
Tad’ago da sauri kwallah sun cika idanunta”a ah ka tsaya kawai hawaye masu d’umi suka zubo mata sharrr…Lafiya kike kuka kuma? Tagirgiza kai inafa lafiya Yaya Musaddiq na shiga rud’ani,zuciya ta tana min zafi, tunani na yana shirin rikicewa.Saboda me? Musaddiq ya tambaya cikin mamakin kalaman ta.Saboda soyayyar mutane biyu”wa zan za6a?Takad’a kai cikin takaici”Kaiyah…Yaya Julaibib bakamin adalci ba,kaci amanar k’auna.Yakalli Julaibib sannan yakalleta”banga ne ba kamar yaya Aisha?Ta share hawayan da suke gudu a fuskar ta sannan tamik’e tsaye”Na so Julaibib amma dole tasa na hak’ura saboda banga fuska ba,kwatsam kuma sai ga ku da tayin soyayya a lokacin da yariga yak’ure. Musaddiq yad’an kalleta kin daina san na shine? Ko d’aya har yanzu ina san shi to amma ya zanyi?Akwai alk’awarin wani a kaina.
Yaya julaibib ka ci amanar k’auna, kwarai na so ka,kai ka k’i bani goyon baya. Aisha ki taimake mu.Takalli Musaddiq da mammaki kamar yaya?Eh ni a ganina lokaci bai k’ureba tunda ba auran aka d’aura ba, gashi kin tabbatar da bakin ki kina san shi,amince mana kawai kome zaizo gidan sauk’i,su Baba zasu shiga cikin lamarin.Julaibib yana sanki,za kuyi zama cikin amana…ta tareshi da sauri”haba Yaya Musaddiq wannan san kai da yawa yake, me yasa kake aran bakinshi wajan cin albasa? Kai ni nama game ba wani so na da yake yi.A ah Aisha karki fad’i haka dan Julaibib ya zo wajanki ba sau d’aya ba ba sau biyu ba to a tunaninki zuwan me yake yi? Sada zumunci,ziyarace ta sada zumunci,kullum haka yake fad’a kuma haka na da’uki zuwan na shi.To Aisha….
Julaibib ya katse shi”kar muyaudari kanmu Musaddiq,neman aure akan neman aure haramun ne a musulunci,ni na yadda da hukuncin Ubangiji duk abinda ba ka samu ba to dama can rubutacce ne tun daga lauhul-mahfus ba na ka bane.Yad’an kalleta Aisha ina miki fatan alheri da dacewa a gidan aurenki.Yarik’o hannnun Musaddiq yamata sallama sukayi tafiyarsu.Tabisu da kallo har suka 6ace ma ganinta.wata sabuwar soyayyar shi ta dad’a mamayar zucyarta.Hashim ma yafad’o mata, shima tana kaunarshi da wata irin soyayya ta daban. Tagyad’a kai”lalalai wannan muk’addari ne”rabon kwad’o baya hawa sama… Tad’an cije le6enta na k’asa sannnan ta juya zuwa gida..
Da daddare bayan sun gama cin abincin dare ya fad’a ma Iyayanshi kome game da Aisha.Sukace ba kome sai a nemi wata.Ya amsa cikin ladabi Insha-ALLAH.
Danbarwa me yawan gaske akayi tsakanin Kasham da Baranzan kafin ya yadda ya tattara kome na shi yabar gidansu tare da alk’awarin tunda tak’ishi saboda wani tsinanne to ko ba jima ko ba dad’e shine nan yanuna kanshi da yatsanshi shine zai zama ajalin Julaibib. Yanunata da yatsa”ni nake fad’a miki wannan maganar ki rubuta ki ajiye.Idan ka kashe shi ba tare da ya maka kome ba shari’a ai ba kyaleka za tayiba,kaima zakabi bayanshi ne.
Tabi k’ofar da ake ta kwankwan sawa da wani malalacin tsaki tadad’a d’ora kanta ajikin matashin “Yes come in”suka shigo sama da k’asa take musu wani kallan uku ahu.Sisters ne su biyu “menene?Cikin d’oki me rik’e da madaidaicin kofin silver tabud’e murfin sannan ta mik’a mata”Shekaran jiya Reverend Father yadawo daga Jerussalam(Darussalam)to jiya Pastor yaje mishi ban gajiya shine yabashi Holy Water(Ruwan Zamzam)me yawa anba kowa ya sha,ke kuma bakije majami’a ba shine aka d’iban miki ta ajiye kofin a gaban ta.Tamik’e zaune da sauri daga kwanciyar da tayi,tasa k’afa ta ture kofin.Kafin suyi wani yunk’uri ruwan yabi carpert d’in d’akin.Suka bita da kallo cikin mad’aukakin mamaki”Kasham Holy Water ne fa?Tawatsa hannaye cikin halin-ko-in kula”dan Holy Water ne sai me?Suka 6ata fuska gaskiya baki kyauta ba.Tagyad’a kai “to sai a yanke min hukunci.Suka juya har sun kai k’ofa d’aya ta juyo”mun manta Pastor yace mu fad’a miki anjima ki shirya za ku tafi a miki baptismal.
Taja dogon tsaki”Allah suturi bukwui inji kishirya k’onanniya” Ku fad’a mishi bana so dan haka ba inda zani wallahi.Takalleta na wasu dak’ik’u Kasham da kinyi hak’uri an miki kinga ran…Cikin hayagaga da tafasar zuciya tamik’e tsaye”na ce bana so,to a kyaleni ko ana dole a rayuwane? Daku dashi kuje kuyi baptismal d’in ko ba daku suke fornication d’in ba?”Get lost dan abu kazan ubanku,get the hell out of my room tanuna musu k’ofa yan iska kawai kuje kuji dana ku zunubin”dan nace ina san d’an Sarai shi kenan sai yazama zunubin da har sai anyi baptismal (wankan tsarki)?Ko wani abune yazama zunubi? Za su sake magana tayi wani ihu ta buga tebur d’in tsakar d’akin sai da littafin kai suka zubo k’asa”now get out dan abu kazan uban ko wace shegiya!.Suka fita ka me da ha6a????lallai Kasham ta ci kai(hauka)dole ko a mata wankan tsarki ko za ta samu lafiya.
Tafad’o gado cikin takaici da damuwa da kuma matakin d’auka.Ba zato wani tunani yazo mata.Tamik’e da sauri har tana bugewa da katakon gefen gadan,tayi tsalle tana wani ihun jin dad’i”Halelujah…Diary d’inta ta d’auka tayi waje da gudu hurrayyy.
Babanta tasamu yana zaune a inuwar barankaci yana sauraran rediyo a cikin shirin tambayoyin addinin kirista.Tazauna a gefen shi cikin walwala,yabita da kallo ba Pastor yana kiranki bane?Tayi yar dariya “Ba kirana yake yiba ya dai cene a fad’amin gobe da yamma inshirya za a min baptismal d’in.Yagyad’a kai Ohooo. Yacigaba da sauraran rediyonshi ita kuma tana bud’e diary d’inta tana karantawa.Wacewar wasu dak’ik’u tad’ago tana kallanshi”ni ko Baba in tambayeka mana. Uhun tambaye ni ina jinki.Tad’anyi rubutu a diary sannan ta kalleshi “wai brother d’inka daka ta6a bamu labarin shi har ka nuna mana hotonshi tun da dad’ewa yana nan kuwa?Yad’aure fuska”me yadameki da Shedrak? Ina ruwanki da jin labarinshi kuma?Yayi d’ad d’as d’as da yan yatsunshi ki karkad’e kunnuwanki ki jini da kyau “Shedrak is no more in our family,mun dad’e da yafeshi mun barma musulmai shi,kamar yadda shima yazabi zama musulmai da addininsu. Ta ta6e baki
“Basakut Baba(Kayi hak’uri Baba)
Dan na ga kamar ranka ya 6aci,ni abinda yasa na tambayeka a cikin wani littafi d’azu dana ke karantawa naci karo da sunanshi shine na tuno da wannan d’an uwan na ka,ai kaima ka san tunda muke dakai ban ta6a maka zancen shiba.Yakashe rediyon dan sun gama shirin.To woo na d’auka kina san jin labarin shine.Tad’an motsa kafad’a ko d’aya Baba dan labarinshi ba zai amfane ni da kome ba.Tamik’e Baba barinje unguwa amma ba dad’ewa zan yiba.Yad’aga mata hannnu yana mata adabo.
“Sai aburak” ( Sai kin dawo).
Sakamokon jarabawar su na fitowa Water Fall Hotel matsirg suka d’auke ta aiki amma k’ememe tace ba ta so duk da albashinta me tsokane.Mamanta takalleta cikin takaici to saboda me ba kya so?Saboda Baranzan yana da hannun jari a hotel d’in ni kuma na gama amfanuwa da duk wani abu indai a kwai Baranzan a ciki wallahi bazan yiba.Suka had’u suka dinga zagin ta amma tayi kunnan uwar shegu dasu ko a jikinta an yak’ushi bishiya.
A sanda rana tatafi tana shirin fad’uwa Kasham tashigo gidan da kaya nik’i nik’i ta zauna tana hutawa.Rahab da Mamanta suka bita da kallo daga ina kike ne?Tabud’e manyan idanunta masu maik’o da suka d’an canja kala kamar me jin bacci”daga kasuwa nake tamik’a musu tsire da lemun kwali Don Simon tashige d’aki.