
Sumayya…!Yakira sunanta da k’arfi yata6a kirjinta difff…Numfashi baya shiga da fita…Sumayya! Yad’aga hannun ta na dama yarafff…yafad’i a kan katifa.Abubuwa da yawa suka yamutsa k’wak’walwar shi bangaran tunani sai yaji ruguzowar wani abu a k’ahon zuciyar shi da k’arfin gaske Dammm…!!!
Ta mutu…!Sumayya ta mutu…?!!!
Sai yafara k’arya ta zuciyar shi dan idanun sun fara mishi gizo sun nuna mishi ga tanan tana numfashin ta”Sumayya au dama baki mutu ba? Yasake kallanta idanun ta a k’ak’k’afe ruwan ciki yak’ame k’amas suna kallan sama tayi tsawo da wani irin kyau na ban mamaki shi bai ta6a ganin wannan kyan ba ko lokacin da take ganiyar lafiyar ta take kwalliya da gayu…bai san awani yanayi yake ba har sai da aka kirashi a waya.
Miqdad ne yake tambayar shi lafiya kuwa ban ganka a masallaci sallar asubahi ba,ko jikin Sumayyan ne?Asanyaye yace”Sumayya ta mutu.Cikin k’araji Miqdad ya sake tambayar shi”ta mutu? Yaushe?Wasu irin hawaye masu d’umi suka zubo mishi sharrr…sai kawai ya katse wayar yakifa kanshi a kusa da fuskar ta, ya rasa abinda yake mishi dad’i sai yafara Istirja’i…Miqdad shi yaje gida yad’auko su Alhaji Hafiz suka d’unguma gaba d’ayansu zuwa gidan hankali a tashe.Amma Salim yayi dauriya dan shi yamata wanka yashirya ta tsab aka mata sallah aka d’auketa a makara sai makwancinta na gaskiya kabari d’aki a cikin kasa”Uh uhun duniya rumfar kara…Wata rana zai fad’i.ALLAH yajikanki Sumayya yasa k’arshen wahalar kenan!
Lokaci d’aya Salim yayi wata rin rama kamar wanda ya shekara yana jinya.A ranar Iyayanta suka zo.Maman tana kuka ta rungume Ummi tana sambatu “Holy Jesus why? Why? Me yasa Kasham za ta mutu yanzu? Me yasa za ka bari a kashe min yarinya…To wallahi bazan ta6a yafewa ba…me Kasham ta tare muku ne?
Alhaji Hafiz ya k’araso wajan da sauri “haba Dinatu ya kike irin wannna kalaman ne? Mutane fa za suyi zatan kasheta akayi.To dama ba kasheta akayi ba? Kaima ai ka sani ko har ka manta tunda ba ‘yar ka bace? Yakad’a kai cikin damuwa”ko na sani a yanzu dai na manta,mudai a addininmu na musulunci duk wanda yamutu to tabbaci hak’ik’a kwananshine kawai yak’are, amma ba mayune suka kashe shiba “ai sara da sassak’a basa hana gamji toho…a ah Shedrak wallahi Kasham dai kashe min ita akayi, ba ta zo sun ganta cikin rufin asiri ba?Takuma yin kururuwa cikin tafasar zuciya”Wai…Wayyoh…ALLAH!!! Kasham ta mutu…Judith ta mutu…oh Jesus Christ of Nazareth!
Shedrak!
Tazuba mishi jajayan idanun ta da suka rine da 6acin rai tadad’a rungume Ummi”bazan yafe ba. Yagyad’a kai”to naji amma dan ALLAH kiyi hak’uri da kukan nan muje ga abincin ku can kije ki k’arya.Bana ci, tasa gefen zaninta tana share hawaye da majina an kashe min Kasham an bar min grandchild cikin maraici… For God sake Shedrak Ummi guda nawa take da zata iya d’aukar wannan tashin hankalin?
Yakalli Ummin”tabbass Ummi ba ta san kome ba,bata ma san me ake kira da mutuwa ba bare har yatashi hankalin ta,guda nawa take?Ko shekara uku batayi ba to amma ya za suyi da hukuncin ALLAH?Yadda duk yaso haka yake zartar da hukuncin shi”idan yaso yafitar da rayayye daga jikin matacce,idan yaso yafitar da matacce daga cikin rayayye”Qaadiran alaa manyasha’u.Dak’yar yasamu ta yi shiru da wannan sambatun da take tayi cikin kuka da d’aga murya.
Makon su d’aya sukayi shirin komawa k’auyansu Madauci,Maman ta so k’warai abata Ummi ta tafi da ita amma Salim da Alhaji Hafiz suka bata hak’uri akan hakan bazai yiwuba kasancewar addini ba d’aya ba.Salim ma yasake ba ta hak’uri tare da alk’awarin kawo musu Ummi lokaci zuwa lokaci suna ganin juna.
“Mutuwa ba ta zama masifa ga mumini,mutuwa hutuce ga wanda yadace da kyakkyawar makoma…ALLAH ba yana nufin 6atama bawa bane dan ya d’auki wani bangare najin dad’in shi Iyaye, mata, miji,Ya’ya da yan’uwa.. Alhaji Hafiz yadafa kafad’arshi “Salim…na san kai namiji jarumi ne,to na rok’eka da girman ALLAH kayi hak’uri kaga yadda kazama kuwa a yan kwana kin nan? Sumayya ta riga ta tafi rayuwarta ta doron duniya ta riga ta k’are,ba abinda take buk’ata awajan mu yanzu sama da addu’a…Addu’a itace abincin mumini…to mu yawaita aika mata dashi.Kaima ka natsuwa kacigaba da zuwa kasuwa ALLAH yabaka macen albarka.Yahad’iye wani abu me d’aci dak’yar yayi furucin” nagode Alhaji ALLAH yak’ara girma…
Ummi tana gidan Alhaji Hafiz dan shi yanemi wannan alfarmar,amma Salim ya dai basu ita dan kawai sun cika mishi idanu ne,saboda yadda yake sintiri ba dare ba rana.Suna hira a d’akin-shak’atawa zuwan shi gidan a aranar karo na uku kenan.Alhaji Hafiz yakalleshi cikin natsuwa “Salim kayi aure mana.Yad’an yi murmushi kawai. Kayi shiru bakace kome ba?Alhaji ba auran ne bana so ba, tunani nakeyi anya zan samu mace kamar Sumayya?Wani irin zama mukayi me cike da amana, me cike da girmama juna,zan samu macen daza ta rik’e min Ummi da amana? Yagyad’a kai”me zai hana Salim?Kai da can abaya ka san za kuyi irin wannan zaman da Sumayya?To karka cire tsammani daga al’amarin Ubangiji mana.jikinshi yayi sanyi wannan gaskiya”nagode Alhaji ALLAH yak’ara girma.
Ummi ta shigo da gudunta dan taji muryarshi”Abba na baka tafi ba?Uh ban tafi ba.Tayi dariya”to muje ka kaini Galaxy…in kira Yaya Zuhair mutafi tare?Yakalleta da kulawa “Ummi baza muje Galaxy ba, lokacin makaranta ya kusa,baza mu sake zuwaba sai an bada hutu kinji ko?Ta6ata fuska sai kawai tajuya tayi tafiyar ta, kwallah sun cika idanun ta.Suka bita da kallo har tafice.
Me yasa kayi haka Salim?Dama taku da Ummi zata 6aci?Lallai yau na ganku a rana.Yad’an yi murmushi”ai ba duk abinda take so nake biye mata ba,wani lokacin ko akwai abin ina hanata saboda ta taso cikin sanin ba ko me da mutum yake so a rayuwa yake samu ba, ko da kuwa yana ganin abin baifi karfin shiba, kauna da soyayyar dana ke ma Ummi ba makauniya bace…
Lokaci k’ank’ani Salim suka dai-daita da ‘yar limamin unguwarsu aka daura musu aure,shima sai ya samu sauk’in zirga-zirga tsakanin gidanshi dana Alhaji Hafiz saboda Ummi.Mariya tana kula mishi da Ummi gwargwadan ikon ta, shima ya yaba da hakan sai suka samu kwanciyar hankali dan kowa yana yaba k’ok’arin dan’uwanshi,sai tak’ara bada himma tana mata rik’on tsakani da ALLAH kamar yadda zata rik’e Ya’yan cikinta”yaba kyauta tukwuici.
Yana sanye da wandon chinos ruwan zinare sai riga me dogon hannu da ratsin ruwan zinari da bak’i,kwantaccen bak’in gashin kanshi yanata k’yallin hair fruits,k’amshin Arabian perfume d’inshi ya cika d’akin. Alk’asim da suke abokan wasa tawajan uba yashigo yana kallanshi “Lallai mutumin nan kana jin dad’in ka, kaga yadda kazama wani d’an matashin bak’in bature kuwa? Yabashi hannu suka yi musafaha.To ya karatun? Alhamdulillahi ai ya zo k’arshe tunda na gama rubuta Project d’ina.Ah lallai sai shirin tafiya bautar k’asa to Ubangiji yasa aje a sa a.Amin nagode. Yad’auki remote yana canja tasha baya san labaran CNN d’in nan,yan kanzagin Amurka (America)kanwa uwar gami ce,da yad’a propagandar k’arya akan addinin musulunci da musulmai.Yacire wayar shi da yasa a caji ta cika,suka fita zuwa gidan Hajiya sai dai gidan na ta da kwado sai sukayi zamansu a dakalin k’ofar gidan suna hira.
Aminu yak’araso yana kallan Julaibib cikin raha yace”hey dude what’s up?Yagalla mishi harara “Amincin ALAH zaka rok’amana ba wannan ba..yatare shi cikin dariya”kar ka wani harareni kai kayi shiga irin ta su ai dole in maka irin al’adarsu,shima yazauna sannan yamik’a musu hannu sukayi musafaha.