GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

A sanda hantsi yadubi ludayi tana zaune a inda tayi sallar walha kiran Salim yashigo tad’aga tana dariya”Humm mijina na wa nakai na.Yataya darawa “Sumayya ta tawa ni kad’ai fito waje muyi hira.Yazuba mata idanu har ta zauna a gefen shi,tabi wajan da kallo “wai kana nufin anan zamu zauna?Mushiga gida mana.A ah gwamma muyi zaman mu anan,mu shak’i natural air, ta tacciya me kamshi kinga turawa sun mana wayo sai su tafi “Bar beach”suje su shak’i iska tatacciya dan jikin d’an Adam yana buk’atar hakan,wajan da ba hayaniya kayi refreshing d’in gangar jiki, zuciyar ka da k’wak’walwarka.

Nayi kewarki fa.Tabud’e idanun ta data rufesu tamishi wani kallan k’auna me cike da shauk’i”nima haka”sai sukayi dariya.

Salim…

Takira shi a hankali. Yakalleta… Tagyad’a kai”samun masoyi na gaskiya shine buk’atar kowani d’an Adam,masoyi me amana, masoyi me girmama abinda masoyin shi yake so matuk’ar ba sa6on ALLAH bane,masoyi me k’ok’ari da jikinshi,da kalaman shi, da aljihun shi, da lokacin shi wajan ganin masoyin shi ya samu abinda yake san samu”Godiya ta tabbata ga Ubangijin mu a kowani hali da yanayi. Wallahi ba ka da abokin tarayya a irin k’auna da soyayyar danake maka.Yayi Murmushin jin dad’i”Ina alfahari dake nagode Ubangijin mu daya mallaka min ke a matsayin mata”Sumayya ALLAH yamiki albarka ya lull6emin ke da rahamar shi.Kwanan su hud’u suka musu sallama suka koma Kaduna garin gwamna.

Yau da gobe karyar ALLAH kome gudun ka sai ta ka mo ka.
Tsufa labari…mutuwa k’arar kwana.

18 Jumaada Awwal 1441
13 January 2020

We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta’in

…GWAJIN DAFI????

Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)

Shafi na goma sha hud’u

Zaman su lafiya cikin girmama juna. A yanzu fatansu bai wuce ganin Sumayya ta sauka lafiya ba.Tana kwance a doguwar kujera da yammacin tana ta nazarce-nazarcenta,tsohon cikin bai hana ta yin wasu abubuwan ba,taji muryar Mamanta.Wayyo!Zama dak’yar ta shi da dabara kafin ma tayi yunk’urin ta shi ita ta shigo.

“Oyoyo Mama sannu da zuwa…

Da har na cire rai da zuwan ki. Taje ta d’auko ruwa da kanta tasha”Haba Kasham ya za ayi in k’i zuwa, bayan ni nace miki zan zo,kin san yanayin taran na mune yanzu haka ma sun tafi, ni a motar haya zan koma gida.Tabita da kallan tausayi”Sannu Kasham ALLAH yasauke ki lafiya, kwanaki ina ta mafarki wai kin haifi ‘yan biyu. Tad’anyi murmushi kawai suka cigaba da hira.

Wannan karan bazan bar Kaduna ba har sai kin kaini gidan Shedrak.Tagyad’a kai”to Mama”takira Salim a waya dan baya gari.

“An ya Sumayya zan barki kifita kuwa? Ba likita ta ce banda yawan zirga-zirga ba?”Na sani kuma ban manta ba,dama Yaya Miqdad zan kira a waya yazo yad’auke mu.To idan baya kusa ko yana wani uzirin na shi baza ki takura mishi ba?”karka damu ai ta mu dashi bata 6aci,zan nemi alfarma na kuma san za a min.To shikenan ALLAH yatsare,kiyi zaman ki acan,nima Insha-ALLAH zuwa bayan Isha’i zan shigo sai inzo in d’auke ki.To nagode”ALLAH yak’ara tsare hanya yadawo mana da kai lafiya.Amin Sumayya nima nagode.

Makonni biyu da tafiyar Maman ta haifi kyakkyawar ‘yar ta sunyi murna sosai dan ba a samu tangard’an kome ba,ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Salim d’in da tadad’e da rasuwa Ruqayya suna kiranta da Ummi.Gidan Alhaji Hafiz takoma Maman Hasan tana kula dasu yadda yakama ta,jegon ya kar6esu dan sunyi shar dasu saboda cimar abincin me amfani me gina jiki da k’ara kuzari ai shine jego “Abincin ka lafiyar ka…

Cikin wani dare tana tsaka da bacci kiran Mama yashigo tad’aga cikin fargaban abinda kunnuwan ta za suji dan ta san tabbass ba lafiya ba.Kasham Judith ta mutu tafad’a tana kuka “lallai soyayyar d’a da mahaifa sai ALLAH”kalli irin wahalar data basu amma Maman take wannan kukan?Itama mutuwar tadake ta,duk da sun san k’arshen alewa k’asa.To amma ai ba yadda za suyi dan mutuwa dole ce ko mutum ya yadda ko bai yadda ba idan ajali yazo to fa silke baya tarewa, Kukan mutuwa kuma ba ya dawo da matacce.

Babu addu’a tsakanin musulmi da kafiri dan haka sai tashiga rarrashinta da kalamai masu dad’i har tasa mu tayi shiru”nagode, ALLAH yamiki albarka bawanda yakwantar min da hankali sai ke”To za kuzo funeral service d’in ne?A ah Mama ba wanda zai zo kuyi abinku,amma Insha-ALLAH idan mukayi arba’in za muzo ai.Shikenan sai da safe takatse wayar.Tun daga nan har garin ALLAH j’arasa wayewa Sumayya bata kuma rintsawa ba,sai juye-juye take tayi da tunani barkatai daya cika k’wak’walwarta.

Suna hirar su da Hafsa a d’akin-shak’atawa sukaji sallama tare da k’wank’wasa k’ofa.Hafsa tabud’e k’ofar tana amsa sallamar. Yana tsaye tad’anyi murmushi”au kaine tabashi hanya bismillah shigo “cikin ladabi yadurk’usa har k’asa yana gaishe da Sumayya.Tagirgiza kai” tana nuna mishi kujera”ta shi ka zauna meye na durk’usan? Bai zauna a kujeran ba sai yayi zaman shi a carpet d’in yana d’an murmushi”ai nan d’in ma yayi.Mamana bata nan ne?Hafsa tayi yar dariya “Aikuwa dai Maman Hasan yau tayi nisan kiwo tana can wajan tsoho me ran k’arfe Malam Muhammad Aminu.

Alhassan d’aya daga cikin yaran da suke zama ma Salim a kasuwa ne, yaro ne me hankali da sanin ya kamata,tunda yaji sunan Maman Hassan shikenan yake ce mata Mamanshi, shi kuma Usainar shi ta rasu tun suna k’anana. Itama Maman Hassan tana yi dashi sosai indai yazo tana gida to sai ta san abinda tabashi kome k’ank’antar shi, tun yana jin nauyi baya kar6a har ya saba dan takance”Kai Alhassan anya wannan Mamana da kake kirana ba a fatar baki kawai ya tsaya ba? Uwa ta ta6a ba d’anta abu yaki kar6a? Tun daga nan yaba ta hak’uri idan tabashi sai yasa hannu biyu yakar6a yayi godiya.

Ya ajiye ledar hannun shi a gaban Sumayya”Alhaji ne yace in kawo.Wai ya kira layinki ya k’i shiga,sai bayan la’asar zai shigo.Bakome Alhassan,nima ina ta kiran shi bata shiga akwai matsalar sadarwa yau”kace ina gaisuwa sai ya zo d’in”Yamik'”Zai ji”yad’an kalli Hafsa “idan Mamana ta dawo nima amik’a min sak’on gaisuwa zan dawo ranar Juma’a musamman dan in gaishe ta.Tagyad’a kai” tam za taji”sukayi sallama.

Tana gama wanka suka tafi Zonkwa ita da Hafsa sun sauka lafiya kowa yayi murnan ganin su.Kwanan su biyar da tafiya da yammacin ranar sai kawai ganin Salim suka yi.Takalleshi cikin kulawa da mamaki”ba ranar Alhamis mukayi da kai za kazo ba?Yamayar da kanshi jikin kujerar”ranar alhamis ne amma na ka sa daurewa ne,amma yanzu ai hankali na ya d’an kwanta danazo na ganku”gobe kenan za ka koma? Yabud’e idanun shi daya fara rufewa yakalle ta da sauri”wai kina nufin tafiya zanyi in barku? Tagyad’a kai”haka nake nufi ga waya muna magana da juna.Yad’an harareta”kina wasa ne ko?Wani irin wasa kuma?Ai naga kwana goma kaba mu to yau munyi biyar ba saura biyar ba?

“Sumayya…

Yakirata…suka zubama juna idanu na wucewar wasu dak’ik’u yasauke numfashi yasa hannu yana yata6a kirjinshi dai-dai saitin zuciya “kina so na kuwa? Takalleshi baki a bud’e saboda mamakin furucin shi”haba Baban Ummi me yasa za kamin irin wannan tambayar?Yad’ora hannayan shi a saman tebur “saboda kince gobe zan tafi ma’ana ni kad’ai? Sumayya akwai ayyuka masu yawa agabana amma naturesu gefe duk da mahimman cinsu naza6i zuwa wajanki,sai dai kash…hak’ata baza ta tadda ruwa ba, dan na ga kina so ki watsamin k’asa a cikin idanu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button