GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

…Julaibib…na san kome zan ba ka a banza zaga ganshi,amma wannan na tabbatar ma kaina koda ba ka so na,na san za ka alkinta shi ko???
I dore you my Enigma…
Kasham Kantiok Donatus.

Yakaranta yasake karantawa,yakai hancinshi yana shinshina frame d’in daya ke k’amshin irin turaran ta.Yayi lallausan murmushi dan yaji dad’i har ranshi yajijjiga kai”Tabbas kin bani abinda zan alkin ta Kasham…na kuma gode. Sai ya d’orashi agefen gado yakwanta yana azkar d’in bacci, yanata kallan frame d’in yana tuna had’uwarsu da Kasham tun ranar farko da kallan farko da sukama juna a haka har bacci yayi awan gaba dashi.

Azaure sukayi kaci6is taja baya da sauri jakar hannunta ta su6uce zata fad’i a k’asa,cikin zafi nama yacafe,yamik’a mata, takar6a tana gaishe shi. Idanunshi akanta”wa yabaki envelop d’in nan?Tamishi wani irin kallo fuska a d’an yamutse”Malama Kasham.Tun yaushe?Baku dad’e da tafiya Zaria ba.Yad’anyi murmushi cikin gyad’a kai”To nagode,Kawu yana ciki?Eh yana ciki.Yajuya zuwa cikin gidan tabishi da kallan mamaki d’ansarai kamar kuli-kuli yake da ba a gane gabanshi wallahi,Jiya fa shine yamata halin-ko-inkula amma yanzu har da wani murmushi taja dogon tsaki “Kai ALLAH yasauwake maka.

Sumayya ta zage dantse tana kwankwad’ar madarar ilimi,gaba d’aya ta canja ta zama wata ta musamman”Unique charisma”fatar jikinta ma ta canja saboda canjin cima,a gidan Alhaji Hafiz za a ci abincin safe me kyau me gina jiki,da ranama haka a mafi yawan lokuta ba sa kasafai suke yin girki da daddare ba,sai dai asha su gwanda,Inibi,tuffa,dabino a kora da madara idan kuma abincin za ayi to mara nauyi za a dafa.

Tana zaune a d’akin-shakatawa sanye cikin bak’ar doguwar riga kirar Saudiya,tayi rolling da mayafin tana nazarin”Dealing with Depression Islamically na Dr.Bilal Philips.Ta gaji lik’is a gangar jiki,amma zuciyar ta, tana k’ara k’arfafarta tad’aure ta k’arasa.Karo na uku kenan tana kallan d’an siririn bak’in agogon dake d’aure a hannunta ta k’osalokacin dawowar Hafsa yayi daga makaranta ta tambayeta wani abu.Tatsiyaya ruwa a k’aramin kofi daga babban tambulan takai bakinta da bismillah kad’an kad’an take kur6a tana jujjuya kofin kamar tana nazarin ruwan har ta shanye,ta ajiye kofin tana fad’in Alhamdulillah…

Ahankali ta d’ora kanta ajikin kujerar tare da lumshe idanunta tana addu’a “Yahaiyu Yaqaiyumu birahmatika astagis,aslihli fi sha’ani kulluh,wala takilni ila nafsika d’arfata ainin” wato “Ya Rayayye dauwamamme,da rahamarka nake niman taimako ka gyara min al’amurana gaba d’aya,ALLAH karka barni da kaina koda da k’iftawar idanu ne”.

Miqdad daya shigo yatarar tana wannan addu’ar ya amsa da amin Sumayya. Tabud’e manyan idanunta masu maik’o da suka d’an canja kala saboda baccin da yake shirin kamasu.

Abrugo? (Ka dawo)

Yagyad’a kai dan shima yanajin yaran,Alhaji Hafiz ya koya musu kuma duk sun iya ko Maman Hasan tanaji.

Umburak (Na dawo)

Wannan addu’ar muhimmiyace daya kamata ace kowani musulmi yana yinta kullum ta ALLAH.Yad’auki littafi d’aya daga cikin tarin littafan data barbaza a saman tebur yana dubawa, yaciro biron daya soke a aljihun gaban rigarshi yana gyara mata wata kalma data rubuta ba dai-dai ba,yanuna mata kinga yadda ake rubutata, wancan wata ma’ana ta daban tabayar ba wacce aka tambaya ba.Tagyad’a kai “na gane,nagode Babban Yaya.

Yamik’e zai shige d’akinshi, danshi ba ma’abocin zaman d’akin-shak’atawar bane. Tad’an kalleshi”afwan Yaya Miqdad ga wata tambaya,yakoma yazauna”Uhun ina jinki”Tace yau Malam nasiha yamana da muke rik’e sunanil rawatib kar muyi sakaci dasu,to ni kuma gaskiya ban san meye su d’in ba,to kuma dana tambaye shi shima bai fad’a min wai ya bani jinga (Assignment)in tambayo gobe yana jiran amsa. Yayi murmushi gaskiya Sumayya kina burgeni nan gaba da alama babbar malama za ki zama. Tajijjiga kai”Insha-ALLAH nima sai na ba al’umar manzon ALLAH gudummawa daga d’an abinda Ubangijinmu yanufeni da sani na ilimi,ka san fatana Yaya Miqdad?Yagirgiza kai.Fatana ALLAH yabani miji me ilimi wanda zai dad’a d’orani akan tafarkin dai-dai, wanda zai sa in zama productive akaran kaina,how I wish Julaibib ya aure ni…

Yanunata da yatsa”ke dai da Julaibib d’in nan?Enigma man ko?Tayi yar dariya ai kuwa, yana da wuyar fahimta sai dai ni na fahimce shi, baya so adame shi,baya san hayaniya,baya shiga abinda ba da shi akeyi ba,amma ni har yanzu ina san shi”so gamon jini”yakad’a kai”ga shi kuma so ba samu ba,sai dai fatanmu har kullum ALLAH yaji6anci al’amuran mu.Amin big Bros.Sukayi murmushi.

Mukoma kan tambayarki abinda ake nufi da sunanil rawatib sune sallolin da akeyi na nafila kafin sallar farilla ko bayan sallar farilla kamar :-

Sallah raka’a hudu kafin sallar azahar da kuma rak’a biyu bayanta.

Sallah raka’a biyu bayan la’asar.

Sallah raka’a biyu bayan magriba.

Sallah raka’a biyu kafin sallar asubahi.

Babu wani musulmi dazaiyi wad’annan sallolin (Nafila) raka’a goma sha biyu(12) a kowace rana yana me d’a a da ganin girman ALLAH da k’ank’antar da kai a gareshi ba tare da ALLAH ya gina mishi gida a Darul-karamah (Aljannah) ba.

Sumayya ba ki da burin samun gida a aljannah?Tayi dariya so kai.Yagyad’a kai “To ki d’auki sahawarar da annabin mu,annabin rahama daya bamu, kidinga yin wad’annan sallolin.Tad’an kalleshi”Bros bayan sallolin farilla dasu shafa’i da wutri,raka’atal fajri da sallar walha ne zan dinga yin wad’annan sunanil rawatib d’in.Eh Sumayya. Tagyad’a kai”na gane Bros I’m very glad, Godwilling daga yau zan fara ina kuma neman taimakon ALLAH da d’orewar shi har k’arshen numfashi na kataya ni addu’a. Ya amsa da To Sumayya Ubangiji yayi jagora.

Suna kwance da Khadija tana duba Hadisin Annawawis Collection a cikin littafin Islamic Studies na B.a’isha Lemu(ALLAH Yajik’an ta.ALLAH yakyautata makwanci????)baturiyar Ingila (England) data musulunta ta auri babban alkali d’an jahar Niger (Minna) Sheikh Ahmad Lemu tayi karatun addini me yasa take bada gudummawa da tarin iliminta ga al’umar manzan ALLAH shekaru masu yawa.

Dawowar Alhaji Hafiz daga masallaci sallar la’asar yasa takalli Khadija data ke kwance a gefenta,ta gaji da wasanta tayi bacci,sai ta gyara mata kwanciya sannan ta tafi d’akin shak’atawa.

“Yauwa Sumayya.ya amsa barka da dawowan data mishi.Takalleshi cikin natsuwa “Uncle na ji wa’azi sosai daga bakunan malamai mabambanta game da girman zumunci da irin matsayinshi a addinin musulunci da hukuncin me yanke shi dame sadar dashi, Uncle ni da kai a jinsi yaran Bajju ne,amma a addini mu musulmai ne, kuma addininmu na musulunci bai hana mu sadar da zumunci ga yan’uwanmu wad’anda ba musulmai ba, to amma kai me yasa ba ka sadar da zumuncin ka da sauran yan’uwanka na jinsi Bajju?

Yakad’a kai”Sumayya ban k’i sadar da zumunci dasu ba har sai da naga suna niman kasheni… Bari kiji abinda yafaru tun kafin a haifeki.

“Wata rana hanya tabiyo dani ta Zonkwa sai kawai na k’arasa k’auyan mu Madauci dan mu gaisa tunda na kwana biyu ban jeba, wallahi kamar jira ta sukeyi sai ganin Kantiok, Dinatu da wasu daga cikin yan’uwanmu matasa a bayansu d’auke da kokara da adduna, nafito daga cikin motar ina kallansu da mamaki “Kantiok ina za kuje da tsakar rana haka?…ban gama rufe baki ba naji an sakar min adda a tsakar ka,aiko nan take jini ya 6alle,wani ne daga cikin yan’uwan mune da wannan aikin, danaga da gaske k’ara saramin yake shirin yi aida gudu nakoma motata amma kafin inyi wani yunk’urin tayar da ita sun fara dukar motar,gilasanta sun farfashe,banyi aune ba naga sun fincikoni wasu suna ba da umarnin a samin taya in babbake kawai kowa ya huta,wallahi na ci na jaki da gasken-gaske.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button