
“Judith…
Abinda zuciyar Sumayya ke fad’a mata kenan. Tasake kallan Baban ranshi a 6ace yakesai kawai tashige d’akin Dammm… Zuciyar ta tayi wata rin bugawa da k’arfin gaske tayi mutuwar tsaye,numfashin ta yatafi wucin gadi na wasu yan dak’ik’u Judith ce a kwance marabanta da k’warangwal ya mushashshiyar fatar data rufe kasusuwan jikinta sai kuma numfashin da take yi.
Da rawar murya ta furta Kasham…sai lokacin Sumayya tadawo hayyacin ta, tafara Istirja’i sai ta fashe da kuka ko ba a fad’a mata ba ta sani cutar k’anjamau ce, tunda dama ba abinda take yi sai yawan ta zubar… Judith ta tare ta”Kasham kar ki zubar da hawayen ki a banza ni ai tawa ta riga ta k’are, taimake ni kawai da ruwa yau ban san laifin dana ma Baba ba,gaba d’aya yaki shigowa d’akin nan.Takalleta wa yake jinyar ki?
A hankali tace Baba.Tazuba mata idanu”Kin tafi yawan ta zubar d’inki kin manta da kowa a lokacin dakike cin duniyar ki da tsinki, ko gida bakya zuwa sai lokacin da kika bushi iska kizo zuwan asha ruwan tsuntsaye ki k’ara gaba,sai yanzu da kika ga mutuwa zaki dawo ki d’orama Baba abinda baiji ba bai gani ba?Tasake fashewa da kuka al’amurar rayuwar su ta taci barkatai da suke yi hankali kwance ya dawo mata, itama ba wayo da dabararta ne ya ku6ubtar da ita ba,ALLAH ne kawai yamata wannna gata da suturar da yanzu itama tana nan tana wannan kwamacalar.
Kukan Sumayya daya tsanan ta ne yasa suka shiga d’akin dan gane ma idanun su abinda yake faruwa.Adai-dai lokacin kuma zawo ya 6alle ma Judit tana kwance kamar gawa sai k’arni da wari daya cika d’akin.
Baban yabiyo su”dan ALLAH ku fito kubar wanna yar iskar yarinyar kar ku kwashi cuta,dan Sumaya tana jin k’arnin zuciyar ta ta tashi,tafara kelaya amai.Yakaisu d’akin- shak’atawar gidan kome atsare yake mayan kujeru da carpet ruwan k’asa sai kayan kallo a gefe da nu’urar sanyaya abubuwa(fridge) shima agefe duk sun zauna jungun-jungun saboda ganin Judith, kowa da kalar tunanin shi akan wani irin ciwo ne haka sannan me yasa ba a kaita asibiti ba? Me yasa Baban yake cemata yar iska a irin wannna hali na rai kwakwai mutu kwakwai? Amma banda Sumayya da Alhaji Hafiz da suka riga suka san dawan garin.
Baban me fara’a ne shi yadinga jan su da hira har dai suka saki jiki.Suna cin abincin da Hafsa ta girka musu yau an hutashshe da Kawunta.Dinatu tahigo gidan cikin kwala kiran sunan Kasham…Kasham… Kasham..
Sumayya ta cire hannunta a abincin tana Istirja’i kafin tashigo Sumayya ta mik’e, a k’ofar d’akin sukayi kaci6is,takalle ta sama da k’asa sai tayi murmushi”Hail Mary…tarungume ta.Sumayya ta rintse idanun ta tana jiran saukar dundu a gadan bayan ta amma bataji hakan ba, har suka saki juna tana dad’a k’are mata kallo, wani kyau da annuri na musamman tayi”Sannu Kasham tad’an dafa kafad’arta”na ji dad’in ganin ki suka shiga d’akin takalli Alhaji Hafiz”Sannu Shedrak shima ya canja mata gaba d’aya to yaushe raban data sa shi a idanun ta shekara da shekaru yayi kyau mijin ta kuma ya tsufa sai yaza kamar shine gaba da Shedrak.Suka shiga gaggaisawa.Ranar dai suna cikin farin ciki musamma Dinatu ganin duk wanda yazo musu sannu da zuwa sai ya yaba irin kyan da Kasham tayi kamar wacce take zaune a wata k’asa,kowa na so yaga na shi cikin wadata.
“Lallai zaman Kaduna ya miki dad’i.Inji Lidiya.Sumayya tayi lallausan murmushi”kawai kishirya kayan ki mutafi.Tagalla mata harara”ai ko da kikayi wannan kyan banga abinda zai rud’eni in bar addinina ba.Itama ta galla mata harara”a ina kike da addinin?Kina da maraba da pagan ne? Kasham kar fa ki zageni.Sumayya tasake yin murmushi”come on Lidiya ni dake ai mun san gaskiya ko dan kawai d’aci gare ta?Ba fa yau na sanki ba,na sanki farin sani kamar yadda kika sanni farin sani,ranar Lahadi kina zuwa majami’a? Sai ta mik’e cikin borin kunya”bana zuwa kuna bazan je ba sai kiyi abinda za kiyi dani.Tafice fuuuu tana surutai rubbish girl…tabita da kallo haba yarinya ba abinda zanyi dake,za kuma ki dawo ne da k’afafunki.
Sumayya tasa mu Maman a d’aki, ta tazauna akusa da ita sannan tafara rok’on ta “Mama dan ALLAH kiyi hak’uri kiya femin laifin dana yi, na san da ciwon haka azuciyar ki.Cikin fushi ta kauda kai”bazan yafe ba ki tashi ki bani waje.Haba Mama kiyi hak’uri kisa min albarka,ai har kwanan gobe ina sanki ina alfahari dake a matsayin mahaifiya,dan kinyi d’awainiya me yawa akaina tun ina cikin cikinki har kika haifeni, wallahi bani da abinda zan biya ki dashi.Tasake tuno girman hakkin y’aya akan mahaifansu musamman uwa da addinin musulunci yazo dashi kaico! Wanda ba ya cikin musulunci wallahi yana cikin duhu me girma, inama-inama tana da wani iko!? Da ayau d’in nan kowa na ta sai ya zama musulmi.
Takoma hannun ta Maman ta fizge da sauri”ke sakar min hannu mara jin magana kawai”kiyi hak’uri Mama na miki alk’awari bazan sake 6ata miki rai har kiji ciwon hakan ba Insha-ALLAH matuk’ar bai sa6a ma addinin musulunci ba.Tamata kallan uku ahu”Shari’a law” bata amsa ba tafara kuka haba Mama yanzu bazaki yafe min ba?Duk duniya bani da kamarki fa(In the whole wide world)
Takalleta cikin fushi”kin san da haka amma nace kar kiyi sallah sai kika gudu wajan Shedrak har kina min k’arya wai an ma Tina Operation?Tagirgiza kai”gaskiya ban yadda ba kin nuna min Shedrak ya fini.Ba haka bane Mama. Tasake galla mata harara”to yaya ne? Tamarairai ce”Mama tafiya ta Kaduna wajan Uncle da duk abubuwan da suka biyo baya”It’s a destiny (k’addara ce) suka kalli juna Sumayya tajijjiga kai “Ki yadda dani Mama wannan k’addara tace daban isa in kauce mata ba no matter how,kuma ai gwamma tawa tafiyar sau dubu tunda gashi na dawo a cikin hayyaci, koshin lafiya da kwanciyar hankali kuma kowa ya yaba,yayi sam barka to ai ko Alhamdulillah.
To amma Mama Judith fa…? Ran Maman yak’ara 6aci Sumayya tacigaba”Judith ta tafi amma bata dawo a cikin hayyaci, k’oshin lafiya da kwanciyar hankali ba, kuma kowa tirrr… Da allah wadarai yakeyi daganin ta, ba kuma wanda yakuma damuwa da ita sai ku.Ba aure tayi ba fornication shine sana’ar ta” which is forbiden”ba addinin daya yadda da hakan Islam ko Christianity sai dai san zuciya kawai,san zuciya kuwa 6acin ta yau ga Judit a ciki kuma Mama…ta tare ta dasauri ya isa haka Kasham jikinta yayi sanyi duk irin alwashin data d’auka ranar duk da sukayi ido hud’u da Kasham sai ta nemi shi tarasa,gaskiya Kasham tafad’a sai ta rungumeta”naya fe miki kome ALLAH ya albarkaci auran ki, wancan d’in shine Julaibib?Tagirgiza kai tana murmushi”ba shi bane.. Taba ta labarin duk abinda yafaru da ita bayan barin ta gida.
Tazuba mata idanu”to ni me zance miki Kasham? Sallah ne dai kin riga kin fara kuma ko na ce miki ki daina na san bazaki daina ba, kuma ma ban miki adalci ba,tunda duk a cikin Ya’yana dana haifa daga ke sai Rahab da Bitrus kune kawai masu jin magana, kune kuka maida hankali a karatu gashi nan kuma kune rayuwar ku tayi kyau,yanzu Bitrus shine personal manager a Bajju Community Bank(BCB) Rahab ta gama karatunta har ta fara aikin ta a asibiti, anjima kad’an za ta dawo gida tunda aikin rana wannan makon takeyi,ke kuma gashi kinyi aure hankalin ki akwance kuma kina cigaba da karatu.Rahab d’inma ta kusa yin aure.Sumayya tana ta godema Ubangiji daya sauk’ak’a kome fiye da zatan ta, tasaki jiki sunata hirar yaushe gamo suna kyalkyala dariya “Da da mahaifa sai ALLAH.