GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, bisa cancanta sai ALLAH,kuma Annabi Muhammad bawan shine kuma manzan shine.

Ma’anar kalmar {لاإله} tana kore duk wani abin bauta ne koma bayan ALLAH{إلاالله}wannan kuma tana tabbatar da bauta ne ga ALLAH shi kad’ai ba tare da abokin tarayya ba.

Sharud’d’an kalmar shahada kuma sune:
1.Ilimi wanda yake kawar da jahilci.
2.Yak’ini wanda yake kawar da kokwanto.
3.Ikhlasi wanda yake kawar da shirka.
4.Gaskiya wacce take kawar da k’arya.
5.Soyayya wacce take kawar da k’iyayya.
6.Janyuwa wajan yin aiki wacce ke kawar da k’in yin aiki.
7.Yadda wacce ke kawar da juyarwa.
8.Kafircewa da kin yadda da duk wani abin bauta koma bayan ALLAH.

Tare da sanin cikakken bayani danga ne da”Shahdatu anna Muhammadan rasulullah.

Ma’anar kuwa:Gasgata Manzon ALLAH a duk abinda yaba da labari,da yin biyayya ga abinda yayi umarni dashi,da nisantar abin da yaja kunne ko yayi hani dashi,da kuma bautawa ALLAH dai-dai da koyarwarshi.

Bayan wannan sai sauran sharud’d’an musulunci sune Sallah,Azumin watan Ramadan, Zakka ga wanda yake da dukiyar data kai nisabin yin Zakkar,Aikin Hajji ga wanda yasamu iko. Kingane ko?Naga ne Uncle, kuma na yadda da duk abinda kafad’a to yanzun nan za ki kar6i musulunci.

Ashhadu anla’ila ha’illallahu wahdahu laashari kalah…Wa ashhadu anna muhammadan abduhu wara suluhu.Yana fad’a tana fad’a har suka zo k’arshe. Yayi murmushi Alhamdulillahi yanzu kin zama musulma, ALLAH yamiki albarka. Acikin sunayan musulunci da kike ji wanne kike so a dinga kiranki dashi?Tad’anyi jimmm…na wucewar wasu dak’ik’u sannan tace”Uncle Sumayya nake so…Yayi murmushi ALLAHU-AKBAR kin za6i suna me daraja a tarihin addinin musulunci,Sumayya mace ta farko data kar6i addinin musulunci.

Tunda kin zama musulma to akwai wankan shiga musulunci dan haka nake so ki natsu kiga yadda zan kwatanta miki.Yadinga mata bayani dalla-dalla sannan yace ta mishi bayanin yagani inda tayi kuskure ya gyara mata.

“Dafarko tsarki zan fara sau uku,sai in wanke hannayena zuwa mad’aurin agogo sau uku,kurkure baki,shak’a ruwa a hanci da fyacewa sau uku,wanke fuska daga matsirar gashin kai zuwa k’arshen ha6a,daga gefen kunnan dama zuwa gefen kunnan hagu sau uku,wanke hannun dama zuwa gwiwar hannu sai uku,wanke hannun hagu zuwa gwiwar hannu sau uku,shafan kai daga matsirar gashin kai zuwa keya,a kuma dawo dashi da duka tafukan hannaye sau d’aya, sai shafan kunnuwa ciki da waje sau d’aya,wanke k’afar dama saman k’afa da tafin k’afar ko ina ya jike da ruwa zuwa k’wauri ko idan sawu sai an tabbatar ta wanku,ta hagu ma haka za a mata, wannan itace cikakkiyar alwala.

Sannan sai in zuba ruwa a kaina da duka tafukan hannayena in cuccud’a in tabbatar gashin kaina ya jik’e da ruwa,zanyi hakan har sau uku,sai in wanke barin jikina na dama har zuwa tafin k’afar dama,sai in wanke 6arin hagu har zuwa tafin k’afa,sai ingame jikina da ruwan in tabbatar ko ina ya jik’e da ruwa,lungu da sak’on jikina.

Idan kuma na so bayan nayi tsarki sai kawai ingame jikina tun daga kai har zuwa tafin k’afafuna da ruwa in cuccud’a ko ina nanma wanka yayi.Tad’an kalleshi amma Uncle wannan wanka zaifi dad’i a shower(shaya)ko?Yayi murmushi wannan sharhin kine amma ko ba shaya mutum idan yaso zaiyi abinshi.Kin burgeni yadda kika kowa kome dalla-dalla kamar yadda na fad’a miki,da alama zaki fahimci kome a d’an k’ank’anin lokaci.

Wannan wankan shi za kiyi duk lokacin da jinin al’adarki tad’auke,shi za kiyi idan janaba tasa meki, shi za kiyi idan jinin biki yadauke,bambancin dake tsakaninsu kawai wajan niyya ne.

Cikin d’an shakku takalleshi “to Uncle kana ganin Julaibib zai aure ni?Sumayya sanin gaibu sai ALLAH, tunda yafad’a miki ko zakiyi sallah shifa bazai iya auran kiba,amma babban abinda za ki fara yanzu shine addu’a”Allah ai maji rok’on bawane,ba kuma abinda ya gagara a wajan ubangiji”.

Yanzu kinga za kiyi wankan tsarki amma dole fa sai kin cire wannan faratan roban(nail fixes)dan a addinin musulunci sa shi haramun ne,tad’auki abin yanke farce tafara k’ok’arin ciresu,data gama yakaita wani d’aki, kishiga kiyi wanka,d’akin yar uwan kice,kome yana zaune a muhallinshi Dammm…Zuciyar ta tabuga saboda irin wannan k’amshin a d’akinsu Julaibib ta ta6a jinshi wallahi ranar data mamayeshi tashiga.Ta tsuke baki kamar zata rufeshi tana zuk’e sassanyar k’amshin tabaki ta hanci tare da lumshe idanunta,tana wata kissima a zuci,wani murmushi ya su6uce mata wucewar dak’ik’u masu yawa, tasauke gwauran numfashi sannan tarage kayan jikinta tashiga wanka.

Yakoma d’akin-shakatawa yazauna, tunanin ya cika k’wak’walwarshi har baiji fitowar taba.Uncle na gama tafad’a lokacin da take k’ok’arin zama,ya kalli agogon dake d:aure a hannunshi lokacin sallar la’asar ya gabato.Yamik’e “zani masallaci,daga nan zan wuce in d’auko mutan gidan,ko kin jini shiru karki damu dan wata kila zamu had’u da cunkuson abubuwan hawa.Ta amsa da”to Uncle a dawo lafiya.Tad’auki wani littafi data gani a saman kujera”Islamic Perspectives On Reproduction, Health childbirth Spacing In Nigeria.Tafara karantawa.

Miqdad ne yafara dawowa a sanda rana ta tafi za ta fad’i magriba na shirin kunno kai,ya san ba kowa a gidan shi yasama yatafi da mukulli amma yana ta6a kofar yajita a bud’e,yasa kai cikin murmushi tare da sallama bak’uwar fuskar yagani a kwance tana karanta littafin da ya ajiye a saman kujera jiya da daddare, tamik’e zaune daga kwanciyar da tayi,tajuya inda taji sallamar Dammmm…Zuciyarshi ta buga da suka had’a idanu,Hafsa yake gani a fuskar ta,hatta manyan idanunta masu maik’o irin na Hafsa ne.

Tad’anyi murmushi”Sannu da zuwa. Yagyad’a kai”yauwa.Tanuna mishi kujera”kazauna mana, mutan gidan ba sa nann ne Uncle ya tafi d’auko su.Yasake kallanta jin tace Uncle wannan yar uwarsu ce ta Zonkwa yayi yar dariya sannnan ya zauna”kema sannunki da zuwa,daga Madauci ko?Tagyad’a kai.

Fara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatai na nesa dana kusa yasa shi mik’ewa barinje masallaci? Bai jira amsar taba yajuya yafita.

Bayan sallar Isha’i suka shigo gaba d’ayansu dama Alhaji Hafiz ya fad’a musu kome tun a hanya.Hafsa ta rungumeta tana dariya “Yaya Sumayya ina tayaki murna da shiga addinin gaskiya.itama tasa hannayenta ta rungumeta tana murmushin jin dad’i suka saki juna suna kallan kallo.

Alhaji Hafiz ya kalleta”Sumayya wad’annan sune iyalina.Yanuna ta wannan Maman Hasan kenan kasancewar haihuwarta uku duk yan biyu take haifa kuma maza amma ba sa dad’ewa suke komawa ga Ubangijinmu,akan wannan yanuna Miqdad haihuwar tafara tsayawa daga shi sai Hafsa, Zuhair da Khadija.Takalli Miqdad”Ashe babban Bros d’inmu ne shine baka fad’a min ba?

Tamatsa wajan Maman Hasan tana gaishe ta”gaskiya Mama nima ina san yan biyu,kimin addu’a ALLAH yaba ni.Sukayi dariya dan bata wani nuna bak’unta ba kamar ta ta6a zama dasu.Maman Hasan ta jijjaga kai “ALLAH buwayi gagara koyo,duk wanda yakalli Sumayya ya kalli Hafsa yasan Yaya da kanwa ne,lallai jini abune me k’arfin gaske ko Khadija batayi kama da Hafsa ba kamar yadda Hafsa tayi kama da Sumayya.

Hafsa ta d’auko abinci amma ba wanda yaci dan a k’oshe suke sai Miqdad kawai yaci,yana gama ci Maman Hasan takalleshi d’auki abincin nan ka kaima almajirai tun kafin ya lalace.Yad’an 6ata fuska dan baiso fitaba”Maman Hasan yanzu a ina za a ga almijiri?Dare fa yayi.Tad’an harareshi”kai malami ba kasan gidan almajiran kasan layin nan bane? Yad’an shafa kai”na sani. To can za ka kai musu suma suci da d’uminshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button