GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sumayya kin san wani abu kuwa? Yadda yayi furucin kamar irin sun dad’e d’in nan ya zo da saurin shi yana so yabata labrin wani abu da d’umi-d’umin shi.Sai tayi saurin d’ago kai tad’an kalleshi amma bata ce kome ba.Idan mukayi aure,ALLAH yabamu haihuwa d’anmu na farko indai namiji ne to ni d’in nan yanuna kanshi da dan yatsa, na miki alk’awari ki rubuta ki ajiye,da bakinki me albarka zaki mishi hud’uba da sunan Julaibib… Dan ki tabbatar ni masoyinkine na gaskiya me san abinda kike so.Cikin mamaki da dariyar data kasa dannewa na jin dad’i ta kalleshi kai tsaye ta d’an bud’e idanunta”to ya akayi kasan sunan shi? Yanunata da yatsa”an ta6o inda yake miki k’aik’ayi ko?

Shi Salim wani irin mutum ne da duk abinda yake so yana yin k’ok’ari wajan sanin wasu muhimman abubuwa game dashi,ta yadda bazai sha wahala wajan mu’amala dashi ba.Ya gane soyayyar da take mishi wata jarabtace daga Ubangiji,tunda ya fad’a mata bazai aure taba,kuma ta yi hak’uri ta fauwalama ALLAH duk da yana ranta,to yanzu ga shi,shi ya zo zai maye gurbin shi da gyara harda alakoro Insha-ALLAH sai tayi alfahari dashi a matsayin mijin sunnah.

Kayi alk’awarin sama d’anka sunan shi?Yajijjiga kai”Eh wallahil-azim na yi alk’awari. Tamishi wani lallausan murmushi sannan ta kauda kai daga kallan juna da sukayi nawasu dak’ik’u.Daga nan hira ta6alle…

Zuhair ne yakatse musu hirar ta hanyar kawo ma Salim ruwan alwala a buta dan mukhtarin la’asar yayi.Tanata kallanshi yana alwalar cikin nutsuwa kuma cikakkiya har yagama yamaida hular shi kanshi sannan yamik’a mata butar,sukayi sallama dan an fara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai,Miqdad ma yafito shi da Zuhair sun tafi masallaci dan sauke farali.Tabi bayanshi da kallo har yafita daga harabar gidan “Yanada saurin shiga rai.

Fuska a sake tashiga gida. Maman Hasan tace”Yaya dai Sumayya?Sai ta zauna a kujera tana yar dariya wallahi haka kawai take jin nishad’i,rabon data tsinci kanta a irin wannan yanayin tun ranar da d’an Sarai yamata nasiha data daina k’arama sama hazo(shan taba) Maman Hasan ta tayata da murmushi”a Alhamdulilla labarin zuciya a tambayi fuska.

Da safe tana shan shayin na’ana’a, kalla,kanumfari,da ya’yan algarib sai tiriri yake yi da k’amshi me dad’in dake k’ara mishi armashin da ko bakayi niyyar sha ba idan aka baka sai ka sha.Hafsa tashigo da waya d’akin baccin su dan yau bata fita d’akin-shak’atawa ba,anan ta zauna tana karyawa tana nazarce-nazarcenta.

Tamik’a mata wayar”ga shi ana magana”takar6a takai kunnan ta da sallama,ya amsa sallamar yana tambayar ta ya gida ya karatu?A takaice ta amsa”Lafiya…Alhamdulillah. Sukayi shiru na wucewar wasu dak’ik’u”wake magana?Takatse shirun.

“Salim ne.

Salim… Salim…

Tafad’a ta maimaita cikin tunanin ga no wa ye haka?Sai yatari numfashin ta,a d’an marairaice”Innalillahi…Ina zan sa kaina…? Mummuna ya ga mata.Kar dai ace baki gane Salim d’in ba?Haba Sumayya to Salim d’in kine fa. Ta d’an bud’e idanu”Oh…Ya Rahman afwan Salim ka san bani da lambar ka.Yayi yar dariya”na sani nima jiya ne na kar6i ta ki lambar a wajan Alhaji,yana nufin Alhaji Hafiz.Kin san ranar dana zo k’aunar ki ta mamaye k’wak’walwa ta har natafi ban baki ba,nima ban kar6i ta kiba.Suka gaisa a mutunce”Sumayya da yammacin yau nake san zuwa wajen ki shin kina da lokacina?

Tad’anyi murmushi”haba Salim girman ka ya wuce haka,ai ko ba lokacin ka to dole a k’irk’iroshi bare ma a kwai,amma I’m really sorry to say…ka san yanayin karatu,yau k’arfe goma na safiyar nan zan tafi makaranta kuma gaskiya sai biyar da rabi za mu gama lectures sai dai gobe.Yagyada kai”ba damuwa da yau da goben duk d’aya ne.Kad’an suka ta6a hira sukayi sallama.

Sumayya da Salim k’ank’anin lokaci suka aminta da juna.Sumayya har ranta take jin ta samu abokin rayuwa,saboda Salim mutum ne me sauk’in kai,bai cika d’aukar al’amura da zafi ba.Dariya takeyi saboda kalaman shi,yabita da kallo cikin zancan zuci,wallahi kome na ta akwai tsabta,hak’oranta farare tas kamar ba dasu take tauna duk abinda yake shiga cikin cikin taba.

“Sumayya dawani man goge baki kike amfani ne?Takatse dariyar”man goge baki kuma?Yajijjiga kai eh dan na ga hak’oranki sun bambanta dana mutane da yawa cikinsu kuwa har da ni d’in nan yanuna kanshi,kamar bakya 6a tasu da abinci sai d’aukar idanu suke yi.

Kana so kasan sirrin?Sosai kuwa.To ka zama me yawan aswaki ba sai lokacin alwala kad’ai ba, kuma musamman kasa mu aswakin al’araq,wannan shine sirrin ga shi kuma sunnane.Kuma ka san ko masana a harkar bincike na yanzu da suke ganin sune tushen ilimin kome,to sunyi bincike kuma sun ga no sun kuma tabbatar yin aswaki goge hak’ora da chewing-stick magogi,ba brush ba yana k’ara k’arfin dasashi. ALLAU-AKBAR tsarki ya tabbata ga ALLAH. Manzan ALLAH sai da yace ba dan kar ya takura ma al’umma ba da ya farlanta mana yin aswaki. Salim ya jijjiga kai gaskiya kin tunatar dani abinda na manta,nagode miki Sumayya lallai tunatarwa tana amfanar da mumini.

Sumayya ki bani dama in tura Iyayena,ai mun d’an fahimci juna,yanzu mun san wasu daga cikin halayan junan mu ko? Duk da dai ba a sanin maci tuwo dole sai miya ta k’are. Takalleshi cikin natsuwa”Salim a da zuciya ta, tana rayamin inyi musulunci saboda Julaibib ne, kuma koda na kar6i musulunci na kar6a ne saboda shi,amma cikin k’udirar Ubangiji sai zuciya ta,tacanja daga wancan tunanani da niyar.A yanzu na yadda saboda zatin ALLAH nake musulunci,da taimakon su Uncle ta fuskar nasiha da zuwa Islamiyya da sauraran wa’azi daga bakunan manyan malamai mabambanta duk su suka cusa min yin abu saboda ALLAH,na san na rasa d’an Sarai amma zuciya ta bata aminta da barin musulunci ba,dan na gamsu addinin musulunci shine addinin gaskiya,ina zaune kwatsam sai Uncle yazo min da maganar ka,a lokacin na amsa mishi ne saboda kawai tsakani na da Uncle ba musu har abadan duniya,wallahi kome rashin jin dad’in abu in dai yabani umarni inyi ko in bari zan yi,dan na san soyayya ce a tsakanin mu,har fa zuciyata ta fara min sak’a da mugun zare amma ban biye mata ba,nayi ta addu’a ina neman rok’on Ubangijin mu yakawo min agaji kar in biye ma sharrin ta.

Amma a ranar da idanuna suka fara yin tozali da kai,kalamanka da kome naka sai suka burgeni, zuciya ta tayi wasai…A ranar na kar6e ka kamaye gurbin Julaibib,tad’an sake kallanshi cikin natsuwa Salim har yanzu ina jin wani abu game da d’ansarai amma ba soyayya ba,saboda sanadiyar shi nabar kowa da kome, harkar da nake yi nabin maza da tara abinda duniya daga garesu yabar zuciya ta,fatana kawai in mallake shi,to sai nagane a yadda yake me natsuwa da kamewa hak’ata bazata tadda ruwa ba, sai na bijiro mishi da maganar aure, na sadak’ar zanyi sallah ba dan kome ba sai dan kawai na k’wallafa rai shi d’in kawai nake san mallaka,manyan idanunta masu maik’o suka cika da kwalla.Ubangijin mu alhakimu ne,sai gashi ya canja min da wani daban kuma zuciya ta ta aminta da shi,dan haka Salim kai nake so soyayyar da ba ka da abokin tarayya.Julaibib dai yana da lada a wajan allah saboda halayan shi masu kyau da tsabta wanda addinin musuluncine yazo dasu da kuma karatun addinin da yayi shine ya siffantu da siffofin,nima sai yanzu nagane wasu halayanshi da, a da nake mugun mamakin me yasa shi baya kaza?Me yasa yake kaza? Tad’aga hannayen ta sama ALLAH kahad’ashi da macen albarka,kamilalliya me addini.ALLAH kasamu daga cikin wad’anda ta sanadiyyar mu wasu za su samu haske irin na addinin ka.Ubangiji ka kara mana lafiya ka kara inganta mana Imanin mu.Yanata kallanta cikin so da k’auna,sai yadad’a aminta da ita dan Alhaji Hafiz ya mishi bayanin kome dalla-dalla ba jibge.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button