
Kiyi hak’uri Kasham dak’yar ya rarrashe ta tayi shiru,manyan idanunta masu maik’o sun kad’a jawur “Kiyi hak’uri Kasham ni kin san matsala ta ba babba bace,zan iya barin ki kiyi sallah tunda kina sanshi, za kuma cigaba da kasancewa ‘ya ta,bazan tauye miki yanciba” you have human right”kuma shekarunki sun kai na duk wani d’an Adam me hankali,babbar matsalar “inda gizo ke sak’ar Dinatu baza ta ta6a amince miki ba,idan kinki ji to na san za ta yafe ki a cikin Ya’yanta, za ta barma hausawa ke forever kinga kuma baki mata a dalci ba, ta so ki ta kula dake ta miki kome na rayuwa…kema ba za kiji dad’i ba.Yakalleta yad’an motsa kafad’a ya cigaba da gyaran waken da yake yi na girkin rana.Itama tamik’e tana k’unk’uni.Yad’anyi murmushi k’uruci dangin hauka,Kasham baki san rayuwa ba.You know nothing but wannan soyayyar data rufe miki idanu.” So makaho…
Lidiya tabita da kallo “to wai ke da kike ta wannan hank’oran,kike k’ok’arin 6atawa da kowa akan wannan tsinannan kun dai-dai tane ya yadda zai aureki zai zama miki uwa da uba dasauran danginki da za ki rasa? Dan abu kazan ubanki ina ruwanki?Babbar manufuka kawai,bitch ai na san ke ki ka k’yank’yasa ma Baranzan!
Lidiya ta k’yalk’yale da dariya dan abun bai ba ta haushi ba,ta kuma k’yalk’yakewa da dariya tana tafa hannaye Jesus Christ of Nazareth gaskiya kin fara cin kai (Hauka)
Kasham ta fad’a gado ta rufe idanunta zuciyar ta tana wata irin bugawa,da bata d’auki alk’warin dai na shan taba ba to da yau ALLAH ne kad’ai yasan ko kwali nawa za ta sha,ba ma kara ba,ta dunk’ule hannu ta dinga naushin matashi idanunta na tsiyayar da hawaye masu d’umi ” So babbar cuta…
Lidiya ta dafa kafad’arta sai tamik’e da sauri kamar wacce kuna ta harba”get the hell out this house…ta fad’a a haukace.Lidiya tamik’e sai dai in bar miki d’aki amma ba gida ba,dan kema ba na ki bane. Wawuya kawai da har yanzu ta kasa gane san maso wani take yi… Sai kinyi 6atan 6akatatan za ki gane ashe shayi ma ruwa ne madara da bournvita ne ya canja mishi kala.
Mamanta tana dawowa daga kasuwa ko hutawa batayi suka tasata a gaba sai gidan Pastor.Dama yasan da zuwansu dan haka suka zauna zaman jiran fitowarshi Yashigo d’akin-shak’atawar cikin bak’in suit, rigar ciki shirt, takalmanshi da mashak’in wuya (neck-tie)ruwan k’asa,wuyarshi da sark’a rosery.
Yana rik’e da King James Bible.Da fara’arshi yake musu sannu da zuwa shi ma yazauna suka gaisa sannan ya nuna Kasham da kanta ke hayaki ta d’ora kafa d’aya akan d’aya”ke kina so ki bamu matsala me yahad’a ki da bahaushe ne?Tagalla mishi harara tana mishi wani kallan uku ahu “ah kaji k’arfin hali 6arawo da sallama,yanzu kurace za ta cema kare maye? Shi har yana da bakin da zai ma wani fad’a yaushe-yaushe aka gama rigima d’an shi na cikinshi yama wata yarinya yar Kurmin-Bi ciki,yanzu haka yarinyar tana cikin gidanshi sunyi auran leda (auren da ba Pastor ne ya d’aura shi a majami’a ba Church)wai sai ta haihu za a yi auran gaskiya dasa albarkan Iyaye.Yasake kallanta ba magana nake miki ba?To me ko zai had’ani dashi banda soyayyay.Ina son Julaibib zan kuma aureshi ko kamin addu’a bazai kama niba,ai wallahi gwamma ni ba ciki a kamin ba.Maman za ta mareta yahana kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake yi, ki barni da ita kawai Dinatu.
Pastor wannan abun yana cimin tuwo a k’warya,Ya’yanmu da zarar sun girma sun yi soyayyya da hausawa sai kaji suma suna san zama masu sallah, sai su gudu su aure su ko muna so ko bama so,to a kan me za su dinga yaudare mana Ya’ya suna mana d’auki dai-dai suna converting d’insu zuwa musulunci?Sannan su Ya’yan hausawa mata basa ta6a yadda suyi soyayya dana mu Ya’ya mazan,abun yana k’ok’rin shige makad’i da rawa fa,na rantse maka da girnan ALLAH Ya’yanmu mata da suke sallah a cikin gari sunyi yawan da ko mun fara k’irgasu lissafin zai k’wace mana,to gaskiyar magana sai kun k’arae zage dantse da k’wazo wajan preaching ta yadda za Ku dak’ile wannan al’amari suma suji suna k’yamar mazan hausawa kai ba su kad’ai ba da duk wani me sallah kawai(????Up up up Diniyal-Islam????).
Yagyad’a kai”Ki kwantar da hankalin ki Dinatu wannan matsalar ita muke tattaunawa a taranmu na Christian Association Of Nigeria(CAN) har yanzu muna kan aikine,ai kowa yaci tuwo damu miya yasha, wannan makon ma a kawai babban taro a Jos har daga kasar waje za muyi bak’i.Wani murmushin mugunta ya su6uce mishi”wallahi za muma duk wasu masu sallah na Southern Kaduna(Kudancin Kaduna)wankin babban bargo a k’aramin k’oko’.Suka gyad’a kai cikin gamsuwa “yauwa Pastor ALLAH yataimake ku. Amin,amin.
Pastor ya dad’e yana jero addu’o’in shi su kuma Iyayan sun durk’usa gwiwa bibbiyu sun rufe idanusu tare da had’e tafukan hannayansu idan yayi addui’ar sai yace In Jesus name we pray sukuma suna amsawa da Amen,amen,amen,ameeennn….
Ita dai kallansu kawai takeyi har zuciyarta ta lula tunanin Enigma man d’inta d’ansarai.Tayi murmushi “Julaibib idan ka aureni za kaji dad’in rayuwar ka,zan saka farin ciki na karanci”Catering & Hotels Management.Na san Food and Nutrition zan dinga shirya maka abinci me rai da motsi, ingantaccen abinci me gina jiki da k’ara kuzari,za kaci har sai ka ture..bata san Pastor ya gama 6aragadar shiba har sai da Babanta ya ta6ata”Kasham tashigo mu tafi gida an gama ganin idanunta a rufe sun zaci ko itama amsawa ta dingayi.
“Gobe ma ku dawo”.
Tajuya tama Pastor d’in wani malalacin kallo sannan tajuya,wallahi ba inda zan dawo idan za a ma mutum addu’a lallai dole-dole sai yana wajan? ALLAN ai yana jin kome…
Abinda yafi kome mahimmanci a rayuwar d’an Adam ya fi kome sauk’i,sai Ubangijinmu bai horema kowa mallakan shiba dan kar a k’unta ta ma bayinshi, sannan bai horeshi kaasatan (ake6e) ga bayinshi na gari ba, a ah yabarshi kowa yasamu,Ubangijinmu me rahama da tausayin bayine…
Iskar da muke shaka ta ALLAH ce ba wani me iko da ita.
Ruwa da kusan shine rayuwa duk rintsi duk wuya akwai shi.
Rana kullum sai ta fito itama ta ALLAH ce babu wani me iko da ita.dasauransu…
ALLAH mungode maka da kayi mu musulmai masu bin tafarkin Manzanka,ba dan mun fi wasu girma da daukaka ba a ah ganin da markace kawai.
Ya Ubangijinmu!Kaine me jujjuya zukatan bayinka…ka tabbatar da zukatanmu a kan addinin da ko a wajanka ka kirashi da musulunci.
27 Rabi’a Thani 1441
24 December 2019
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na tara.
A gida Nasir yasamu Julaibib yana fad’a mishi jiya da daddare su Aisha suka dawo.Yauwa Nasir nagode maka ba kad’an ba, yad’ibo dabino me yawa yabashi.Yasa hannu biyu yakar6a cikin murna.Nima nagode Kawu.
Bayan sallar la’asar suna tsaye a k’ofar gidan tafito sanye da farin hijab tana murmushi.Tagaishe su a ladabce.Musaddiq yace to ya gajiyar hanya? Sai kawai kiyi tafiya ba sallama?Tad’anyi murmushi Yaya Musaddiq a min afuwa bazan sake ba.Yagyad’a kai to shikenan. Yayi gyaran murya karmu 6ata lokacin mu tunda lokaci jarin d’an Adam ne,Aisha magana ta gaskiya za muyi.Yad’an kalleta tana tsugune natsuwarta na ga sauraran abinda zai fad’a. Julaibib yana sanki, za ki iya auranshi? Shiru ya ratsa wajan, ta had’a kai da gwiwa dak’ik’u nata tafiya bata ce kome ba.Aisha yi magana mana. Yakalli Julaibib to wata kila ni take jin kunya barin ba ku waje”dama shirun budurwa yaddan ta… Bawazara kuma sai ta tanka.