
Ana bikin duniya ake na k’iyama.
Akwai lauje cikin nad’i…
20 Jumaada Awwal 1441
15 January 2020
We Ibrahim’s Daughters????
Asdilat KD…2geda with Ra’ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta’in
…GWAJIN DAFI????
Almost true story
Daga alk’alamin????
Ya’yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara’atu Ibrahim (Ra’ibs)
Masu k’orafin dan me Sumayya bata auri d’ansarai ba,da masu zaginmu wai labari ya d’auko dad’i sai kuma kawai a kashe Sumayya to duk mun ya fe muku bak’ak’en maganganunku, ALLAH ya yafe mana gaba d’aya.Sai dai ku sani shi Ubangijinmu baya ta6a barin wani dan wani, madamar wa’adin barin duniyar ka ya cika to fa ba tsimi ba dabara dole sai ka barta.Kuma ya kamata kufahimci wani abu,shi fa labarin nan idan kuna duba duk shafukan da suka gaba ta,ai muna rubuta”ALMOST TRUE STORY”ba k’irk’irar shi muka yiba,kaso casa’in na cikin shi ya farune,to sai ku gane ba dukkan abinda kake so ne kake samun shi a rayuwa ba,kuma dole ka kar6i rayuwar a yadda tazo maka,canja wani bangare na labarin to yana nufin canja labarin gaba d’ayan shine.
…GWAJIN dafi????labarine me jigo kusan biyar d’unkule cikin d’aya,dan auna fahimtar makaranta.
Your comments is beyond our expectation…
Ibrahim’s Daughters really appreciate.
1.Zainab Tijjani Ahmad (Ummu Bilqis)
2.Abdullahi Lawal Abdullahi (d’an Sarai).
3.Me Sunan Manya Khadija Kafanchan.
Ya’yan Ibrahim suna godiya,dan kulawa yabawace.
1.Ummu Ammar.
2.Salima Uba d’an Zainab.
3.Maimunatu Ibrahim.
4.Bilkisu Muhammad (Darling)
5.Zaynerb bello 36
6.عيناء ابرهيم عبد المؤمن
7.Ummul Ameen.
8.Shamsiyya Sani 661
9.Ummee Umar Musa.
10.Samira Garba.
11.a’isha Rabi’u.
12.Zainab A.Sulaiman.
13.Hafsa A.Sulaiman.
14.Khadija Bashir(Ummu Hanan)
15.Ummu aimanal habashiyya(Maman Kinanata)
16.My Sau’ash( Asdilat???? for real)
17.Nasiba Namadi ‘Yar Zonkwa????
18.Khadija A.Muh’d (Ummu a’isha)
19.+234 813 109 04..I don’t really no your name,but you care.
20.a’isha Nura Sani (Dr.Maidiyam)
21.Saudat Ibrahim Yahya.Takwarata wannan sunayen na kifa sune rayuwata????????ni Asdilat KD…ina yinki fiye da shurin masaki.
Shafi nagoma sha biyar.
Soyayyarsu ta bazu a dangi,wasu sun yaba sunyi sam barka,yayin dawasu suka koma gefe suna k’unk’uni an rasa gane manufarsu. Suna hirarsu da Hajiya yake fad’a mata”Megado tace a gaishe ki,wannan k’arshen makon baza tazo Islamiyya ba suna jarabawa.Dan haka sai kisa ta a addu’a.Tagyad’a kai”Ubangiji yasa a fara a sa a, yasa asamu kuma abinda ake nema.Amin Hajiya.
Sudaida tana share tsakar gidan tad’an ta6e baki”ni ana fad’in ban iya girki ba sai na iyayi,to su kuma Fulani kona iyayin ma ai basu iyaba,to su da abinda suka iyane banda tatsan nono da tallanshi gidaje da kasuwanni ne?Kai ALLAH yasauwake.Taja dogon tsakin dayasa Julaibib da Hajiya juyawa suna kallanta”lafiyar ki k’alau kuwa Sudaida?
Ta’ajiye tsintsiyar bayan ta kwashe sharan ta zubar.Takauda kai daga kallan da suke mata”kalau d’ina Hajiya gida zan tafi… Fuuu tawuce cikin fushi ko sallama bata musu ba.Hajiya tabita da kallo cikin nazari…sai kuma tayi yar dariya”dawalakin goro amiya.
Julaibib yasauke numfashi “Hajiya kwana biyu yarinyar nan sai ta dinga cimin mad’aci,wallahi jiya data shigo wajan Inna tana kallona amma tad’auke kai ba ko gaisuwa kamar bata ganniba.Hajiya tace”yan wasan ne bata jin yi dakai,kaima ba sai ka share ta kaji da hayagagar…su Nasmat ba?Yayi d’an murmushi “Hajiyar mu ALLAH yaja nisan kwana me amfani. Amin Julaibibi amin.
Malam Lamid’o dattijon arzikine yayi karatun addini dana zamani me zurfi a yanzu hakama likitan dabbobine(Veterinary Surgeon) abinda yatarfama garinsu nono kenan Ya’yanshi suke yin karatun boko me zurfi.Bilkisu itace ‘yarshi ta biyar,ya barta ta cigaba da karatune kasancewar ta me san karatun,kuma tun data gama Secondary ba wani tsayayye sai Jauro shi kuma yace bazai ba Jauro auran taba,data ce ga abinda takeso ta karanta aikin jinya da unguwar zoma,yaji dad’i ya k’arfafeta dan karatun da za tayi zai amfani mata yan uwanta.Shi da matarshi sunyi tufka me kyau da k’wari wajan tarbiyyar Ya’yansu, sai Ubangiji yadubi niyyarsu sai suka ta so cikin tsoron ALLAH da ganin girmanshi ga kunya da sanin mutuncin mutane.
Nurse Bilkisu Muhammad Lamid’o…
Farace Kyakkyawar matashiyar budurwa,kyau irin na tsurar fulani da bashi da gauraye da kowace kabila dan gaba da bayanta, uwa da uba typical Fulani ne, kome na ta irin na mahaifin tane sai dai bambanci na ita macece shi kuma namiji ne,yanayin maganarta da muryar ta shine kawai irin na mahaifiyar ta.
Bilkisu Megadon zinare…idan tayi murmushi ko dariya kai ko magana tayi sai kaga kamar da san a sanine…takeyi dan kawai tanuna yar lotsar(dimple)dake gefe da gefen fuskar ta da kuma yar siririyar wushiryar ta, abinda yak’ara mata kyau na musamman bak’in gashin kanta me yawa da tsantsi irin na asalin tsurar fulani,sai tattausan jajayan la66anta kamar ta turasu da jan jambaki… Bilkisu me kyauce ga sauk’in hali dan bata rud’u da kyawun halittar da Ubangiji yamata ko ilminta ba,kome na ta a natse take yinshi cikin mutunci da sanin kimar kai(a very meek damsel)Tun tana k’aramar Secondary ta sauke Alqur’ani me girma,har yanzu kuma tana karatun littafan addini.
Sauri take yi tana kuma addu’a ALLAH yasa tasamu abin hawa dan gaba d’aya d’alibai sun gama watsewa a hanyar,Khausar ma ai ta tsufa a gida taimakon ta d’aya da Khausar ta tafi mata da jaka, da harda jakar da littafan ciki da ita kanta ruwan saman da yake shirin sauka zai k’are akansu.
Takad’a kai cikin damuwa”gaskiya wanda duk baiji bari ba zaiji hoho,dama su Nasmat sun fad’a mata kar tasha maganin mura da tsakar ranan nan bacci zai sata,tamusu kunnan uwar shegu tawuce dispensary na makaranta takar6i maganin tasha aiko tun a masallaci suna sallar azahar bacci yafara kawo ma idanun ta ziyara,duk k’ok’arinta na korar baccin abin ya ci tura,ganin haka yasa tama Metron magana dan tasu da Sudaida ta zo d’aya sai ta bud’e mata Hostel”Clerkin’s House”har kwanar Kakus d’inta, yar ajin suce amma sunan su d’aya da Hajiya dan haka suke kiranta da Kakus ta haye gadonta ta kwanta aiko bacci yayi awan gaba da ita har aka tashi bata sani ba,bata farka ba sai biyar saura na yammacin amma taji ta garau zazza6in da yake shirin rufe ta ya sauka,sallar la’asar tayi ta d’auki takalmanta tana sawa,lokacin Kakus ta takawo mata jik’ak’k’en k’anzon alkama da madara(corn flakes).
Na ga kina sa takalmi badai tafiya za kiyi ba? Tagyad’a kai tana murmushi”yanzu kuwa”tazauna agefen ta”to amma ai kya tsaya kici abinci na san baza ki iya cin garau-garau d’in dining ba shi yasa na had’a miki wannan me d’an ruwa-ruwa tunda kina fama da mura,tamik’a mata kofin.
Kakus…tasake dubu agogon dake d’aure a hannunta na dama.Uhun Jikalle me kike so kifad’a baza ki sha ba ko me?Tad’an marairaice”ALLAH Kakus…Sai kuma tayi shiru, tasa hannu biyu takar6a,cokali hud’u tasha ta’ajiye “nagode”taharareta”wannan dai dan kar ince baki sha bane kawai.Tadaki kafad’arta’ke yar rainin hankali, to ko akan me zan cika cikina da wanna bayan na san abinci na me rai da motsi yana jirana a gida.Ta tafa hannu cikin salati”Oh ni zamani! Yanzu Jikalle ni kike dukar ma kafad’a saboda wuyanki ya isa yanka.Yadda tayi furucin kamar irin Kakar nan ta gaske yasa Sudaida ta kyalkyale da dariya,sai kuma tad’an marairaice itama”come on Kakus don’t be upset”kema kin san bana miki haka,to yau d’aya dai ya kamata ki kar6i uzurina, Yaya Khausar ta dad’e da tafiya gida,kuma kinga hadari yana ta had’uwa sai cida akeyi bana so ruwa yatareni.Tadafa kafad’arta”na fahimce ki. Suka mik’e…muje in rakaki.Har gate d’in k’arshe nafita daga makarantar tarakata,dan ALLAH ni dai karki manta gobe ki taho min da soyayyiyar gyad’a,tad’an harareta”to anawa?A neman albarka tad’an zaro mata idanu ko bakya san albarkan manya?Sukayi dariya”so kai”sukayi sallama, sannan suka d’aga hannu suna ma juna adabo.