
Tabud’e wallet d’in hannunta kud’ine sababbi yan naira d’ari tad’ibo su dayawa bata tsaya k’irgawaba tamik’a mata, amma Sudaida bata kar6a ba. Tamata kallan nazari”Me yasa?Ba kome kawai ki barshi.Ba zato Sudaida taji ta rungumeta “Kar kimin haka Sudaida,ni kaina ban san dalilin da yasa nake k’aunar duk wanda yake da alak’a da Julaibib ba,ban san dalilin ba, hakanan nake jinku a jinina,tanannad’e kud’in tasa mata a tafin hannu, ai ni naba ki ba rok’ona kika yiba,sai ta sake ta a hankali.
Kiyi karatu Sudaida,dan shine hasken rayuwa,shine abinda baya k’arewa kullum kina tare da abinki ba a fashin shi duk rintsi duk wuya yana cikin kwakwalwarki,Ina miki fatan alheri,ki gaishemin da d’an Sarai,Julaibib my enigma man dakyau da kyau.Me mashin d’in yatayar tahau,Sannan suka d’aga hannu suna ma juna adabo????sudaida tad’an d’aga murya dan har sun kusa shan kwana”Malama Kasham kema ina miki fatan alheri nagode.Kasham tamata murmushi”Toh nagode suka sha kwana. Suka 6ace ma Sudaida.
Cikin sa a suna zuwa tasha motar saura mutane biyu ta cika tabiya kud’in mutum biyun sannan ta sallami me mashin da kud’in da baiyi zatoba dan ta ninka mishi abinda yace tabayar,yatafi yana mata godiya.Tana shiga tazauna ta d’aura belt direba yaja motar sai…
KADUNA garin gwamnahhh…cibiyar ilmi,wayewa da iya d’aukar wankan dake bin jiki.Oh yessss…mune the KD’s mune nan,kowa kagani da wanka rainan mune,a wajan mu ya koya…????
Me neman ruwa yatafi randa.
Me neman jini yatafi kwata.
Me neman labarin wuta ya tambayi tsire.
Masu mura suke da majina.
Masu ruwa suke da kifi.
Masu abin fad’a ba sa fad’a.
3 Jumaada Awwal 1441
29 December 2019
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A. Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na goma.
Motarsu na tsayawa a kawo tad’auki shatar taxi,dak’ik’u kad’an suka iso unguwar saboda ba cunkoson abubuwan hawa, tabi wajan da kallo bayan tasallami me taxi,tasake kallon wajan da tunanin ina za tabi dan hanyoyin sun karkasu.
Yan makarantar Islamiyyar rana sun fara tafiya,wasu yara guda biyu maza za su wuce ta tsayar dasu “Sannunku yan makaranta. Suka amsa da yauwa sannu.Dan ALLAH tambaya nake yi gidan
“Alhaji Hafiz Donatus”
Tamik’ama babban katin hannunta, yad’an kalleta da mamaki bayan ya duba katin, sanin Alhaji Hafiz da yayi mutumin kirki me rik’o da addini,dan babban d’an Alhaji Hafiz abokin Kawun sune, to ita kuma wannnan me zak’o-zak’on faratan rumfar shaid’an fa?Kuma ko mayafi babu haka take tafiya kamar wata namiji,a gidan Alhaji Hafiz ma basa mu’amala da kome sai hijab,to kuma meye darin gamanka da ita? Tamabayarka tayi idan ka sani fad’a mata,idan baka sani ba fad’a mata.Zuciyarshi tafad’a mishi haka.sai yagyad’a kai.
Yamik’a mata katin,gidan wanda nasani nake kuma kyautata zatan shine to kinga wancan titin yanuna mata titin da d’an yatsan shi tagyad’a kai tana kallan titin, to kimik’e shi,kwana tafarko zaki shiga,gida na hudu nan ne gidan ai zama kigani idan kika duba katin. Tahad’a tafukan hannayanta”nagode.A ah ba kome yarik’o hannun k’aninshi suka tafi.
Tacigaba da tafiya har tazo gidan me k’atuwar k’ofa ruwan zinare,tayi tsai…na wucewar wasu dak’ik’u,ta kai hannu zata fara rank’washin k’ofar kenan sai gata a bud’e wata farar mota kirar marsandi tana fitowa, yabita da kallo ta cikin madubi,itama shi take kallo, yashiga tunanin a ina yasan wannnan fuskar ne? “Mahaifiyarshi”abinda yafad’omishi kenan daya ga manyan idanunta masu maik’o da yanayin k’irar jikinta,sai yayi ribas tabbas wannan yar’shice,yar d’an uwanshi Kantiok ga kamanni nan,yafito daga motar suna kallan juna,itama tagyad’a kai cikin gamsuwa tabbas wannan dan uwan Baban tane sai dai shi bak’i ne,Babanta kuma fari,yana sanye da dogayan fararan kaya,bak’ar hular dara akanshi da bak’in takalmi,yanata k’amshin turare me sanyin dad’i wajan shak’a.
Tayi yar dariyar murna”Uncle.Yayi murmushi”na’am.Rahab ce ko Kasham ko Judith? Uncle Kasham ce.Masha-ALLAH sannu da zuwa, yakulle motar yazare makullin”to bismillah yanuna mata hanya mushiga ciki,yakar6i trolley d’in har suka shiga wani babban d’akin-shak’atawa me cike da ni’ima,wani sassanyar iska da k’amshin turaran d’aki ya mamaye ko’ina,kome agyara tsab a muhallinshi,tazauna a kujera tare da lumshe idanun ta tana zuk’e k’amshin tana zancen zuci “Lallai Uncle yana jin dad’in shi,tasauke numfashi sannan ta bud’e idanunta, suka kalli juna sai ta d’anji kunya ta kauda kanta gefe.
Yayi murmushi kinsha hanya ai na san kin gaji,yad’auko abinci da ruwa da lemun kwali na biyar a raye (five alive) yamik’a mata kofi,tazuba ruwa tafara sha sannan taci abincin ya kuma mata dad’i taci to k’oshi dan bata wani tsaya bak’unta ba,kad’an tasha lemun ta godema Jesus Christ,Yesu almasihu me ce to.
Saida da tagama suka fara hirar yaushe gamo?Shi dama bai san taba dan tun kafin a haife ta rabonshi da kauyansu Madauci.Ikon ALLAH banyi zaton wani a cikin ku zai zo inda nake ba,wai Kantiok ne da kanshi yafad’a miki inda nake?Tagirgiza kai”a ah ba shi bane,ni nayi ta bincike har naga complementary card d’inka, ni ba ma wanda yasan wajan ka na zo dan na fad’a ma Mama wajan k’awata Tina za ni.
Yayi yar dariya”Dinatu kenan,wato me hali baya fasa halinshi,amma ba abinda yafaru ko?Eh Uncle ba abinda yafaru kowa lafiya.suka cigaba da hirar yan uwa ya tambayeta wannan,ya tambayeta wancan, wata amsar ta bashi dariya, wata kuma tabashi tausayi, wata tambayar kuma tace bata gane ko suwa yake nufi ba,dan tun kan a haife ta fa,har suka gangaro kan yan uwanta.
Alhamdu Ya’yanshi nawa yanzu? Tad’an ta6e baki ita kanta tana dad’ewa bata ganshi ba”ai duk cikinsu Bitrus ne kawai yayi auran majami’a,amma Alhamdu ai gaba d’aya ya koma D one(d’orawa one)yana tsiran naman kare,baka ga yadda ya lalace ba saboda shaye-shayen miyagun k’wayoyi,amma watannin baya budurwar shi ta haihu ta kawo mana yarinyar data haifa mun gani.Yakad’a kai cikin damuwa,wannan irin rayuwa dame tayi kama?
Yakalleta ke kuma na ki y’ayan guda nawane?Bazaice kaso nawa bisa d’ari ba dan ba shi da k’ididdiga amma dai ya san samun cikakkun ‘yan mata(Virgin)a cikinsu,ba masu yawa bane saboda wata irin rayuwar san zuciya,taci barkatai da suka za6a suke yinta cikin kwanciyar hankali.Tagirgiza kai”Uncle ban ta6a haihuwa ba,kuma duk abinda muka yi da Baranzan”I repent”Ya yadda da ita,yajijjiga kai”toh ya karatu kin gama secondary ko anan zaki k’arasa?Ta ajiye kofin lemun a saman tebur sannan ta bud’e jakar hannunta taciro wani babban envelop ruwan k’asa ta mik’a mishi.
Yad’ago cikin mamaki da murmushin jin dad’in ganin sakamokon jarabawar ta na College of Education.Kinyi k’ok’ari kuma na yadda lallai baki tsaya shashanci ba”wai rok’o a gidan bebe”suka cigaba da tattauna al’amura mabambanta har Kasham tafad’a mishi gaba d’aya abinda yakawota.
Yakalleta lallai kin yadda za ki musulunta Kasham?”Eh Uncle na yadda zan musulunta.Yagyad’a kai”To ki sani musulunci yana da sharud’d’a guda biyar duk wanda kika ganshi a cikin musulunci to tabbaci hak’ik’a sai da ya yadda da wad’annan sharud’d’an, Sharad’in farko kuma mafi girma a cikin su shine kalmar shahada.