
Dabara ba ta d’aure kaya dole sai da igiya.
6 Jumaada Awwal 1441
1 January 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na goma sha d’aya.
Hajiya Sumayya Kantiok Donatus…
Ta canja tayi kyau na ban mamaki, kome na musulunci ya fara ratsa ta,sai dai ko a d’awafi baiwar ALLAN nan bata manta da Julaibib ba.Kullum addu’arta ALLAH yamallaka mata shi yazama mijinta,dan ita har kwanan gobe bata ga wani namiji kamar Julaibib ba.
Makonsu biyu da dawowa tafara zuwa makaranta Sanawiyya kansancewar ta me k’wak’wa da san karatun kullum iliminta k’aruwa yake yi,dan addu’o’in cikin Hisnul-Muslim wallahi kad’an ne bata haddace ba,a kwaita da tambaya sai kuma akayi sa a mutan gidan suna da ilimi dai-dai gwargwado suna mata bayanin kome dalla-dalla ba jibge.
Maman Hasan tabita da kallan tausayi”Iska na wahalar da me kayan kara”ta tsuniyar gizo ba ta wuce k’ok’i”Julaibib,d’an Sarai ko Enigma Man,wad’annan sunayan dai duk wayewar garin ALLAH sai ta kira d’aya daga cikin su,sun san labarin Julaibib a baki duk da basu ta6a ganin shiba.
Rannan dai Miqdad ya galla mata harara”Ke malama kar ki damume da maganar wani d’ansarai mutumin da ko hoton shi baki dashi.Wani lallausan murmushi yasu6uce mata”na rantse maka da ALLAH inada hotunanshi,ni ban san yadda akayi da nazo nan ban gansuba ina tunanin Lidiya ce ta bincike min jaka ta kwashe su amma da hannuna na sakasu.Bros karka damu duk ranar danaje Zonkwa bazan dawoba sai da hotunan shi”za kaga kyakkyawan bak’in mutumi na,me tsabta,ma’abocin sa fararan kaya.
Sumayya…a d’an firgice tad’ago sannan ta amsa”Na’am.Lafiya kika zabga wannan tagumin?Takad’a kai kwallah sun cika idanunta tamaida kanta jikin kujeran dan ba ta so su zubo “Maman Hasan Julaibib ne na kasa yin yak’i da zuciyata wajan cireshi a cikinta, kullum sai na yi mafarkin shi sai dai ban kwanta bacci ba me yasa?Saboda abinda kika sa a zuciyarki kenan tunanin shi,duk abinda ka kwallafa rai da shi to a mafi yawan lokaci sai kayi mafarkin shi”sa rai a ci shi ke kawo jin yunwa”
Takamo hannayenta,Sumayya ki fahimci wani abu”d’an Adam da kike ganinshi to shi yake saima kanshi mutunci da daraja,shi zai kame kanshi sannan mutane su d’aukeshi da mutunci su girmama shi”Haja ita takema kanta kud’i.kin damu dashi da yawa,sannan abin takaicin bai san kina yi ba harara a duhu..kilama ya manta ya ta6a ganinki,shi yana can hankalin shi a kwance yana gudanar da al’amuran rayuwar shi,ke kina nan kin takure kanki cikin tunanin shi”wannan fa kamar aikin banza ne sammakon gaida mak’iyi.
…Julaibib yana da matar aure makaranta ake jira tagama musha biki,kuma k’anwata ce…kalaman matar Musaddiq kenan ranar dataje musu murnar aure…
Tasauke numfashi”to amma ai banyi laifi ba ko a addinance.Maman Hasan tajijjiga kai”kwarai kuwa bakiyi laifi ba,hakan ya halatta sai dai a yadda muka saba a al’adance namijine yake furta hakan ga ‘ya mace,saboda kawaici irin na Hausa-Fulani,sai dai ban san sauran al’ummatai ba,ba kasafai matan suke yin haka ba.Kiyita addu’a ALLAH alhakimune ba yadda ba ya shirya al’amura. Jikinta yayi sanyi ba wata gaskiya bayan wannan”a hankali tayi furucin nagode Maman Hasan da wannan tunatarwa.
Miqdad yafito daga d’akinshi yana karya hula.Sumayya tabishi da kallo yanayi da d’abi’unshi suna mata shige dana d’ansarai shima ma’abocin sa fararan kayane.Yayi murmushi ganin kallan da take mishi”Sumayya ya akayi ne? Tayi yar dariya”wallahi Bros kayi kyau ba k’arya wannan shigar sunnan ta k’ayar dani fa. To nagode,yau ba Islamiyya ne?Akwai sai zuwa anjima.
Hafsa tafito daga d’akin-girki tana kallanshi “Yaya Miqdad baza ka tsaya kaci abincin bane?Yad’an sosa kunne”fita zanyi.Tad’an marairaice”ALLAH sarki Yaya Miqdad inata sauri ne fa,wallahi na kusa gamawa. Yakalli agogon dake d’aure a hannun shi na dama”Ina bazan tsaya ci ba gaskiya.Ta turo baki gaba gaskiya ni dai banji dad’iba.Sai kawai tajuya tana k’unk’uni. Yarik’o hannunta”baba tawaje nah,kiyi hak’uri kiran gaggawa aka min a wajan aiki,yadafa kafad’arta yad’an d’age gira cikin murmushi”Yaya Miqdad ne fa?Tad’an harareshi tana dad’a turo baki ni dai…yatari numfashin ta”kinga kwantar da hankalin ki”bayan sallar azahar zan aiko a kar6a sai inci acan shikenan ko?Tad’anyi tsallan murna”yauwa Yayanmu to adawo lafiya”tabashi hannu sukayi musafaha suna dariya.ALLAH yasa tawaje nah…suka d’aga hannu suna ma juna adabo.
Julaibib tunda yatafi sau d’aya yazo sai yanzu da suka samu hutun Semester, haka yadinga zaga gidajan yan’uwa yana gaishesu.Suna zaune shi da Musaddiq suna tattauna al’amuran daya shafesu Safiyya tayi sallama tashigo d’akin-shak’atawar sanye da dogon hijab suka gaisa cikin mutunta juna ta tashi tafita,bata sake shigowaba sai da tagama abincin rana tahad’a duk ahinda za su buk’ata a babban tire takai musu.Musaddiq yakar6eta da saurin shi”yauwa Safiyya,ALLAH dai yak’ara miki albarka da lafiya.Shida ita suka kalli juna suna murmushi,ta tsuguna da niyyar zuba musu yace”a ah wallahi amaryata ai kinyi me wuyar jeki kawai tuzuru zaiyi kome.
Julaibib yayi kamar bai gane shagu6en ba,yad’auki kofi yazuba lemun kashu da abarba,yayi hismillah yafara kur6a.Musaddiq yace kai ni bangane bane anyi yamma da kare ni baza ka zuba min bane?Ya ajiye kofin yana nuna kanshi da yatsa”ni kace zanyi kome ko tuzuru? Ni sunana Julaibib ban san wani tuzuru kake nufi ba, ka san dama ni ban saba da sai anyi service d’ina ba, yazuba abincin a faranti yafara ci.Musaddiq yagalla mishi harara”wa za ka raina ma hankali? Malam kayi aure kaji dad’in rayuwar ka,dawani tuzuru ne bayan kai?Yayi kamar ba dashi yake magana ba.Musaddiq yad’auki cokali to ajiye abincin muci mana. Yajanye farantin da sauri”a ah yau bazan ci abinci dakai ba,tashi katafi wajan matarka taba ka abincin abaki ma wannan ba damuwata bace.Au haka za kace?Yad’an d’age gira yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi”Eh haka nace da magana ne?A ah ba ni da tacewa…wai ankama 6arawo da kayan sa ta.
A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar alhamis Sudaida da d’an d’okinta na san ganinshi ta tafi gidan Inna,amma irin amsa gaisuwar daya mata yasa jikinta yayi sanyi”wai an jefi kaza da gishiri,baiko d’ago kai ya kalleta daga tarin littafan daya barbaza a saman tebur ba,a dak’ile yake amsa gaisuwar da take mishi da lafiya…Tazuba mishi idanu na wucewar wasu dak’ik’u sannan ta d’ora envelop d’in hannunta a saman tebur d’in gabanshi.Yakalli envelop d’in a gajarce yacigaba da rubutun shi ba tare kuma daya d’ago kanshi ba yake tambayar ta”na meye? Haushinshi yakamata,ta galla mishi harara tajuya”nima ban sani ba.garammm tabugo k’ofar da k’arfi.Sai lokacin yad’ago yakalli k’ofar,yad’an motsa kafad’a yacigaba da abinda yakeyi har aka fara kiraye-kirayen sallar azahar bai gama ba, turesu kawai yayi gefe yayi alwala yatafi masallaci.
Bai samu damar bud’e envelop d’in ba sai daya zo kwanciyar bacci”d’an k’aramin frame ne me hoton ayatul Qursiyu,a kasanshi wani tsibiri ne me ban sha’awa ruwa yana gudu…sai d’an takadda anyi rubutu sad’ara hud’u.