
Suna ta hira amma ya dai na jin abinda suka fad’a tunda ya hangota”indai yana gari to ranakun k’arshen mako irin haka yana ganinta.A natse take tafiya irin ta ‘ya macen data san abinda take yi wato gefen hanya, yanata kallanta har tasha kwana.Wani murmushi yasu6uce mishi”Yarinyar can ya yaba da hankali da natsuwar ta.Aminu yayi yar dariya”Dan Sarai kenan biri yayi kama da mutum fa…na rantse maka ALLAH da zafi-zafi ake dukan k’arfe idan katsaya kallan ruwa…irin na Aisha to ko ba abinda zai hana kwad’o yamaka k’afa. Yajijjiga kai “tabbass zancen ka dutse…
Washe gari lahadi yakafa ya tsare sha d’aya da rabi yabar Musaddiq a shago yaje dakalin wajan yazauna yana fatan ganinta,dai-dai lokacin aka ta shi daga Islamiyar su,wucewar wasu yan dak’ik’u sai ko gata ta zo zata wuce,yabita da kallo tana sanye da dogon hijab me hannu ruwan sararin samaniya kafad’arta rataye da bak’ar jaka.
“Assalamu alaikum…
Karo na biyu kenan yamata sallamar.Dafarko tayi tsammanin ba da ita yake yiba shi yasa tayi shiru, sai da yasake maimaitawa,a hankali tad’an juyo ta kalleshi sannan ta amsa.Da sauri yamik’e daga dakalin ganin ta juya taciga da tafiyarta… “am… Dan ALLAH…Jimana.Tatsaya ba tare data juyo ba tana jiran abinda zai fad’a.Yayi k’asa da murya “kinga yanzu sauran d’aliban za su firfito kuma kamar zamu takura musu idan muka tsaya anan, ko zamu d’an matsa daga can bakin Library? Batace kome ba suka k’arasa wajan yad’an jingina da k’arfen allan bayani(signboard)d’in yana kallanta ta sunkwui da kai.
Ya Ilahi…sai yarasa abinda zai fad’a ta mishi arwa.Wucewar wasu dakk’ik’u tad’ago kai ta kalleshi cikin natsuwa dan shirun yayi yawa “Malam lafiya?Yad’an sosa kunne”Kiyi hak’uri da na san gidan da kike bazan tsaida ke a hanya ba,can d’in zan biyo ki dan kambamawar data dace dake kenan”Dan ALLAH ina ne gidan ku?Tagirgiza kai”ni ba yar garin nan bace karatu nake yi a Nursing School a cikin makaranta nake zama.
Ayyah…to ya muka ji da shan geron Sunday?(garin kwaki/rogo)yadda yayi furucin cikin jimami yasa tad’anyi murmushi”har da kai? Yagyad’a kai”eh ai duk kanwar ja ce,nima d’alibi ne gobe war haka ai na tsufa a makaranta.Atakaice yamata bayanin kanshi itama haka da garin data fito.
Adai-dai lokacin suka shawo kwana dawowar su daga makarantar allo kenan.Juyowar dazaiyi dan sunyi sallama da Bilkisu caraf idanun su yahad’u dana Sudaida”wani irin yanayi mara dad’i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta, tagalla mishi harara sannna takauda kai,cikin fushi tayi gaba su Khausar suka tsaya gaisawa suna d’an tsokanar shi”a k’ofar gidansu Nasmat tatsaya dan allanta yana hannun Nasmat d’inne kuma rubutu za tayi da wallahi bata tsaya ba”Khausar takalleta “to ke wai saurin meye haka kike yi?Sauri kuma ba wajan zuwa ba tunda gashi dole ta tsaya jiranmu.Tamusu wani malalacin kallo”shiru ma amsace.Nasmat tacigaba”anya waccan ba budurwar d’ansarai bace?Cikin tafasar zuciya ta fizge allanta”kya tambayi kaza hanyar rafi…?Fuuu tayi gaba tana k’unk’uni.Suka bita da kallan mamaki cikin tunanin abinda ya caza mata k’wak’walwa haka.Nasmat tad’an motsa kafad’a “wallahi can da yawarki yarinya.
Tun daga ranar d’ansarai bai kuma yadda sun had’u da Bilkisu a kwanakin k’arshen mako ba. Ranar wata Juma’a yayi shigarshi ta fararan kaya yad’auki motarshi sai Matsirga anan yayi sallar Juma’a.Yana fitowa daga masallaci yadinga bin kwatancen Bilkisu kasancewar shi ba bak’o bane a garin sai ko gashi a k’ofar gidan.Wani dogon dattijo kyakkyawan farin Bafulani yahango, shi da wani da bai k’arasa shi a tsufa ba suna magana, sun dad’e suna maganganunsu sannan sukayi sallama.
Julaibib yatare shi cikin sallama…
Malam Lamid’o ya amsa sallamar yana mik’a ma Julaibib hannu dan suyi musafaha amma ya nok’e a haka ya gaishe shi cikin girmamawa.Malam Lamid’o sai ya yaba da natsuwarshi yayi murmushi”samari daga ina? Cikin ladabi ya amsa”Baba ni bak’on kune. Yagyad’a kai yana kara nazarinshi”af to,to madallah sannu da zuwa to bismillah shigo ciki,yabud’e mishi d’akin zauran suka shiga yanuna mishi wajan zama”zauna ina zuwa”yajuya zuwa cikin gidan sai gashi ya dawo da damammiyar fura da nono tasha zuma da ruwan sha “bismillah samari”to Baba nagode”yajuya yasake fita dan yabashi waje. Wucewar dak’ik’u talatin yasake shigowa lokacin Julaibib yad’an sha fura dan baya wani jin yunwa.
“Samari daga ina kake?
Julaibib Abdullahi d’ansarai…
Shine cikakken sunana daga Zonkwa nake.
Yabashi labarin kome game da had’uwarsu da Bilkisu…Ita kanta ba ta san zanzo nan ba.Ni nazo wajan kane Baba indai bakama Bilkisu miji ba to idan ka amince zan turo maka manyana.Yamishi kallan nazari” yanzu misali idan na amince ita kuma Bilkisu bata amince dakai amatsayin miji ba fa?Yad’anyi jimmm…sannan yad’ago cikin natsuwa yakalleshi “bazanji dad’i ba amma bazan ji haushi ba ,dan na san kome na rayuwar bawa yana rubuce ne,yana kuma tafiya daki-dakine kamar yadda numfashi yake shiga da fita ajikin d’an Adam,zan mana addu’a ni da ita Ubangiji yahad’amu da abokan zama na arzik’i.
Malam Lamid’o yabishi da kallo cikin zancen zuci”wannan d’an matashin tun yanzu yana da halin dattako to inaga ya dad’a girma,ilmi yadad’a cika k’wak’walwarshi? Julaibib idan har Bilkisu ta amince da kai to nima na amince dakai dan ni bazan ma Bilkisu auran dole ba sai wanda ta yadda tana so dan haka,kaje na yadda ka nemi soyayyar ta. Irinka nake ma Bilkisu sha’awa kasancewar ta me d’an ilmi duk da bai taka kara ya karya ba,to amma na san idan tazama matarka za ka ciyar da ita gaba,ta inda taka sa zaka taimaka mata har itama ta tsaya da kafafunta wata rana.
Nayi karatun addini dana zamani dai-dai gwargwado,shi yasa na hana Jauro auran ta saboda ba abinda ya iya ba abinda yasani sai kiwon shanu,ni na san illar zama da jahili dan bazai amfanar da ita da kome ba,d’an abinda tasani d’in ma idan ba tsananin raboba a haka zai k’are.Katuro min manyanka za muyi magana gemu da gemu.Ubangiji yasa Bilkisu rabonka ce.Yasunkwui da kai yana murmushi labarin zuciya a tambayi fuska.
Tana goge kayan sawanta abokiyar karatunta tazo mata da sak’on daya bata mamaki”Julaibib kikace yana nema na?Eh ai kibar wani mamaki dan ga kai ga k’afa ai ba tambayar me aka yanka, jeki wajan da ake ajiye abubuwan hawa za ki ganshi ganin idanunki.
Dogon hijab me hannu ruwan k’asa tasa, yana hangota yafito daga cikin motar.
“Bilkisu me gadon zinare…
Tagaishe shi cikin natsuwa.Ya amsa yana murmushi”Yau dai gani ALLAH ya nufeni da zuwa a wannan yammacin,da zan bari sai gobe to amma dana tuna yaufa Juma’atu babbar rana ce sai kawai nace barin dai k’araso in k’ar6i goron juma’a ta kawai.Tad’anyi murmushi “goron juma’a kake so? Ai ko ka tara ka samu sai ta mik’a mishi lemon Schweppes d’in hannun ta.Yasa hannu biyu yakar6a “wannan kyautar goron juma’ar ta faranta min rai naji dad’i na kuma gode dashi zanci tuwon dawar Inna miyar kuka.
“Bello yace a gaisheki”
Takalleshi tabbass ya je Matsirga tunda basuyi maganar yan’uwan taba, Bello kuma shine autansu. Yaushe kaje?Duk suna nan lafiya? A lafiyarsu kalau,suma suna gaishe ki dakyau. Yad’auko bak’ar leda yaba ta “Malam ne yace in kawo miki.Tarungume ledar cikin farin ciki “nagode.Yad’an kalleta sannan yasanar da ita abinda yake tafe dashi.Tasunkwui da kai”bazance kome ba sai abinda Malam yace”fad’uwa ta zo dai-dai da zama kenan”Malam ai ya amince dani Bilkisu.A kunyace tace to ai shikenan.Sukayi sallama dan rana ta tafi za ta fad’i magriba na shirin kunno kai.