GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Rahab tabiyota wai kashe-kashen kud’in nan da kikeyi ko dai kin yi sabon saurayine? Tamata wani malalacin kallo kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru tad’auko diary d’inta tana rubutu.Tagama abinda takeyi takwanta da tunanin wanda zai zo yasiye aladunta gaba d’aya dan kud’i sosai take buk’ata,dama ita da Rahab kiwon aladu sukeyi da shi suke rufama kansu asiri shi yasama basa harkar tara samari barkatai,mazan ma ba sa, ba su na jaki kamar yadda suke ma yan matan bariki dan sun san ba da kud’insu suka dogara ba,a dating zata watse. Yauma aladu biyar takama tasiyar dan ba ta da kud’i.

Dasafe tasamu Babanta a d’aki yana kallo tazauna tana tayashi suna hira. Baba ka san abinda yake bani mamaki?Yagirgiza kai”to wai shi Shedrak da aka yafeshi a cikin dangi yana jin dad’i?Yatsaida idanunshi a kanta tsawon lokaci, nazarin ta yake yi”Kin dameni da maganar Shedrak a yan kwanakin nan me ki ke so kiyi ne? Me ki ke shirya wane? Banza bata kai uwar akuya kasuwa,Meye a zuciyar kine Kasham?Cikin dariya tace kai Baba ALLAH ba abinda nake shiryawa,ni abinda yake bani mamaki ace mutum ba shi da yan uwa blood relatives saboda zai yi sallah kuma shi ya yadda da haka? Ni fa shi yasa nafara canja tunani a kan Julaibib saboda zo mu zauna zo mu sa6ane,to idan munyi fad’a wajan wa zani inji dad’i ku kun yafeni? Yagyad’a kai “Ehem yanzu kika zo inda muke so kizo, yanzu kin gane abinda muke k’ok’arin nuna miki kenan amma ki ka k’i sauraran mu gashi daga fara addu’a kin fara dawowa hayyacinki.

Yayi yar dariya”God bless you my daughter. Wani murmushi ya su6uce mata amin Baba.Tagyara zama”gaskiya Baba ni yanzu na amince gobe muje a min baptismal.Yayi kyau Kasham,Yakad’a kai cikin damuwa “Hum Shedrak? Kar kiyi tunani irin na shi fa.Tagyad’a kai”haka fa.Ko yanzu yana ina ne oho mishi.Yace wa? Shedrak ai nasan inda yake da Dinatu ma tana zuwa gidanshi a shekarun baya…bai k’arasa ba tad’an ta6e baki tare da mik’ewa cikin halin-ko-in kula da maganar,Baba barinje inyi wanka dan yau zanje a min nail fixes.Tana shiga d’aki tayi tsalle tafad’o gado Hak’anta za ta tadda ruwa Halelujahhhhh…

Ranar lahadi duk suna ta shirin tafiya majami’a(Church)ita kuma tana zaune tana shafama faratanta da taje aka sa mata na roba jan farce.Mamanta ta kalleta ke baza ki shirya ba sai kin makara? Ta yamutsa fuska”ni fa yau ba inda zani”baki da lafiya ne?Rahab data fito daga d’aki take tambayarta.Lafiya ta k’alau zuwan ne kawai bazan yiba.Shikenan sai ki mana abincin rana.Tagyad’a kai To Mama.Tad’aga hannu tana musu adabo sai kun dawo.

Tamaida k’ofar gidan ta kulle sannan tashige d’akin Baban wajan daya ke ajiye muhimman takaddunshi tanufa,d’aya bayan d’aya take dubawa cikin tsanaki,wasu takardun ma tun na makarantar Primary suna nan saboda ya iya ajiya,anan taci karo da wani tsohon hoto Baban ne da Maman suna ganiyar k’uruciya, tamayar da hoton tana dariya,kakaf binciken ta bata ga abinda take nema ba.Rai a6ace taja dogon tsaki”Ohhh no damme,ta dunk’ule hannu ta naushi iska.Tayi jifa da wani tsohon wallet k’ananan katunan ciki suka tarwatse a tsakar d’akin.Tadafe kanta dake barazanar ciwo.

Wucewar wasu dak’ik’u tana zaune cikin tafasar zuciya,ta tsuke bakinta kamar za ta rufeshi amma bata rufe ba tana zuk’ar iska, ta zuk’eshi da yawa sannan tafara fesar da iskar ta baki ta hanci ta sauke gwauran numfashi tamik’e ranta in yayi dubu ya baci ta tura hannunta acikin gashin kanta,tasake dunkule hannu ta naushi iska”Damme…a kasalance tamayar da takaddun, sannan ta tsuguna tana kwashe tarwatsastsun k’ananan katunan a cikin ma’ajiyarsu,idanunta suka kai wajan guda d’aya daya kusa shigewa k’ark’ashin kujera,tad’auko shi tana dubawa.

Complementary card ne me d’auke da sunan Alhaji Hafiz Donatus,sunan unguwar da yakeyi,sai lambar waya na gida dana wajan aiki.Tayi tsalle cikin dariyar murna,ta k’ank’ame katin a kirji”Hallelujah…wallahi wani karfi da karsashi ne ya mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta.Batayi niyyar yin abincin ba amma farin cikin data tsinci kanta a ciki yasa ta zauna ta shirya musu abinci da abun sha me rai da motsi(Yummy).

A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar talata tagama shirya kayanta a yar madaidaiciyar jaka trolley,tana zuge zip d’in Mamanta tashigo tana mata kallan nazari

“Ani yake ?(Ina za ki)

Kamar da gaske tajuyo cikin damuwa suna kallan juna,tad’an sosa kunnen ta na dama”Ramai zani wajan Tina tun jiya da rana nasamu labarin an mata Operation,tun ajiyan naso tafiya to bani da kud’ine.Wayyo! Takad’a kai cikin damuwa ALLAH yabata lafiya, kigaishe ta,tasa hannu a mata sun gane(Lalita)taciro kud’i to kenan ko na mashin baki dashi? A ah ai na samu Mama ina da wanda zai kaini.To gashi kya kara wannan zai miki amfani, dan na san zaki tarar da ita da wata buk’atar,kin san majinyaci.Takar6a tana d’an murmushi “Nagode Mama. Maman tarakata har sai da ta hau mashin tana dad’a jadda dama me mashin d’in Ramai za ka kaita kayi tafiya da ita a hankali,dan jiya na hau mashin d’in wani wawan yaro saura kad’an yazubar damu.To Mama zan tafi a hankali kar in zubar miki da wannan kyakkyawar yarinyar ni da zaki bani ita wallahi ina so.Shi da Maman sukayi dariya ita kuma ta d’aure fuska”Kai malam ina da abinyi dallah ja mutafi. Mama sai na dawo.Yauwa Kasham ALLAH yakaiku lafiya.

Suna zuwa kwanar da zata sadasu da cikin gari tace shiga nan yad’an juyo ya kalleta ba Ramai a kace zan kai kiba? Eh can ne amma na fasa mushiga cikin gari idan nagama abinda nake yi ka kaini tasha.Yaja mashin”to amma kin san kud’inki ya k’aru da yawa tunda har sai na jiraki kin gama abinda za kiyi a cikin garin ko? Tagyad’a kai “Indai kud’i ne to ka kwantar da hankalinka kamar ka mari uwar soja,wallahi abinda ka yanke da bakin ka shi zan ba ka.Yayi yar dariya “godiya nake yi me kyau, wallahi irinku nake so.

Tanata mishi kwatance har suka zo gidansu Julaibib amma k’atan kwad’an da suka gani a k’ofar gidan yabata tabbacin mutan gidan ba sa nan tace su wuce shigon shi sai dai kash…nan d’in ma a kulle. Tasauko tana waige-waigenta ta hangota.

“Hey Sudaida Ibrahim Me-Lambu…

Sudaida tajuyo,idanusu yahad’u tak’araso wajan tana murmushi”Malama Kasham ke ce?Ina kwana. Takamo hannunta”Lafiya lau Sudaida,ya karatu? Alhamdulillah. Sukayi d’an shiru na wuce war wasu dak’ik’u.Kasham tasake kallanta”yanzu ajin ki nawa?Aji uku zamu shiga idan aka koma hutun nan.Tagyad’a kai”yayi kyau,kidage sosai kinji ko? Ina Ya’yanku na ga shagon a kulle? Sudaida tabi kofar shagon da kallo”Yaya d’ansarai ai baya gari,watanni biyar kenan har yanzu bai zo gida ba,Shida Yaya Musaddiq zuwan shi uku.Suna ina? Tad’an kalleta “Suna Zari’a k’aro karatu.Tad’anyi murmushi “Julaibib ya tafi Jami’a zai d’ora degree a Islamic Studies kenan,tun a Gidan-Waya taso canja course,da ace shima Special Education yake yi irin karatun Musaddiq wallahi da sai ta koma irin karatun,da yanzu itama ta nemi addmision ta bishi can.

“Hummm my enigma man wish you all the best”…

Takalli Sudaida to me zan bakine? Tazuge zip d’in jakarta taciro yar k’aramar “Damask rose-flower”ta rabo me kyan gaske tashak’i k’amshin sannan ta mik’a mata”gashi ba yawa.takar6a da godiya.Kasham ta sake ciro wani rufaffen envelop tamik’a mata”wannan ki ba Yayanki d’ansarai duk lokacin da ya dawo dan ALLAH ki adana shi dakyau,kar kuma kimanta, tahad’a tafukan hannayenta please… Sudaida tayi yar dariya ganin yadda tawani marairaice mata tagyad’a kai”Malama Kasham Insha-ALLAH I will do as you say”tadafa kafad’arta”Yauwa Sudaida thank you very much,I really appreciate sukayi dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button