GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tadaki k’irji cikin ambaton Yesu alhamisu me ce to(Jesus Christ)tamik’e cikin tafasar zuciya”Kasham tana sallah bayan haka ma ta yi aure ni mahaifiyar ta ba tare da sani na ba?Tayi d’as da yan yatsunta ban ta6a sanin kai munafiki bane sai yau,wato ka tura Kasham taje tayi sallah dan adinga kawo maka kud’i ko?Haba no wonder baka wani nuna damuwar ka lokacin da muka neme ta muka rasa.Wallahi tirrr…da halin ka,kai munafikin addini ne tunda kana supporting masu sallah tacika gidan da hayagaga…

Da abin ya ishe shi shima ya daka mata tsawa kin dameni fa,ki rufe ma mutane baki ke baki san dare bane?Tagirgiza kai, ai idan kaga na yi shiru to kafad’a min in da Shedrak yake a Kaduna gobe in buga sammako in d’auko yarinya ta dan bazan barma wasu tsinannun hausawa ba.Yayi shiru kamar ba dashi take magana ba,zuwan ca kuma ya d’ago ya kalleta”To tunda baza kiyi shiru ba, bari kiji kafin ki tafi Kaduna ni zan rigaki yin sammmakon tafiya,kuma na rantse miki da ALLAH tafiya ta bata dawowa bace,nima na bar gidan nan kenan har abadan duniya muje muci gaba da yin sallah sai in ga wanda zaki dinga wanke ma hannu a ka.Taja dogon tsaki “karka bari sai da safe yanzu ma kahad’a kayan ka dan ka tafi sai me?Mutuwa za a fasa ko hijabi? Tajuya garammm tabugo k’ofar,sai dai fa maimakon bacci yayi awon gaba da ita kamar yadda suka sa ba duk dare sai tane mishi tarasa sai kalaman mijin ta suka dinga dawo mata.

Kusan mako d’aya kenan bataje kasuwa ba wai dan kar yatafi Kaduna bata sani ba,yayi dariya Dinatu kenan idan nayi niyyar tafiya Kaduna zaman ki acikin gidan nan bazai hanani tafiya ba…Dan ALLAH ba wannan nake san jiba,kace kawai ka fasa tafiya,kayi hak’uri da abinda na maka raina ne ya 6aci kayi hak’uri. Yakalleta ai dama kece za ki sani tafiya ba tare dana shirya hakan ba, amma idan muna zaune lafiya ai bazan yi tunanin tafiya wani waje ba tare dake ba”we’re together for better for wost till death due part us.

Yana waya tashigo d’akin-shak’atawar ta zauna a hannun kujerar daya ke zaune tana kallan shi, ganin wayar ta k’i k’arewa yasa tamik’e zuwa taga,tad’aga labulan tagar tana kallan mutane na kai kawo a cikin yamma cin.Bataji zuwan shi ba sai maganar shi taji cikin rad’a, tajuyo da sauri tana yar dariya”Kai Salim da girman ka da kome kake irin wannan furucin? Yagalla mata harara “Kaji yar rainin hankali ke kuma…sai ta sunkwui da kai tana murmushi.Toh shi kenan adai bar kaza cikin gashinta kawai.Ta girgiza kai”Uh uh gwamma kawai a yankata a dafata acinye ta kowa ma ya huta.Yamata wani kallo cikin d’an d’age gira,itama tarama irin kallan da manyan idanunta masu maik’o sai ko ya kyalkyale da dariya”Hun Sumayya me duniya…Za ko a yi yadda kika ce da kazar, tad’an motsa kafad’a, sukayi murmushi.

Yakalleta cikin natsuwa”to ya jikin na ki? Abinda yadawo dani daga kasuwa kenan dan na kira wayarki ta ki shiga matsalar sadarwa”naji sauk’i sai dai bani da k’arfi kuma bakina ba d’and’ano.Yagayad’a kai”to Alhamdulillahi, k’arfin jikin sai a hankali za ki da wo dai-dai,ya6are vitamin c guda d’aya yasa mata a baki.

Yakamo hannunta suka zauna a kujera “kuma na zo miki da wani albishir.Albishir?Ta tambaye shi”eh albishir.Tayi murmushi fad’i albishir d’inka yanzun nan in wanke ka tasss…da ruwan tukwuici.Yakalleta da natsuwa yana murmushi”d’azu munyi magana da Alhaji akan tafiyar mu Zonkwa ya ce idan mun shirya shima a shirye yake musa rana, to nafad’a mishi jibi idan ALLAH yabamu a ran rai da lafiyar za mutafi,dan haka sai ki fara shiri yau,gobe da sassafe zan tafi kasuwa duk abinda kike so asiyo sai ki fara rubuta shi tun yanzu kin gane ko?Wani dad’i yamamayi zuciyar ta sai ta dad’a jinta garau ba sauran ciwo,ta k’ank’ame shi cikin murna”nagode mijina lallai ka cancanci tukwuici sai ta fara mishi wani irin salo na ta,da sauri ya k’waci kanshi yana dariya har hular shi tana fad’uwa”Ke wannan ne tukwuici?Ni na zaci wasu mak’udan kud’ad’e za ki sa min a asusun ajiya ta ta gidan kud’i?Tagirgiza kai”A ah wannan ai somin ta6i ne”tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a. Yagayada kai”ah nima na aga alama to amma jama’a na jira na akasuwa amin afuwa sai na dawo anjima.Tam adawo lafiya suka d’aga hannu suna ma juna adabo????

Cikin nishadi suke tafiyar Alhaji Hafiz da Sumayya suna fad’a musu sunayan garuruwa da k’auyaukan da suke ta wucewa,sannu a hankali har suka shiga garin Zonkwa.Alhaji Hafiz yajuya yana kallan Maman Hasan”yanzu zamu shiga shalkwatar k’aramar hukumar Zongon-Kataf sai ku bud’e idanu ku fara kallo “tafiya mabud’in ilmi “Hafsa tace Zongon-Kataf d’in na gaba kenan?Eh Hafsa yana gaba ina gama idan zamu koma tacan zamu biya kuga garin sai mu bi ta Pambegua mu kuma gida.

Jikin Sumayya yayi sanyi tunda matuk’in motar Miqdad yakusa shiga k’auyansu Madauci dan ta san halin Mamanta bata da mutunci “ALLAH kamin maganin abinda bazan iyaba…bani da kowa sai kai…

Sumayya…

A sama taji kiran Alhaji Hafiz”na’am Uncle me kace? Nace na ga an samu cigaba me yawan gaske,kinga wancan asibitin?Takalli asibitin”Eh Uncle.Da nanne wajan da muke buga k’wallon k’afa.Sukayi dariya, Zuhair yace dama Baba kayi wasan k’wallon k’afa?Eh Zuhair amma da ne.Yad’anyi tsallan murna”nima daga yau zan dage in koyi buga k’walan k’afa.Yakalleshi da kulawa “a ah Zuhair bana maka sha’awar k’wallan k’afa,na fiso kayi karatu sosai kazama”Cheif Judge”ko ka fasa zama alkali me adalcin ne? Yakyalkyale da dariya yana bud’e idanun shi”Wallahi ban bafasa ba.Yauwa Zuhair d’ina ALLAH yamaka albarka.

A inuwar barankacin k’ofar gidan Miqdad ya tsaida motar,yabi gidan da kallo an gyara shi gwanin sha’awa,ba kamar zuwan da yayi watan nin baya ba,itama Sumayya abin ya mata dad’i tana rik’e da hannun matar Yaya Miqdad Zainab suka shiga gidan da sallama” Baban na ta kamar ko yaushe yana zaune shi kad’ai a tsakar gidan yayi tagumi da duka hannayen shi”labarin zuciya a tambayi fuska,ranshi a 6ace yake,yasa hannu ya share hawayan da ya zubo mishi sharrr…yana d’ago kai idanun su ya had’u yamik’e da sauri da sauri cikin mad’aukakin mamaki”

Kasham…yanunata Kasham ke ce?

A sanyaye ta amsa”na’am Baba…

“Kasham kece nake gani haka? Halelujah suka rungume juna cikin murna”naji dad’in ganin ki Kasham…

Hankalin ta yad’an kwanta ganin shima ya saki ranshi”Baba ai bamu kad’ai bane…bata gama rufe bakin taba sauran suka shigo.yasake ta ya rungume Miqdad yana shafa kanshi”My son sannnu ku da zuwa.

Miqdad yanuna mishi Alhaji Hafiz”Here is your elder brother sai suka hau kallan kallo na wucewar wasu dak’ik’u aannan suka rungume juna suna ta kyalkyala dariya kamar wasu kananan yara

Awunba wan Shedrak(Shedrak Dan’uwa na)

Alhaji Hafiz ya janye jikin shi yana gabatar mishi da sauran,duk aga gaggaisa sai a k’arshe yasake nuna Salim wannan shine surukinmu mijjn Sumayya. Salim yak’arasa wajan shi cikin girmamawa dan ya gaishe shi,sai kawai ya rungumeshi cikin jin dad’i “Kaine karik’e mana yarinya da amana irin haka? Gaskiya naji dad’i nagode,ALLAH yama auran ku albarka,ALLAH yaba ku zuri’a masu amfani.Salim ya sunkwui da kai yana murmushi a ranshi yake amsawa da amin.

Daga wani d’aki suka fara jin wani irin tari matsanan ci, bayan tarin yad’an lafa cikin galabaitacciyar murya aka fara magana”Baba dan ALLAH kazo kabani ruwa” duk suka bishi da kallo

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button