
Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)
Dammm…zuciyar shi tabuga da k’arfin gaske.Sumayya…Sumayya yafad’a ya maimaita cikin san tantance wai wace Sumayyar?Yad’auki wasik’ar yakaranta yasake karantawa,kenan ita ce Amira Sumayya da ta musu lecture akan”Media Influence?(Tasirin kafofin sadarwa)Kasham dai daya sani wacce sukayi College of Education ita ce ta musulun ta?ALLAH buwayi gagara misali,ko shekaran jiya sun samu sak’o ta k’ark’ashin k’ungiyar da take jagoran ta akan Islamic Vacation Conference(IVC)yayi zuru cikin tunano wasu kalamanta da suka ta6a had’uwa da ita a wata seminar da akayi a”National Teachers Institute Kaduna akan”Post Primary Institution Programmed”(PPIP)alokacin ta d’aga hannu aka bata damar yin magana”Tace a gajeran tunani na a kirashi da Propaganda zai fi armashi fiye da Program… Bata gama rufe baki ba d’akin yad’auki kabbara kowa yayi na’am da hakan,wallahi shi yasha jin wannan sunan Sumayya Kantiok Donatus to sai dai ko sau d’aya bai ta6a tunanin wai Kasham ce ba…Yatuna ranar farko da daddare a wajan seminar abincin alfarma me rai da motsi aka aiko mishi dashi wai inji Amira Sumayya to ganin sauran ma an basu sai bai kawo kome ba”ashe albarkacin kaza k’adangare kan sha ruwan kasko
“Amira… Sumayya Kantiok Donatus…
Yafurta sunan a zuci…sai yaji wani irin yanayi ya ziyarci ilahirin gangar jiki da zuciyar shi game ita na farin ciki.Ashe shine bai gane taba saboda nikabin data sa,har da gilashin data rufe idanunta”Ina mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Musha ruwa lafiya”abinda ta rubuta a k’arshen wasik’arta kenan.Yajijjiga kai “Tabbas yau goma ga watan”Muharram”yau kuma ga duk musulmin daya samu iko yana azumin “Ashura”Itama tana azumin kenan kamar yadda shima yake yi?Yakad’a kai cikin farin ciki.
“Sumayya ina miki fatan alheri a rayuwa,ALLAH yadauwamar dake a musulunci har k’arshen numfashin ki,ALLAH yaba ki mijin da zai rik’eki da amana,mijin da zai ha6aka miki ki cigaba a rayuwa…
Yad’auki jakar ya rataya a kafad’a yana kulle shagon sai ko ya hango wani d’an k’auyan su Kasham daya ke aikin share-share a Fajumali-Hotel yakira shi…yak’ara so da fara’ar shi”idan kaji gangami da labari,wallahi kamar ka san yunwa nake ji.Yakalleshi da natsuwa ai ba abinci na ce zan ba kaba,kuma ai yanzu lokacin cin abincin rana ya wuce k’arfe hud’u da rabi na yammaci fa?Yabuga k’atuwar hamma baki a bud’e kai da kake a k’oshe kenan wallahi rabo na da abinci tun daren jiya sai yan kame-kame dana yi da safe,ka taimaka min da abinda zan sai abinci dan ALLAH.
Yagirgiza kai”k’wandala ta bazan ba kaba tunda na san mashayar d’one za ta tafi…zai fara mishi rantse-rantse yakatse shi da sauri”kaga in dai yunwar da gaske kake ji to jeka katako kace ma Umma tabaka tuwo na yadda zai isheka in jini…Yad’aga hannayen shi sama”Praise the Lord,Thank you God”yajuya da sauri yaje ya kar6o yazauna zai faraci Julaibib yasake kallanshi cikin natsuwa”Kasham tana ina ne yanzu? Kasham…Kasham… Yakalli Julaibib wace Kasham d’in?Kasham kanwar su Alhamdu.Yata6e baki “Kasham ai ta dad’e da barin gida wai ta zama me sallah irin ku,ance wai tana Kaduna amma ni”I don’t give a damme ko ma a ina take da me take yi fa.Hakane to idan ka gama ka mayar mata da kwanan.Yajuya yayi tafiyar shi…
Sautu a kasuwar wauta jahilci.
14 Jumaada Awwal 1441
9 January 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSICIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na goma sha uku.
Rana ba ta k’arya sai dai uwar d’iya taji kunya,ranar juma’ar d’aya ga watan Rabi’a Thani aka d’aura auran Salim da Sumayya,Miqdad da Zainab a ranar kuma ko wacce ta tare a gidan mijinta,sai dai mahaifin Kasham bai samu zuwa ba saboda zazzabin da yake yi.
Sumayya sune zaune lafiya suna da fahimtar juna,suna ma juna uziri shi yasa suke da kwanciyar hankali,suna kuma fatan hakan yad’ore har k’arshen numfashin su.
Yana karya hular k’uben dazai sa tashigo da sallama,ta kar6i hular tak’arasa karyawa tasa mishi. Yad’anyi gyaran murya”Ya dai Sumayya yau fa na ganki wata iri.Me ka gani? Shiru yayi yana mata kallan nazari “banga kome a fuskar kiba amma yana yinki ya nuna akwai wani abu,yadafa kafad’arta “kar kiji kome Sumayya ni mijin kine,ba ki da wanda za ki fad’ama damuwar ki sama dani.
Yamata wani kallo”Sumayya mecece matsalar?Fad’a min in har akwai wannan amincin dake cikin zaman na mu. Tamayar da turaran data gama fesa mishi sannan tajuyo cikin d’an murmushi”Miji na nawa ni kad’ai ko?Yagirgiza kai”ai na fad’a miki Sumayya a yanzu bani da buk’atar sake aure,kuma in dai zaman na mu yad’ore a haka to ai ko kin isheni rayuwar duniya, yakalleta amma fa ba alk’awari na miki daga ke ba wata har abadan duniya ba.Tajijjiga kai”d’aya daga cikin abubuwan da suke k’aramin k’aunar ka a zuciya ta kenan fad’ar gaskiya kome d’acin ta. Sukayi murmushi.
Tasake kallanshi cikin natsuwa”tun daren jiya nayi mafarkin Mama kuma har yanzu mafarkin ya tsaya min a rai sosai,dan haka nake neman alfarma kabarni in je in ganta,ka san Uncle ya hanani zuwa wai sai nayi aure idan miji na ya barni shikenan ban san dalilin shi na hakan ba.A yanzu na san kima da girman da uwa take dashi,lallai ta cancanci a mata kome dan a samu albarkar ta, rayuwa tayi kyau duk da rashin sallar da ba tayi, ina san ganinta kewar ta ta dameni,zan kuma yi k’ok’ari wajan ganin na shawo kanta mun dai-dai ta,wata kila tsawon shekarun da mukayi bamu sa juna a cikin idanu ba yasa idan taganni ta yafe min,ni dai ina ta addu’a ALLAH yasa sanyi a zuciyar ta,na san ba abinda yafi k’arfin Ubangijin mu.Yajijjiga kai”gaskiya ne Sumayya iyaye suna da girma da daraja a wajan Ya’yansu, a addinin mu na musulunci suna da mafificiyar daraja sama da kowa.To yaushe kike so mutafi? Bani da za6i,sa mana lokaci.Yad’auki agogon shi yana d’aurawa “Shikenan za muyi magana da Alhaji idan naje kasuwa.To nagode.Yayi murmushi kawai
Tafiyar Dinatu Kaduna waja taransu na zumuntar mata a babban majami’ar su dake Sabon Tasha”Evangelical Church Winning All” (ECWA)na tsawon makonni biyu yabashi damar gyare-gyaran dayace zai yi, gidan yafito rasss har da sabon fenti ko’ina yanata kyalli.Ranar data dawo ta cika da mad’aukakin mamaki tana ka me da ha6a take tambayar shi”ni dai tun kafin in tafi Kaduna da ma na lura da wasu canje-canje saboda yawan kashe kud’in da kake yi,kai ko a ina ka samu mak’udan kud’ad’en da kayi wannan gyaran?Anya kuwa Baban Alhamdu ba ka daga cikin masu zuwa cikin gari suna fasa shagunan hausawa?Dama kwanakin nan abinda ake ta musu kenan.
Yagalla mata harara”ai kema kin sani ko lokacin dana ke ganiyar k’uruciya banyi sata ba,bare yanzu da girmana da kome ALLAH yasauwake.To me kake siyarwa da bazan yi tunanin haka ba?Ba kome. Tazuba mishi idanu “gaskiyar magana bazan yadda dakai ba in dai ba fad’a min in da kasa mo kud’in nan kayi ba. Yamik’e”ai nima ba so nake yi ki yadda dani d’in ba. Tabishi da kallo har yafita.
Da daddare har ya fara bacci ta tashe shi,fuska a yamutse yake kallan ta dan yanzu shima ya daina d’aukar raini tunda hatimin nasaran nan yana dashi”lafiya kin katsemin bacci kuma baki ce kome ba?”Baban Alhamdu please… Kafad’a min in da kake samun kud’i,dan hankali na ya k’i kwanciya.Yasake d’aure fuska”Brother na Shedrak shi ya aiko min da cheque na mak’udan kud’ad’e,kuma ina so ki sani Kasham tabbas tana wajan shi,kuma tana sallah, bayan haka ma tayi auri wancan watan, na so zuwa ma to sai dai zazza6in dana yi yahana ni tafiya kuma suna nan zuwa, ina fata yanzu hankalin ki zai kwanta.