,kuma d’ansarai zan aura.Yakalleta da sauri yana maimaita sunan d’ansarai? Dansarai? Waye kuma haka?
D’ansarai shine wanda nake so kuma a cikin gari yake,shi zan aura zan kuma yi abinda yake yi,shi musulmi ne,nima wallahi sai na musulunta na yi sallah. Yatafa hannaye cikin kad’a kai”Jesus Christ.Yabita da kallan nazari sai huci takeyi kamar ta ci babu.Yanunata da yatsa”to ban yadda ba.Tagyad’a kai”ni ai na fad’a maka ne dan ka sani,ba wai dan ka yadda ba,tunda dai ai ni zanyi zaman auren ba wani ne zai min b…saukan marin da aka mata yasa sauran kalaman suka mak’ale…
Kasham ai ban san baki da hankali ba sai yau, a duk zuri’ar mu ba me salla sai ke ce za kice za kiyi? Tayi d’as d’as d’as da yan yatsunta”to baki isaba,ina tagirgiza kai wannan ba za ta sa6uba bindiga a cikin ruwa, dama abinda ki ka dinga yi kenan a makaranta bin mazan hausawa?Tama Maman na ta wani kallo me kama da harara”ni ina ruwa na da rashin sallar zuri’arku?Kuma aike ma kin san mazan hausawa ba k’ashin yarwa,sau dubu nawa ina kawo miki kayayyaki kinaci,kin kuma sani sarai su d’inne suke bani,baki ta6a k’in kar6a ko ki min fad’a akan in rabu dasu ba, sai yanzu dan nace ina san zama irinsu?Ashe kowa yana san wawa haihuwar shice ba a so? Tsamaninki banza kika dinga ci? Takai mata wani mari amma tagoce dasauri yabi iska, tamata dak’uwa kinci uwaki,dan abu kazan ubanki ba za kiyi sallah ba,abinda ba mayi dake sa’in’sa amma gashi daga fara cewa kina san wani tsinannen bahaushe har kina min rashin kunya kina fad’amin maganar dakika ga dama…Tabuga cinye na rantse da ALLAH baki isaba sai dai idan bana numfashi za kiyi sallah.Kasham tagyad’a kai”To maji ma gani ai…an binne tsohuwa da rai.
Lidiya tashigo suka had’u suna ta zagin ta amma ko a jikinta wai anyak’ushi bishiya.Tad’an motsa kafad’a tare da ta6e baki “Kanku ake ji…ta d’auki jakarta”bazan iya wannan bud’ar kan karyan ba, kuci kanku kusha bak’in ruwa.
“Kasham ani yake?(Kasham ina za ki?)
Tajuyo muryar Maman a tsawace.Tayi taku biyu sannan taja ta tsaya”Ani yake?Tasake tambayar ta,ko a jikinta tace.
“Ana kari Julaibib(wajan Julaibib zani)
Dawo ki zauna karki kuskura ki bar gidannan.Tad’anja tsaki sannan tak’arasa ficewa da saurin ta”idan na dawo kar ki barni inshigo”kuma ko ku mutu ko ku rayu wallahi sai na yi sallah kuma ALLAH zai taimakeni in auri d’an Sarai…ALLAH dai yakai damo ga harawa…
Tajuya kan mijinta cikin tafasar zuciya ni dai ka sani gaba d’aya zuri’armu babu wanda yake sallah,sai dai in wancan ne yake yaudare min yarinya,yake so tabi layin shi,to kaji na rantse da girman ALLAH bazan yadda ba, zanje har cikin gidanshi inci mutuncin shi, ba ki yamana ga shi nan yana shirin kama Kasham, dama ya dad’e yana fad’in idan munki sallah to Insha-ALLAH Ya’yanmu sai sunyi.Yagirgiza kai cikin damuwa yasan matarshi bata da mutunci, to shima dai dan uwan na shi Yayanshi uwa d’aya uba d’aya Shedrak,wanda a yanzu yake amsa sunan Alhaji Hafiz ba barin ta kwana yake yiba shima mafad’aci ne wallahi.
Kiyi hak’uri Dinatu mu zauna musan abinyi,nima ba na goyon bayan abinda tazo dashi,kuma da kike fad’in Shedrak ne yake yaudare ta to yaushe rabonshi da zuwa garin Zonkwa bare har yashigo k’auyan Madauci?Tayi shiru.Yawatsa hannaye kingani ko?Ai shekarun da yawa ko Kasham baki haiifa ba a lokacin. Muje wajan Pastor ayi addu’a ko Baptismal idan yaka ma sai a sake mata.Tamik’e cikin gyad’a kai”eh to ka kawo shawara to tasu mutafi ai bamuga ta zama ba da zafi-zafi akan daki k’arfe.
Kasham bata kwana a gidan ba,sai washe gari da hantsi.Lokacin kuma Mamanta ta dad’e da tafiya kasuwa,dama ita take fita ta nemo musu abinda za suci dama sauran buk’atunn rayuwa,yar kasuwa ce sosai da take cin kasuwancin ta gari da k’auyuka na nesa dana kusa,shi kuma mijin kullum yana gida yana aikacen-aikacen yau da kullum da akeyi a gida har girki ma a wasu lokutan idan ba kowa shi yake yi.Yad’ago yana kallanta “Kasham zo mana ganin tana shirin shigewa d’akin ta,tayi kamar ba ta ganshi ba kuma har had’a idanu sukayi lokacin da za ta shigo.
Tazauna a d’aya farar kujerar robar,ko sannu bai samu arzk’in tace mishi ba bare in kwana (Oh mu Ya’yan Ibrahim????inda ranka ka sha kallo…sunan wani shiri a Freedom Radio)A ina ki ka kwana Kasham?Tazuba mishi manyan idanunta masu maik’o”wannan wace irin tambaya ce haka Baba? Yagirgiza kai “ai na ga ke a gida kikafi kwana shi yasa na tambayeki kuma Baranzan yazo nemanki na san ba a wajan shi kika kwana ba.Baba ba ruwanka da inda na kwana. Tad’ora k’afa d’aya akan d’aya tana karkad’a kafar dama,tana wata yatsina da hura hanci alamar bala’i takeji da gasken-gaske.Ta sauke gwauran numfashi Ka na ji ko Baba? Eh ina jinki.ALLAH sai na auri Julaibib,ka san yadda nake jin k’aunar shi a zuciya ta kuwa?Takad’a kai”no matter how zan kwatan ta maka ba za ka gane me nake jiba…sai tafashe da kuka duniyar ta cukurkud’e mata wallahi,rana zafi inuwa k’una,to a ina ake so tasamu sassauci ne?Julaibib,Iyayanta,Baranzan, Lidiya, da yan uwan ta kowa yana jin haushinta? To ita tace ma zuciyar ta ta k’aunaci d’ansarai ne???
Tausayi irin na d’a da mahaifi ya mamaye zucyarshi,saboda shi yana da san Ya’ya sai dai abinda tazo dashi me girma ne, amma ga dukkan alamu tana san wannan d’an…menene ma sunan na shi oho ya manta, tunda har ta yadda tabar Baranzan da suka shafe shekaru hud’u suna soyayyar su hankali kwance ba abinda ya ta6a shiga tsakanin su na tashin hankali amma akan shi wannan bahaushen sun fara fad’a,dama duk cikin Ya’yansu ai daga Kasham sai Rahab ne basa canja samari kamar yadda ake canjin kayan sawa,kuma su biyun ne suka maida hankali ka’in da na’in akan karatu, sauran maza da matan suna can suna cin karansu ba babbaka. Matanma sai su shafe watan ni takwas basu lek’o gida ba, suna can wasu garuruwa da jahohi suna zaman kansu suna kuma sheke ayarsu yadda yaka ma ta,galibi ma zuwan su gida sai da dalili me k’arfi kamar lokacin Christmast,New-Year, da Esther,su kanzo a Valentine amma ba kowane Valentine ba.