GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Shigowar Maman Hasan yasa yanuna ta da yatsa”kin gan ta nan Sumayya har yanzu muna zaman lafiya.Tazauna a kujera tana kallansu”Eh gani nan,to me namaka kake ta nunani da yatsa?Tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a.Sumayya tayi murmushi ganin wani irin kallon k’auna me cike da shauk’i datake mishi.Tsam tamik’e za ta shige d’aki “Sumayya dawo kiyi zamanki mana…dasauri tak’arasa shigewa ta rufo k’ofar tana girgiza kai “wanan kallan da abinda zai biyo bayan shi ba dani ba gaskiya”ga d’a da fatalwa.

Bayan shekara d’aya Sumayya ta gama karatunta,har tasamu gurbin karatu a jami’ar Kaduna (KASU) tad’ora degree a Islamic Studies ta kuma k’ara zage dantse tana kwankwad’ar madarar ilimin addinin musulunci, dama can a goge take ga Ilminta na Catering &Hotel Managements,gashi kuma yanzu wani fannin na daban take karanta,yanzu larabci kamar dama can dashi ta taso sai dai me zurfi daya wane ba ta ganewa har sai ta duba k’amus d’in larabci…

Sai dai weak point d’inta Julaibib musamman da sukaje taran Muslim Student Society Of Nigeria(MSSN)a jahar Katsina ta ganshi ganin idanun ta yayi kyau,yadad’a zama d’an gayu,shigarshi kamar ko yaushe ta fararan kaya.Shine shugaban kungiyarsu ta ABU,har tagaban shi tawuce suna tsaye shi da Maimun amma ba ta ga Musaddiq ba,wallahi daurewa kawai tayi ba ta musu magana ba amma ta dad’e a tsaye a gefensu tana k’are mishi kallo tana wata kissima a zuciya,har had’a idanu sunyi amma bai gane taba saboda tasa nik’abi ta kuma rufe k’wayar idanunta da gilas.Tunda taganshi d’aliban da suke k’ark’ashin kulawarta suka ka sa gane kan Amirarsu Sumayya…Da akace tazo zasu yi magana da yan Jami’ar Ahmadu Bello kasancewar su yan Jaha d’aya ne,kwanciya tayi wai bata jin dad’i,dan wallahi idan taga Julaibib har kuma sukayi magana to tsohon mikin k’auna ne zai 6alle gwamma daga nesa-nesa kallan kura…

Yafito yana sa links d’in hannun riga Maman Hasan tanuna mishi Sumayya.Sai yazauna yana kallanta”Tatsuniyar gizo bata wuce k’ok’i,abu d’aya yahana shi zuwa yasamu Julaibib suyi magana akan Sumayya shine yace baya son ta,to ko dabara kad’ai bazata d’aure kaya ba dole sai da igiya.Yakira ta da kakkausar murya tunanin me kikeyi?Tun d’azu kin tasa kofi a gaba kin kasa san shayin.Yatsareta da idanu cikin d’aurewar fuska,ganin haka yasa ta sunkwui da kanta tayi shiru.

Kina sane da maganar danace za muyi?Eh Uncle.Yanunata da yatsa”Ina sane da abinda ke faruwa, banyi niyyar magana ba,to sai dai naga abin yana k’ok’arin shige makad’i da rawa,mutane uku suna zuwa da niyyar auranki amma kina korarsu,wannan kuma ba dai-dai bane tunda ba haka zaki dauwama ba dole za kiyi aure,dan haka akwai abokin kasuwanci na dayace yana sanki to nayi na’am da shi dan mutumin kirki ne,kuma ban 6oye mishi kome game da keba, shima ya amince yana sanki a haka.To jiya yasame ni dan niman izini yana so zai zo ku gaisa.

Sumayya karki 6oye min kome idan ya zo baku dai-dai ba,dan ba auran dole zan miki ba kin gane ko? Me zatace?Tagyad’a kai”Uncle zan zama me biyayya zan kar6i duk hukuncin daka zartai,dan haka ko wanene shi na yadda zan aureshi dan na san baza kamin za6en tumun dare ba.Yayi murmushi kin amince kenan?Tajijjjiga kai”eh Uncle na amince.To ALLAH yamiki albarka,yasa ki gama da duniya lafiya,ki kuma yi hak’uri da kome akan Julaibib, Sumayya wani hanin ga ALLAH baiwa ne.To Uncle nagode. Yamik’e shikenan ki daure kisha shayin.Takai kofin tsakanin la66anta kamar tana sha,suna fita shi da Maman Hasan da take mishi rakiya tadire kofin a k’asa tawuce d’akin baccin su takwanta tare da lumshe idanunta, kwallan da suka cika idanun suka samu damar zubowa sharrr…ranta ba dad’i sai ta fara karanta”ALLAHU-ALLAHU Rabbi laa’ushrika bihi shai’an.Tana ta maimaitawa har bacci yayi a won gaba da ita,sai da lokacin makarantar yakusa Maman Hasan tashiga ta tasheta.

…Aiki ke koran bak’o d’an gida ya dad’e da sabawa.
…Nagaji sai rago????

10 Jumaada Awwal 1441
5 January 2020

We Ibrahim’s Daughters ????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi nagoma sha biyu.

Tana yankema Khadija faratan ta Hafsa tashigo da sallama,tazauna a hannun kujerar tana kallansu cikin murmushi sun sha wanka da kwalliya kayan su iri d’aya,doguwar riga k’irar Bahrain ruwan makuba, k’amshin turen ta ya mamaye d’akin.

Tad’an kalli Hafsa”bakin ki da magana. Tayi yar dariya”Yaya Sumayya ba wata magana,amma fa kina da bak’o a waje.Tayi luuu da idanun ta kamar zata rufesu,sai kuma tabud’e su gaba d’aya a fuskar Hafsa “bak’o?Ta tambayi Hafsa itama.”Eh bak’o ne a wajan ki amma wasu lokutan nakan ganshi tare da Baba.Tad’aga idanu takalli agogon da ke manne a jikin bangon d’akin k’arfe uku saura minti goma na yammacin. Tagyad’a kai “fad’a mishi ina zuwa.Ta amsa da to.Sumayya tabita da kallo da tunanin irin mutumin da idanun ta za su gane mata wani daban,ba d’ansarai ba.Tayi wani d’an huci cikin kad’a kai,sai da tagama yanke mata faratan duka sannan ta d’auki farin dogon hijab d’inta a saman kujera tasa.

Miqdad yana zaune a d’akin-shak’atawar yana cin abincin rana yad’an kalleta ganin ta nemi waje ta zauna”Sumayya ba jiranki ake yiba?Tamishi nuni da Maman Hasan data basu baya tana kallan taga,waya takeyi.Ya watsa hannu”kije kawai ai ta san da zuwan shi ita ta aiki Tawaje nah(Hafsa)tafad’a miki,kema ai kin san gama wayar Maman Hasan ba yanzu ba,idan suka fara hira da tsoho me ran k’arfe Malam Muhammad Aminu sai kin sike ko kuma kud’in wayar ya kare an katse sadarwar tasu.Tarik’o hannun Khadija Miqdad ya girgiza kai “saketa kiyi tafiyar ki,ke Khadija zo nan ya yafito ta da hannu.Bata so ba sai dai ba yadda za tayi ne,yanuna mata kujera zauna anan kijira ta,ba dad’ewa za tayi ba kinji ko? Tagyad’a kai idanun ta sun cika da kwallah,yayi kamar bai gani ba yacigaba da cin abincin shi.

Yana zaune a dakalin dake harabar gida yana duba wani d’an k’aramin littafi Dammm…taji ruguzowar wani abu me k’arfin gaske a k’ahon zuciyar ta, ta dafe kirji cikin Istirja’i dak’yar tak’arasa wajan da sallama.Yamayar da littafin aljihun gaban rigar shi yana amsa sallar. Yana d’ago kai zai kalleta caraf idanun su ya had’u,shi dama ya san ta,dan d’ai-d’ai kun ranane baya ganin ta lokacin da take zuwa Sanawiyya, itace dai yau tafara ganinshi.

Takauda kai ba wani babba bane dan ita tayi zatan sa’an Uncle za ta gani tunda yace abokin kasuwanci shine,dogo ne kuma shima yana da nashi kyau da fasalin, yana sanye da shadda me maik’o ruwan siminti, hularshi k’ube ruwan siminti da ratsin bak’i, sai bak’in takalmi sawu waje.Yakatse shirun”ranki yadad’e barka da fitowa.Sai lokacin ta gaishe shi,yamik’e tsaye yana nuna mata wajan Bismillah ga waje ki zauna “tagirgiza kai “bak’on ka annabin ka”kai yafi cancanta daka zauna. Nagode amma ki barni a tsayen,ni namiji ne zan jure tsayuwar koda awanni biyu ne.Bata ce kome ba tazauna “Yad’anyi gyaran murya “Malama Sumayya kin san abinda yake tafe dani ko?Fuska a d’an yamutse ta amsa”Uhhh” ba tare data bud’e bakin taba.Yabita da kallan nazari dama Alhaji Hafiz ya sanar dashi kome shi yasa take amsa mishi a d’ad’d’age kenan,sai yayi murmushi cikin kad’a kai.Sai fa ya yi hak’uri dan ya san jin kan mata sarai bare kuma ga matsalar k’auna.Wayyo!Sumayya kema sai kinyi hak’uri,ni da shi ba d’aya bane koda kuwa uwar mu d’aya uban mu d’aya ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button