
Sumayya…
Bata amsa ba tad’ago a hankali suka kalli juna”Sumayya yau rana ce ta musamman a wajan mu ko?Tasunkwui da kai daga kallan da yake mata tana murmushi.
Sai da a ka tsaida ranar auran Salim da Sumayya,Miqdad da budurwar shi Zainab sannan Alhaji Hafiz yatashi Miqdad d’in musamman dan zuwa k’auyan su Madauci wajan d’an uwanshi,bai ta6a zuwa garin ba amma da tambaya sai gashi a k’ofar gidan.Yanata sallama yaji shiru ba a amsaba,zuwa can sai yatuna to su ina ruwansu da wata sallama?Sai yakai hannu yafara rank’washin k’ofar.Yana gyangyad’i kamar a sama yaji ana buga k’ofar yamik’e dasauri yana fad’in”kai wanene haka daba zai shigo ba,bayan k’ofar ba kulle ta akayi ba amma yatsaya awaje?Sukayi kallan kallo na wucewar wasu dak’ik’u sannan ya matsa mishi yashigo,suka zauna a fararan kujerun robar tsakar gidan har yanzu kallan juna sukeyi “daga ina haka d’an Samari?Kantiok ya tambaye shi.Miqdad yayi murmushi daga Kaduna nake.Ai yana jin haka sai yamik’e ya rungumeshi yana dariyar murna”haba no wonder naji a jikina kamar na san ka to sai dai a ina?
Kai yaran Shedrak ne ko?Ina Kasham? Ya baku zo tare ba?Su ma suna nan zuwa.Yasaki Miqdad yafita dasauri,lemun kwali Don Simon,ruwa da kofi yakawo mishi gashi nan kasha barin kar6o maka abinci… Ya tareshi da saurin”a ah kabar shi kawai.Yaja yatsaya yana kallanshi”Kazo gidana amma baza ka ci abincin mu ba saboda me?Yad’an shafa fuskar shi”Kayi hak’uri Kawu ina azumi ne amma da ba abinda zai hana ni ci.Yadawo yazauna to kai saboda ALLAH za kayi tafiya ba sai kabar azumin ba?Ya amsa mishi cikin girmamawa”Kawu azumin yana da muhimmancine.
Suna ta hira kamar sun saba. Miqdad yabashi sak’on da aka aiko shi wasik’a ce Alhaji Hafiz d’in yake sanar dashi”Kasham tana wajan shi tana kuma sallah,yanzu kuma ta samu mijin aure,dan haka zai aurar da ita,amma bayan bikinza suzo Insha-ALLAH,sai takardan kud’i (cheque)an rubuta mak’udan kaud’ad’e an sa hannu sai zuwa gidan kud’in(Bank)a Kar6a “Hallelujah..yafad’a saboda mamakin adadin kud’in daya gani a rubuce,gaskiya shi har yagama aiki bai ta6a kar6an rabin-rabin wannan ba,yana ta dariyar murna,shi kuma Miqdad tasbihi yakeyi a zuciyar shi”ALLAH buwayi gagara misali hatta wushiryar shi irin ta mahaifin shine,sunyi kama sosai sai dai wannan fari ne, mahaifanshi kuma baki ne.
Kiran wayar ta tashigo yad’aga da sallama”Yaya Miqdad ya hanya ka sauka lafiya ko? Yagyad’a kai”na sauka lafiya Sumayya gani ga Kawu na ganshi ganin idanuna.Tayi yar dariya.”to masha-ALLAH ba shi wayar.Yamik’a mishi.Yana jin muryarta yayi dariyar jin dad’i “Kasham sai kuma yajuya harshe zuwa yarensu na Bajju,sun dad’e suna hira sannan yafara gyad’a kai da alama wata magana me mahimmanci take fad’a mishi yake gyad’a kan cikin gamsuwa”amin Kasham nagode ALLAH yamiki albarka.Miqdad yakad’a kai”wato kowa dai ya san akwai ALLAH yadda da shine dai ba kowa yayi ba.
Yana shirin tafiya yace ni har zan tafi banga Maman Sumayya bawai Kasham ce ta koma Sumayya?Eh kawu”Yayi murmushi kawai, Maman Kasham ta tafi kasuwa gashi kuma sai yamma za ta dawo,to ka kwana mana.Yayi yar dariya”Kawu ina da ayyukan da zanyi da yawa amma zan zo na musammma idan nasamu sarari zan kwana in ga sauran yan uwan mu.To shikenan ALLAH yakaimu”yarakoshi har inda ya ajiye motar shi yana bashin tabbacin zaizo ayi d’aurin auran su dashi.To Kawu aiko za muji dad’i ba kad’an ba,yad’auko rafar kud’i yan naira ashirin guda d’aya yabashi,sai yagirgiza kai,haba My Son ni ban ba ka kome ba ai kuma bazan kar6e na kaba, kabarshi kawai nagode,ga cheque na kud’i me yawa da zan kar6a.Miqdad yakalleshi cikin natsuwa”Kawu ai wancan d’an uwan kane yabaka,wannan kuma d’an kane yabaka,tashi kyautar daban,tawa ma daban,sai dai ban sani ba d’an uwa ya fi d’ane a wajanka?Yasake mik’a mishi sai yakar6a yanata mishi godiya,sukayi sallama cikin farin ciki.Yad’aga hannu yana mishi adabo tare da addu’ar ALLAH yatsare ya kiyaye mishi hanya,har motar tasha kwana ta6ace ma ganin shi, sannan ya juya,yak’are ma gidan kallo lallai gyara yazo tunda kud’i sun samu.
Lokacin daya k’arasa cikin gari har an idar da sallar azahar dan haka yayi alwala yayi sallarshi raka’a biyu ta k’asaru yayi azkar d’inshi sannan yakoma mota yana bin shagunan bakin titin da kallo yana kuma tunano kalaman Sumayya “Idan kaje Rahama Store to ka tambayi shagon Julaibib za a kai ka,yana tambaya kuwa aka nuna shi shagon sai dai kash…Musaddiq ne a shagon, daya tambayi Julaibhib yace yana gida sai bayan sallar la’asar zai fito.Yamik’a mishi wata yar madaidaiciyar jaka ruwan k’asa”Idan ya fito abashi “Miqdad yasake mik’a mishi hannu sukayi musafaha yajuya ya fita daga shagon.
Shima ya so ganin wannan d’ansarai d’in da Sumayya take bala’in so,yayi murmushi ganin yadda tayi da yace bazai kar6i sak’on wani Julaibib ba dan shi ba d’an aiken ta bane, wallahi idanunta har sun cika da kwallah ta sunkwui da kai k’asa bata kuma magana ba,sai tabashi tausayi.Sumayya yakira sunan ta,tana d’ago kai sharrr…hawayan masu d’umi suka zubo a kyakkyawar fuskar ta,tasa hannu ta share su sannan ta amsa a raunane”na’am…Yad’an harareta ke fa raguwa ce daga wasa sai hawaye? Tagirgiza kai”ni ma ban so hakan ba, ban kuma san ya akayi suka zubo ba,ni da Julaibib ai ba wata alak’a kuma sai ta yan uwan takan musulunci,sak’on dazan ba ka wallahi tun a Makka nasiyo mishi,da kuma na san zan had’u dashi a taron MSSN d’in nan na Katsina dana tafi dashi na bashi…ni a yanzu ina san d’ansarai ne saboda shi mutumin kirki ne me addini,amma karka manta ina da jan gwarzo na,dubu jiran mutum d’aya tad’an d’age gira tana wani lallausan murmushi sannan tafurta sunan Salim.Yayi yar dariya “Sumayya kenan so gamon jini.yashige mota yazauna ya d’aura belt sannnan yatayar cikin ambatan sunan ALLAH yad’auki hanyar Kaduna garin gwamna.
Musaddiq yana lissafin wasu kud’ad’e bayan sallar la’asar Julaibib yashigo da sallama yazauna yana kallanshi har yagama yayi rubuce-rubucen shi a littafin da suke rubuta kome na kud’ad’en kasuwan cinsu yamayar cikin dirowa sannan ya ajiye mishi jakar a gaban shi “dazu aka kawo maka.Inji wa?Musaddiq ya dauki mukullin motar julaibib d’in zai fita sannan yabashi amsa “Wallahi ban san shiba bak’o ne”ni nafi. Yagyad’a kai ” To Allah yatsare.
Yabud’e jakar dabinon ajwa yagani, ruwan zamzam da farin miski sai envelop da sunan shi yake jiki 6aro-6aro da manyan bak’ak’e
“JULAIBIB ABDULLAHI D’ANSARAI…
Yabud’e da tunanin wa ya aiko mishi da wannan sak’on?
Assalamu alaikum warahmatulla. Julaibib ina gaisheka gaisuwa irin ta addinin musulunci.Ya su Mama?Ya karatu?ALLAH yamaka jagora.Julaibib kasance wata yau raye a cikin musulunci ba wayau da dabara ta bace,a ah ganin damar Ubangijinmune”Alhamdulillahi bi ni’imatil Islam.Wallahi a duk inda naje babu rauni da tsoro zan bayyana identity d’ina saboda addini na yafi kowane addini tunda ALLAH mahaliccin muma yafad’i hakan a Alqur’ani cewa”Addinin musulunci shine addini ko awajan shi “Subhanallahi addinin mu kome anyi programming d’inshi an ba mu.
“Julaibib na san kai mutumin kirkine me k’ok’arin bin dokokin ALLAH gwargwadan iko, dafatar baza ka canja daga yadda na sanka ba. Dan ALLAH kar kabari shaid’an ya rud’eka, rayuwar jami’a ta canja ka.
Daga k’arshe nake mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Me maka fatan alheri a rayuwa.Musha ruwa lafiya…