GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuhair ya mik’e”Yaya Miqdad barin d’auka muje in rakaka.Yauwa Zuhair nagode.Suka fita Zuhair yana bashi labarin abinda yafaru d’azu a gidan Malam Muhammad Aminu (Kakansu).

Sunyi hira sosai suna dad’a wayar mata da kai,ita kuma duk abinda bata gane ba kai tsaye zata tambaya karfe goma Alhaji Hafiz yakallesu to ya kamata kowa yaje yakwanta haka, Sumayya sai ALLAH ya kaimu gobe zamu fara karatu.Hafsa tamik’e”Baba Insha-ALLAH yanzu kafin muyi bacci zamu fara.Yagyad’a kai cikin gamsuwa”yauwa Hafsa ALLAH yamiki albarka.Su kayima juna saida safe.

Hafsa matashiyar budurwa me ji da ilimin addini dana zamani,ajinta biyar Secondary a fanni kimiyya (Science)Suka shige d’akin baccinsu suna jin k’aunar junansu a zuciya.Taje tayi alwala tafito sannan takalleta “Yaya Sumayya kema kije kiyi alwala ganin tana shirin kwanciya.Alwala kuma Hafsa?Ba d’azu nayi alwala nayi sallar…tayi shiru sallar me ma?Ta tambayi Hafsa.Sallar Isha’i.Hafsa tabata amsa tana murmushi.Tagyad’a kai Yauwa shi.Hafsa ta zauna a gefen gadon “wannan alwalar idan za a kwanta bacci a keyin ta dan ita kariyace daga shaid’anu,shifa zama da alwala yana ba mutum kariya sosai a rayuwa amma ba kowa yake iya jure yiba,shi yasa Baba da Yaya Miqdad suke burgeni saboda sun rike wannan,wallahi basa zama ba alwala,nima dai wasu lukutan nakan kwatanta.

Mako d’aya,biyu,uku shiru makatau balaguro a lahira,ba Kasham ba labarinta.Rahab taja dogon tsaki saboda gajiya dajin mitan da Maman take yi a kan rashin dawowar Kasham. Tadago takalleta”To wai menene abin damuwa dan har yanzu bata dawo ba? Kasham fa ba k’aramar yarinya bace.Yakike irin wannan maganar Rahab?Kasham ba ‘ya ta bace, ya bazan damu ba.Yar kice amma kin san lafiya ita kesa aji mutum shiru, tad’anyi murmushi amma Mama kema sometimes bakya ganewa…ta tari numfashin ta kamar ya bana ganewa? Rahab tamik’e zaune daga kwanciyar da tayi ta d’an ta6e baki”ni wallahi na san ba yadda za ayi Kasham tayi wad’annan makonnin a Ramai,ni nafi kyautata zatan tana cikin gari wajan saurayin nan data nace tana so.Tadaki kirjinta da karfi”Jesus christ…ta jijjaga kai lallai biri yayi kama da mutum ni banyi wannan tunanin ba,yanzu barin shirya intafi Ramai d’in ga kai ga k’afa ai ba tambayar me aka yanka.

Matina tana zaune a shagon kitson attachment d’inta ta hagonta Tamik’e dasauri ta tarota “oyoyo Mama sannu da zuwa”tabata wajen zama sannan ta kar6o mata ruwa da lemon mirinda da manyan cincin guda biyar a faranti. Tazauna suka gaisa.Mama kwana biyu ni da Kasham ba wanda yakawo ma wani ziyara,ni dama wannan Sunday d’in zanzo. Tafara girgiza kai tana tafa hannaye”Jesus Christ”Kina nufin Kasham bata wajanki makonni uku da suka wuce?Tace an miki Operation za tazo gaisheki? Matina ta kama ha6a”kaji muguwa zata jazamin masifa to ni Mama lafiya ta kalau ba abinda akamin.Takad’a kai”wato gaskiya ne abinda Rahab tafad’a Kasham tana cikin gari wajan wannan tsinannan bahaushen?Anya Mama Kasham tana wajan Julabib?Kin san yace bazai aureta ba…Ke tafi can idan takai mishi kanta yana ganin ta fad’i gasassa zai yi wani yunk’urin korarta ne?Matina tagirgiza kai”Kin san ALLAH Kasham bata wajan d’an Sarai dan bata ta6a 6oye min kome game dashi ba, kinga ko a makaranta bai tsaya kulata ba dan bata gabanshi,lokacin nema yake zaune zaman yanci da aikata abinda yake so dan ba idanun wani babba na shi,bare kuma yanzu dayake cikin iyaye da yan uwa?

Tina nifa ban yadda ba idan kin san gidansu kawai ta shi mutafi ki rakani,tasan gidan har shagonshi sun ta6a zuwa da Kasham, to amma ta san halin Mama bata da kirki,yanzu zataje ta tada hayaniya bayan ta san wallahi Kasham bata wajanshi,to sai dai itama ta fara tunani ina Kasham za ta tafi tayi wannan dad’ewar?Bata saba haka ba dole kuwa Mama ta damu, amma dayake Judith da halin tane haka ai bata ma maganar ta sai ranar da aka ganta kawai.

Shiru na nucewar wasu dak’ik’u zuwa can Tina ta numfasa”Mama na fi tunanin Kasham tana Kaduna?Cikin rashin fahimta tace Kaduna kuma?To wajan wa?Ko tayi sabon saurayine a can?Kasham bata da wani saurayi acan,sai dai kwanaki tafad’a min matuk’ar za ku takura mata,ku hanata auran Julaibub to lallai zata koma wajan Uncle d’inta dayake sallah.Tadafe kirjinta dan taji kamar ruguzowar wani abu a zuciyarta,ranta in yayi dubu ya 6aci.Takalli Tina “nagode,gobe dole zan tafi Kaduna na rantse da ALLAH ban haifi yarinyar da zatayi sallah ina numfashi a doron k’asa da raina da lafiya ta ba, Kasham taci k’arya ta kwana da yunwa ta tashi a rame.To maji magani an binne tsohuwa da rai.

Cikin rashin sa a ta isa Kaduna,sai dai almajirai ta tarar agidan bayan sun gaisa da malamin take tambayarshi Alhaji Hafiz yad’an kama baki “Wai wai wai ai Alhaji Hafiz yafi shekara goma sha biyar da barin gidan nan,danshi yabani yace halak malak acigaba da koyarwa, kuma yanzu hakama basa k’asarnan shida Iyalinshi sun tafi aikin hajji.To ko kasan unguwar daya koma? Ban rik’e sunan ba,saboda shi lokaci zuwa lokaci yana zuwa mu gaisa,amma Lado ya sani.

Kai Lado…Lado dayake biyama wasu almajirai karatu yad’ago yakalli Malam,Malam ya yafito shi da hannu zo mana.Yak’araso cikin ladabi.Ya sunan unguwar da Alhaji Hafiz yakoma? Ya amsa da ladabi unguwan Kanawa,amma Malam kafin tafiyarsu aikin hajjinnan mun had’u da Miqdad yace sun tashi sun koma Unguwan Rimi G.R.A inzo muje inga gidan,ni kuma ranar baka nan ni zanma yara darasu shi yasa ban bishi ba, amma na san idan sun dawo zaizo har nan ya daukeni muje.Malam yace”to kinji ko?Tayad’a kai tamusu godiya.

Tadawo gida agajiye lik’is ga mugun 6acin rai,tadinga zagin Shedrak zagin tsamen nama tun mijinta yana tayata har abin ya isheshi yayi shiru dan abun na ta ya wuce makad’i da rawa,zagin shi takeyi kamar cin kwan makauniya, yadda take mishi tofin alatsine sai yaji ba dad’i “Lallai na ka na kane ko ya cinyeka bazai tauna k’ashin ba”ai koda suka yafeshi suka barma musulmai shi amma dai ai still blood brother d’in shine.

Dakarfi yabuga sandar hannunshi a k’asa”Wannan zagin da kike ma Shedrak ya isa haka for what?Tanunashi da yatsa Shedrak d’inne baka so a zaga?To an zageshi matsiyaci kawai,ai dama yadad’e yana mana wannan mugun baki “Dinatu ya ishe kifa” yafad’a a tsawace dan banga abinda yamiki ba,shine yazo yatasa k’eyar Kasham sai sun tafi koko itace ta saci jiki tafi har inda yake?

Ta tafa hannaye cikin bala’i”Holy Mary mother of christ yanzu saboda Shedrak kake min wannan hayagagar…Ashe kai munafiki ne, tunda har kake fad’a dani akan masu sallah?To kasani tayi d’as d’as d’as dayan yatsunta”as from today an daina dafa abinci a gidan nan kowa yazage yanemi kud’i yaciyar da kanshi,idan Kasham tadawo shikenan everything will be normal.

Jikinshi yayi sanyi,fushin daya taso dashi yane mishi yarasa,sai yakoma rarrashi madadin shi da za a rarrasa”hun kud’i k’are magana.Yaro da kud’i abokin tafiyar manya.Hajiya naira Zainabu-Abu me maganin surukan zamani… Inji Sadi Sidi Sharifai.ALLAH ka azurtamu da arzik’i na halali.ALLAH muna niman tsarinka daga masifar talauci????.Idan tahana shi abinci ai ya kad’e har ganyanshi, baya aikin kome,tunda aka sallameshi daga leburancin daya keyi na titin jirgin k’asa,to dama aikin ba wani na azo a gani bane,sai dai motsi yafi la6ewa indai ba niman ka a keyi ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button