
A babban d’akin-shak’atawar gidan suka yi jam’in sallar su saboda k’auyan gaba d’aya ba masallaci tunda babu me sallah.Suna jam’in sallar Isha’i Rahab ta shigo da d’okin ganin Kasham dan tun a hanya tasamu labarin zuwan su, d’agowar su daga ruku’u Rahab ta tafi zata rungume ta Maman ta dakatar da ita”Ke Rahab karki ta6a ta baki ga sallah suke yiba?.Taja da baya da sauri”Oh Basakut”ta tuna idan suna sallah ko magana basa yi.Tajingina da bango tana kallansu”yadda suke tsayuwa,suyi ruku’u su d’ago, su tafi sujjada,su d’ago,su sake komawa sujjada suyi zaman tahiya har zuwa sallama kowa yafara karanta azkar d’in bayan kowace sallar farilla.
Cikin murmushi tajuya wajan Rahab. Rahab takama ha6a cikin mad’aukakin mamaki tayi tsalle ta rungumeta tana ihun murna Jesust Christ Halelujah”Kasham kece kika zama wata big madam?What a suprise, ta daki kafad’arta”tell me the secret.Sumayya tashafa wajan”gaskiya fa akwai zafi”suka kyalkyale da dariya.Rahab ai kema kin canja kinyi kud’i fa”mint note”suna shiga asusun ajiyar ki duk k’arshen wata suka saki juna. Rahab tasake binta da kallo daga sama har k’asa gaskiya canjawar da nayi ba irin wacce kika yi bace”wonderful”tashafa kyakkyawar fuskar ta data ke ta hasken musulunci da Imani”wannan irin kumatu da kika fara ajiyewa ga fari, ni dai ko shafa man sa fari kika fara ne?(bleaching)Ba Sumayya ba hatta sauran sai da sukayi dariya dajin yadda Rahab taketa kod’a ta.Tazauna suka gaisa d’aya bayan d’aya take tamabayar Sumayya sunayan su.Salim yabisu da kallo ga dukkan alamu suna san junan su suna da kirki dama Sumayya tafad’a mishi Maman suce kawai sai a hankali to itama bata nuna kome ba banda farin ciki da ganinsu.
Sumayya,Hafsa,Zainab da Rahab su suka gyarama Judith jiki da d’akin dayake ta k’arni kudaje sai budiri sukeyi,tana kwance cikin hawaye”wallahi da ace zan warke babu abinda zai hanani binku Kaduna in zama musulma.Hafsa ta amsa da sauri “ai ba dole sai a Kaduna ba, ko yanzu za ki iya k’ar6an musulunci.Wani dad’i yakama Sumayya.Ki yadda ki amince kina da rabo ne. Judith ko baki warke ba ALLAH zai kar6eki a haka Tagirgiza kai “uh uh ku kyaleni kawai dan bazan iya sallah ba tunda k’arfina ya riga ya k’are.Sumayya takalleta cikin natsuwa”ai addinin musulunci sauk’i gare shi Judit, ba dole sai a tsaye ko kina da k’arfi a gangar jiki za kiyi sallah ba matukar akwai lalura ko a yadda kike akwancen nan akwai yadda za kiyi sallah.
Rahab tagalla musu harara sannnan taja dogon tsaki”addinin ta’addancin kike sha’awa Judith?Tamik’e a zuciye zata bar d’akin Sumayya tarik’o hannunta.Rai a 6ace tace “malama sakarmin hannu kishiga hankalin ki fa.Tagyad’a kai sannan tasake kallan ta ckin natsuwa”to kiyi hak’uri kizauna magana za muyi Takoma ta zauna fuska a yamutse.Shiru ya ratsa d’akin na wucewar wasu dak’ik’u. Tad’ago kai a zuciye”bana san wawanci fa, ke nake sauraro kin kuma yi shiru.To ai naga ranki a6ace yake shi yasa nayi shiru har sai kin d’an huce karr in k’ara miki zafi.Tamik’a mata lemon biyar a raye(five alive)d’an jik’a mak’oshin ki mana.Kasham I’m I your toy to play with?Tayi yar dariya “absolutely no kiyi hak’uri, amma ina so ki sani addinin musulunci ba addinin ta’addanci bane,addinin sauk’i da salama nw ga mabiyanshi.Tawatsa hannaye “ahab…ba cinya ba k’afar baya”ko d’azuma abinda wani musulmin ku Adam yagama fad’a min kenan awajan aiki.Nidai banga dalilin da zai sa inyi sallah ba,ina da yanci bazan koma inda bani da wani yanciba.
Zainab ta tareta da sauri”ai ko addinin musulunci shine yabaki cikakken yanc me lasisi ma, musamman a matsayinki na ‘ya mace,kina da yanci kamar yadda namiji yake da yanci,sai dai mu addinin mu, duk da yancin daya k’wato mana ya nuna mana namiji shine a sama da mace,idan banda addinin musulunci wa yake girmama ‘ya mace ne?
Rumawa da suke kiran mace”Devil” shaid’aniya? Wai mace shaid’aniyace ana neman tsari da ita kamar yadda ake neman tsari da shaid’an.
Persia su kuma sun d’auki mace wulak’antacciya k’asa da duk wata halitta wulak’antacciya.
Yahudawa su kuma sun d’auki mace kamar baiwa,da zatai tama namiji hidima, ita kuma ba ta da wani hakki akan namiji
Zamanin jahiliyyar larabawa kuma idan aka haifi macen sai ma adinga zuwa maka jaje kai kuma kana 6uya,amata rik’on wulakanci,ko kuma tanaji tana gani da ranta da lafiyar ta a tona k’asa abinneta.
Wanne daga cikin wad’annan suka ba mace yan cinta?
To a duniyar musulunci da gidan musulunci ne kawai mace take yar ga ta,yar lele, sarauniya kome yi mata ake yi,kome kud’in ta k’wandala na ta na k’ashin kan ta sai ta ga dama za ta kashe.Duk masu yeekuwar yan cin mata indai ba wannan da addinin yabasu bane to wallahi k’arya ce,haushi suke ji, suna so ne ku fito ku sha wahala.
Rahab ta ta6e baki”ni kalaman naki duk a matsayin tazo muji ta tawuce ta bayan kunne na d’aukesu. Sumayya tagirgiza kai”ai ko sun wuce tazo muji ta tawuce ta bayan kunne wallahi.A baya dana ke kamar ke ina fad’in haka, amma a yanzu dana san hak’ik’anin musulunci ai na san k’arya ce. Rahab kije kiyi bincike ki ga ne menene addinin musulunci na gaskiya da abinda ya k’unsa,ba abinda kike ganin gama-garin musulmai suke aikatawa ba, ba abinda kike karantawa a mujallu da jaridu ba,ba abinda d’ai-d’ai kun mutane suke fasara musuluncin ba,kije kiyi karatu da bincke a cikin littafan musulunci,ki saurari preaching da luctures d’in malamai,ba abinda wasu gur6atattun musulmai da rashin ilmi ko san zuciya yake musu jagoranci ba.
Musulunci bai yadda da ta’addanci ba ko misqala zarratin,kuma duk wanda yake fakewa da musulunci to gaskiyar magana san zuciyar shi yabi… Rahab ta tari numfashin ta”za ki fad’i haka mana tunda kema kin zama musulma…”Eh zan fad’i haka dan na zama musulma na kuma san d’an abinda ALLAH yanufe ni da sani na daga ilmominshi.
Rahab barin baki misali Christianity bai yadda da shan giya da karuwanci ba,hakane? Rahab tagyada kai.Takalleta cikin natsuwa”to yanzu abinda Alhamdu da Judith suke yi sai ace addinin Christianity ne yace suyi?Sai taki magana. Sumayya ta d’an motsa kafad’a kin gani ko? To kamar haka addinin musulunci yake.Ki yadda kawai Rahab ki kar6i musulunci wallahi sai kinfi jin dad’in rayuwar ki.Ta ta6e baki tana hararar ta.
Sumayya tagyad’a kai tana murmushi “ALLAH kuwa gaskiya nake fad’a miki tabi hotunan d’akin da kallo kin gani,ko Jesus da Mary irin shigar musulunci suke yi a duk irin hotunan da zaki gani an za na su.Tajawo wata mujallar “Jehovah Witness”tana bud’e shafukan ciki Zainab da Hafsa kuzo kutaya ni gani a duk shafukan ciki kunga me”mini skirt da strap top kai ba d’ankwali? Suka kar6i mujallar suna dad’a gani,bayan sun gama dubawa Zainab tagirgiza kai”har shafin k’arshe ba bu,kowacce cikin mayalwacin kaya da lullu6i.Sumayya tace”to mazan fa”?Hafsa tace “suma suna cikin dogayan kaya ga gemu da k’asumba wasu ma har da rawani.Suka zuba ma Rahab idanu.Kingani ko?Wannnan shi yake nuna miki addinin gaskiya mukeyi”ai ko Annabi Isah Alaihissalam Jesus d’in musulmi ne.
Judith cikin hawaye tace”wallahi na yadda daku.Zainab takalleta cikin natsuwa” to ki kar6i musulunci mana.Tagirgiza kai”I seek repent from God and I know he will forgive me.Hafsa takad’a kai cikin damuwa.Sumayya tadafa kafad’arta karki 6ata ranki”dan shiriya ba ta wajan kowa face mahaliccin mu,shi yake shiryar da wanda yaso a lokacin daya so.Tajijjiga kai “wannan gaskiya ne Yaya Sumayya.Haka suka kwanta zuciyoyin su ba dad’i kowacce da irin tunanin ta musamman ganin yadda Judit tazama “k’ashi da rai.Ubangiji kamana kyakkyawar k’arshe.