
Magana take mishi amma yayi kamar ALLAH baiyi ruwan tsiran taba,ganin haka yasa tayi saurin k’arasawa bakin k’ofar da zai fita ta tare hanya sai yaja yatsaya.
Please…Julaibib…
Magana nake so muyi please…tahad’a tafukan hannayenta alamar magiya.”please Julaibib, wallahi with all my heart ina sanka,kana burgeni, me zai hana ka aureni?
Yagirgiza kai”Bazan iyaba.Idanun ta suka ciko da k’walla”wai kai wannan amsar ta “Bazan iyaba”bazata bar bakinka bane d’ansarai? Wai me zan yine da zaka so ni Julaibib?Yakalli agogon dake d’aure a hannunshi nadama tana 6ata mishi lokaci fa.
Ki matsa zan wuce.Tasake kallanshi “Julaibib zanyi sallah fa…yad’ago yana mata rikitaccen kallanshi “Ki bani hanya nace ko? Yafurta hakan da 6acin rai a fuskarshi.
Yamata wani irin kwarjini data kasa aiwatar da k’udurin zuciyarta.Sai tagyad’a kai ta kuma matsawa a kofar”shi kenan zo ka wuce.Ya ra6a ta gefenta kamar wanda akace idan ya ta6ata ya gama amfani a doron duniya.
Tabi bayanshi da kallo har ya6ace ma ganinta…sai tayi d’an yak’e mak’alallun k’wallan cikin idanunta suka samu damar d’igowa a kyakkyawar fuskarta, sai kuma wani sanyi-sanyi data faraji, tsigar jikinta yana tashi alamar zazza7i yana so yakawo mata ziyara.
Harshenka zakinka idan kasa keshi yacin yeka”…
11 Rabi’a Thani 1441
8 December 2019
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2 geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in.
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Shafi na biyu.
Musaddiq yashigo da sallama, yad’auki ya zauna yasha,sannanya kalli Julaibib “sak’o aka bani wajanka…sai kuma yaja yayi shiru. Yad’an d’ago ya kalleshi”Uhun ina jinka sak’on me? Yaciro d’an k’aramin kati launin ruwan k’asa yanata kyal-kyali yamik’a mishi “karanta kagani.Kasham ce take gayyatar su party dan murnar zagayowar ranar da aka haifeta(Birthday) ranar talata a Bigard Hotel.
Yad’ago yana mishi wani rikitaccen kallo “nasha fad’a maka yarinyar nan ta daina aiko ka wajena kana zuwa kana fad’amin ko?Ya jijjiga kai”to ba laifi ka cigaba amma abinda zan maka zaka sha mamakinshi wa…bai bari ya k’arasa ba shima yatareshi”ba laifinka bane nawane ainan d’in tace za tazo tasame ka da kanta, ni kuma sanin da nayi baka san hakan yasa nace mata ka tafi Matsirga amma takawo in ajiye maka da…shima Julaibib ya tare da sauri…”na tafi Matsirga,na tafi Matsirga fa kace?To saboda me zaka min k’arya?Ganin ranshi ya 6aci yace”kayi hak’uri d’ansarai.Baice komai ba yakoma yakwanta,duk sukayi shiru,zuwa can Musaddiq yasake kallanshi.”Kasham da gaske tana sanka Julaibib, ko zamu d’an lek’a matane ko na rabin awa dan itama taji dad’i yaba kyauta tukwuici.Yagalla mishi harara”idan zakaje to ni ina ruwana?Musaddiq yayi murmushi”d’ansarai autan Inna me duniya.Inje kuma?To ni asuwa?Kare da gudun laiya?Da dai zakaje dana maka kara na rakaka.
Yamik’e ni ga ka tafiya ta wajan Safiyya,yamik’a mishi hannu sukayi musafaha”Ka gaisheta.Musaddiq yad’an zaro idanu dan mamaki “Wuuu yau wace rana Julaibib yaji zanje wajan masoyiyata yace agaisheta? Julaibib yamik’e zaune da sauri,yana k’ok’arin kai mishi naushi yagoce yana dariya, ah ka ga mugu da 6allallan kafad’a kake so inji hirar”uu tambayata kakeyi?To tsaya yanzu zaka gani ya yunk’ura zai mik’e Musaddiq yafito daga d’akin da gudu yana fad’in “mu had’u a gidan Hajiya bayan sallar la’asar”.
Agajiye yashigo gidan,dawowar shi kenan daga Kaduna.Yaya Karima ta tareshi “oyoyo barka da dawowa.Yauwa Yaya Karima.Yacire takalman shi masu rufi,sannan ya zauna a tabarmar tsakar gidan suna gaisawa.Inna tafito daga d’akin-girki”lale d’ansarai autan Innar shi”sukayi dariya to gashi,ruwa tabashi a k’aramin kwanan sha.
Yakar6a”nagode Inna.Da bismillah yafara shan ruwan,ruwan randan Inna me dad’in gaske ga wani irin sanyi,kowa kuma ya san ruwan randa sanyin shi baya cutarwa,ga k’amshin saiwoyin da take sawa a ciki da suke k’arama ruwan armashi wajan sha.Kad’an yarage sannan ya ajiye kwanan cikin hamdala ga ALLAH.Yakalle ta”Inna ruwan randarki gard’i da d’and’anonshi har yafi ruwan roba Swan.Sukayi dariya.
Abdullahi babban d’an Yaya Karima yayi sallama ya shigo yana rik’e da hannun k’anwarshi Kamila da take kuka.”Mama ga tanan tak’iyin shiru tunda ta dawo daga makaranta,wai me yasa baki bari an taso suba kikayi tahowarki.?Ya k’arasa wajan Kawunshi cikin murna “Kawu sannu da zuwa,sannan ya gaisheshi.Yarik’o hannunshi “Yauwa Abdul yakaratu?Ya d’ibo Inibi to ga tsarabar ka.Abdul yasa hannu biyu yakar6a”nagode Kawu ALLAH amfana.
Karima takalleshi kwana biyu ka daina zumunci sai Musaddiq kad’ai yake sadar da ita.”Baban Abdul dai yagaji shine yace in biyo sawu ko mun maka laifine”?Yayi murmushi yana shafa kai”Yaya Karima ba kumun laifi ba,bana samun lokacine amma Insha-ALLAH wannan Juma’ar zan shigo kin san tsarin karatunmu ba d’aya bane.Ta gyad’a kai”hakane Ubangiji yanuna mana Juma’ar.Ya amsa da amin.
Wata magana zamuyi.Sai ya tattara hankalin shi ga sauraran abinda zata fad’a.”Julaibib me zai hana kafito da yarinyar da kake so a had’a bikinka dana Musaddiq?Ina sha’awa k’warai ace yadda kuke kome tare to lokacin aure ma ku angwance tare.Yagirgiza kai”ni bani da budurwa ma, ki tayani addu’a ALLAH yakawo tagari.To amin. Amma duk yan matan Gidan-Waya ba wacce ka k’yasa?Yad’anyi tsaki’ni fa ba tsayawa kallansu nake yiba,abinda yarabani daku,yakaini can d’in shi nakeyi (karatu)
Musaddiq yashigo yatarar da zancen, yace tab shi autan Inna sai a hankali kuma gashi da farin jini a wajan yan matan amma kowacce sai yace bata da kamun kai,bayan shi kanshi ya sani a shari’ance ba haramun bane dan mace ta yaba da kai tafurta maka kalmar k’auna.Musaddiq yaja dogon tsaki yana hararar Julaibib saboda tuno abinda yata 6ama yar course d’insu…..
Atikah Aliyu Kagoro.
Jikar Sarkin Kagoro ce tana da hankali da natsuwa kuma k’wak’walwannar dai Ubangiji ya hore mata shi na fahimtar karatu,Malamai ma ji da ita sukeyi bari d’alibai yan karankad’a miya.Tunda taga Julaibib tace nan duniya ba wanda yamata da aure kamarshi.sai dai kashhh…yawatsa mata k’asa a idanu.Atikah Aliyu Kagoro tayi kukan rashin shi.
Rannan tazo wajan Julaibib d’in amma bata same shiba sai Musaddiq shine take fad’a mishi zata bar makarantar saboda ba zata iya cigaba da ganin Julaibib ba bayan yace baya ra’ayinta,ita tanaso yasota da zuciyarshi ne ba yaso ta dan an tursasa shi an mishi dole ba,amma badan haka ba tana kai maganar nan wajan Me Martaba to anyi angama maye ya auri ramammiya, Julaibib zai zama mijinta dan bai isa Sarki yabashi auren jikarshi yace baya so ba”ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya”tad’ibo wasu damin sababbin kud’i tabashi,ya girgiza kai ki barshi kawai.Sai tad’an harereshi “kai karfa ka 6atamin rai dan ka san kai ba Julaibib bane,dogarai zansa su baka na jaki”.Sukayi dariya.Yagyad’a kai”wannan gaskiya ne ranki yadad’e.
Ta sake mik’a mishi”To d’an ALLAH ka kar6a.Yasa hannu biyu ya kar6a yamata godiya, sannan ya d’an kalleta”yanzu Atikah kin bar karatunki kenan?Tagirgiza kai”zan koma wajan Mahaifina a Saudi-arabia,dama tun daga yaye zamana ya d’ore anan,bayan na gama Secondary d’ina yaso k’warai in koma can in cigaba da karatu amma nace nafi san nan,ba dan ya so ba yahak’ura,saboda ni tagaban goshin Me Martaba ce,abinda nake so to dole kowa ma yahak’ura yasoshi indai yana neman zaman lafiya dashi.