
Ibrahim Me-Lambu shine tushensu Alhaji Ibrahim,dan haka Ya’ya da jikoki da Ya’yan jikokin gidan suna amfani da Me-Lambu a k’arshen sunayen su na makaranta,wasu ma da wane ko wance Me-Lambu suke amfani.Ibrahim Me-Lambu ya samu sunan Me-Lambu ne saboda sana’arshi ta saida kayan lambun kamarsu:-tumatur,tattasai, albasa, alaiyaho,yalo,latas, karas,lafsir da sauransu da sauransu.
Asalinsu yan k’aramar hukumar Tsanyawa ne ta Jahar Kano.Cirani yakawosu garin Zonkwa Iyaye da kakanni,dad’in garin da kuma k’addarar ALLAH inda ya rubuta maka zama to ba makawa anan d’in zaka zauna kome dad’i ko rashin dad’in waje,da suna zuwa ganin gida daga baya suka daina sai kalilan daga cikinsu dan suna da yawan gaske a Zonkwa,wasuma basu da sauran dangi na jini a Tsanyawa,Unguwa gudace dasu k’atuwa ta musamman da ake kira”Lungun Kanawa.Sukayi zamansu a nan suka hayayyafa.
Alhaji Ibrahim matanshi na aure guda biyune,Mama itace uwargida kuma mahaifiyarsu Musaddiq,Khausar,da sauran kanninsu maza da mata.Sai Umma mahaifiyarsu Aminu,Adnan,Sudaida da tarin kaninsu maza da mata.Kan ya’yansu a had’e yake saboda matan sunada fahimtar juna,mijinsu kuma yana musu adalci dai-dai iyawarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Julaibib yana zaune atsak’ar gidansu yana nazarin wani littafi duk da wancan makon suka samu hutu.Musaddiq yashigo da sallama,yad’an daki kafad’ar Julaibib “Haba malam an samu hutu kaima ya kamata ka hutafa”Julaibib yayi kamar ba dashi yake maganaba.Musaddiq ya jijjiga kai”gaskiya na gaisheka”yawuce dak’in Inna, tana zaune a inda ta idar da sallar walha,sai yasaki labulan”to barinje na dawo anjima”.Daga ciki ta amsa”shigo ai na idar.Yazauna suna gaisawa,sai yafara mata hirar Safiyya budurwarshi da sak’on data bashi yakawo mata.
Aminu shima yashigo da sallama yana fad’in shi wai d’ansarai baya gajiya da karatune Inna?Yakama ha6arshi da hannun dama”Tabbb ina ruwan Alhuda-huda,koda yake bazai gajiba tunda yafi sha’awar zaman gida, gaskiyar magana wannan da macece da sai ince ALLAH ya kashe ya ba mijinta kakarshi ta yanke saka wallahi.Inna takalleshi”kamar yaya?Yawaiwaya inda Julaibib yake zaune”o Inna aishi ya huta da fitinar mata tayawan tambayar unguwa, zani gidan wance,anyi haihuwa zan shiga barka, zanje dubiya dan gidan wance an mishi shayi, muna da biki agabas,gobe suna a arewa,jibi tarewar yar gidan wance a yamma, zani, zani, zanin mata ai bata k’arewa.Inna tayi dariya.
Julaibib yakalleshi ba laifinka bane, ka ci bashi zan kuma rama.Aminu yagyad’a kai”Nima zan so haka,ina nan ina jira,yashige d’akin-girki yad’auko kunun tsamiyarshi yafito”Inna yau naci aikine kamar ba gobe,tun daga sallar asubahi sai yanzu zan koma gida.Inna takalkeshi da tausayi “Wayyo sannu,a lallai ka aikatu neman kud’i makahon aiki, ALLAH dai yak’aro masu albarka.Amin Inna nagode barinje in kwanta.To ALLAH huta gajiya.
Kasham…da yaransu na Bajju yana nufin abu me kyau.kuma a zahirin gaskiya wannan suna ya dace da ita dan me kyance, matsakaiciyace a tsawo,me k’irar kalangu,gata da yalwataccen gashi me tsawo da santsi,shi yasa ba kasafai take kitso ba, manyan idanunta masu maik’o(Oil eyes)da d’an k’aramin bakin ta su suka k’ara mata kyau na musamman,wankan tarwad’a ce a yanayin kalar fatar jiki,itama dalibace anan Kaduna State College Of Education(KSCOE) Gidan Waya.Aranar farko a kuma kallan farko data ma Julaibib so da k’aunarshi suka mamaye zuciyar ta ba tare data shirya hakan ba, duk tarin samarin dake mata nacin suyi soyayya sai taji ba wanda yamata nan duniya daya wuce Julaibib,ta so k’warai a ranar suyi magana amma hak’anta bata tadda ruwaba, saboda kwarjinin daya mata lokacin data tunkareshi,ashe gaba da gabanta aljani daya taka wuta.To amma me san d’an tsuntsu shi yake binshi da jifa”naci da shishshiginta yasa suka fara gaisawa duk da idan ba ita ta gaishe shiba ko zasu had’u sau dubu a rana bazai nuna yama ta6a ganin taba.
Duk inda tasan zata ganshi to in dai ba tana da lecture ba to tana wajan,yau da gobe sai ya fahimci tana neman wuce makad’i da rawa sai yadad’a kamewa,amma da Musaddiq sun saba dan suna d’an ta6a hira dan shima yana da miskilanci idan baiga dama ba,amma gangaran d’in miskilai sai “Julaibib Abdullahi d’ansarai “.
Musaddiq yana zaune a capteria yana cin abinci tazo tasa meshi tana fad’a mishi “Wallahi Musaddiq na ka sa danne zuciyata,na ka sa yin yak’i da ita,gaskiyar magana ina san Julaibib zan aureshi”.
Cikin tsoro da mamaki yace kina san Julaibib?Yagirgiza kai”to gaskiya ki cigaba dayin yak’in wajan ganin kin cireshi a zuciyarki,baza ki samu abinda kike so…ta tareshi da sauri”me yasa za kace haka? Saboda baki dace dashi ba”wai d’an dambe ya d’auki adda”ni nasan Julaibib farin sani wallahi,kinga kuma addininmu ba d’aya bane. Idanunta suka ciko da k’walla,”wai yau ita ake fad’ama namiji ba zai so taba a yadda take d’in nan me kyau…
Tayi jimmm..na wucewar wasu dak’ik’u “Musaddiq kafad’a mishi “ni Kasham tanuna kanta ina sanshi,ina neman goyon bayan shi ya yadda muyi aure,na mishi alk’awari zanyi abinda yakeyi (Sallah)zanbi addininshi (Musulunci) Abincin da bai gama ciba kenan yamik’e dan zata dame shine kawai.Tabishi da kallo dan ALLAH kafad’a mishi.Ya amsa da To.
Rannan tana zaune a d’akin karatu, nazari da bincike(Library) ta ka sa yin abinda yakaita tunanin Julaibib ne kawai yacika kanta,kamar ance ta d’ago kai sai kawai gashi yashigo dak’in,yaja kujera yazauna.
Ganinshi yak’arasa kashe mata jiki, tanajin wani sabon yanayi daya tsirga ilahirin jiki da zuciyarta,gefe guda kuma tana jin takaicin k’in kar6an tayin soyayyar data keta mishi naci duk da kasancewarta k’wararriya data isa da kanta in dai a fagen hilatar d’a namiji yafad’o tarkon tane,ba wanda ta ta6a d’anama tarko bai fad’aba sai Julaibib,ta rasa me zatayi dan shawo kanshi,dan abinda takeji game dashi ba irin abinda takeji game da sauran maza bane,wani irin abune me sark’ak’iya,me zagaye ilahirin gangar jiki da zuciya,ita kanta bata san ya zata fassara shiba wallahi.Tasake kallanshi rubutu yakeyi cikin natsuwa,takad’a kai.
“Julaibib…you’re an enigma”.
Ahankali ta furta hakan,sannan tabi d’akin da kallo mutane dayawa sun gama abinda yakaisu sun fita,saita samu k’warin gwiwa koda zai wulak’anta ta bazai mata ciwo dayawa ba tunda mutane kad’anne. Tamatsa gaban kujerar dayake zaune,tasunkuyo tana kallan fuskarshi”Sannu da aiki Julaibib…tafurta hakan da wani salo irin na ta na yanga.Bai d’ago ya kalletaba kamar yadda take fa ta,bai kuma amsaba “shiruma amsace”rubutun shi kawai yakeyi.
Tatsareshi da manyan idanunta masu maik’o,ya mata kyau cikin fararan kayan,yau kanshi ba hula,kwantaccen bak’in gashin kanshi yanata sheki da k’amshin irin mayukan gyaran gashi da yake amfani dasu,jikinta ya gama mutuwa murus,ga k’amshin arabian perfumes d’inshi yadad’a jefata a wani irin yanayi,ta lumshe idanunta wani murmushi ya su6uce mata “ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baiciba yayi burgima”taja dogon numfashi tana zuk’e k’amshin,ahankali kuma tafara fesar da iskar tabaki ta hanci sannan tabud’e idanunta tacigaba da mishi kallan k’auna me cike da shauk’i har yagama rubutun,yatattara takaddun daya shigo dasu a gefe, yakwashi wad’anda yad’ibo a d’akin yamayar dasu mazauninsu.