GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da yayi wata d’aya sannan ya dira a Zonkwa dawani yammacin laraba rana ta tafi zata fad’i magriba na shirin kunno kai,yatsaya yayi sallar magriba sannan yatafi gida.Inna tayi murnar ganinshi dan bazata ya mata bai fad’a mata ko awaya ba.Baije ko ina ba sunata hirarasu ta yaushe gamo yana cin abinci ita kuma tanata kalan hotunan dasuka d’auka lokacin da a ke basu horo(training)tad’aga wani hoto tana murmushi ashe kunsha wahala?Yagyada kai”Eh Inna akwai wahala dan sojojine suka bamu horon cikin dare zasu kafa su tsare kowa sai yafito su fara bamu horo tayi yar dariya”lallai kun zama k’ananan sojoji.Amma ni ban wani sha wahala ba. Tagyada kai”ai baza kashaba tunda ka saba motsa jiki da manyan k’arafa yanzu har mata sai sunyi wannan?Eh har su sai sunyi masu tsohon ciki ne kawai naga an d’aga musu k’afa.Taja tsaki wannan tsarinne kawai bai min ba.Yad’anyi murmushi”To ya zamuyi Inna tsarin ne yazo da haka amma Insha-ALLAH bama cire rai da wata rana za a samu manya a harkar masu addini da zasu zamantar da abin dai-dai da shari’ar musulunci a raba mata musulmai da irin wannan shigar a bainan-nasi.Inna tad’aga hannu “Allahumma amin Julaibib.

K’arfe shida na safiya sukayi kaci6is akwanar gidansu,dawowar shi kenan daga masallaci sallar asubahi,k’afafunta sanye cikin takalmi sneaker fari igiyoyin d’aurewa ruwan bula,wando ruwan bulu,farar riga sai hijab iya gwiwa ruwan bula sun sha guga tana goye da bakar jaka da Maths-set a hannunta.Tad’an bud’e idanu cikin mamakin ganin shi”Kai Yaya d’ansarai saukar yaushe? Yabita da kallo duk da garin bai gama wayewa ko ina yayi haske ba amma dai tayi kyau”Jiya gab da magriba.Excursion za kuje? Tasake kallan farin agogon dake d’aure a hannunta na dama”ba wani excursion Mr Goje malamin turanci(English)ne yabamu jinga (Assignment) kuma to be submitted before seven o’clock”to shine kike wannan saurin kamar za ki tashi sama?Tagyad’a kai”eh mana wallahi ji nake kamar inyi tsuntsuwa,wai dan ma ba acikin makaranta muke ba shine yad’aga mana k’afa,su yan cikin hostel ai k’arfe shida yabasu,duk wacce tawuce shida koda da dak’ik’a d’aya ne bazai k’ar6a ba,shikenan kuma fa a matsayn C.A test d’in mune,kuma nayita rok’on Yaya Adnan yakaini yace ba abinda zai fitar dashi awannan sanyin,ai dai ALLAH yajik’an Yaya Aminu ba dan yamutu ba dayana gida na san zai kai ni.Tayi gaba da sauri.

A bayan ta taji horn yabud’e mata kofa”ke Sudaida zo ki shiga mutafi.Yad’an kalleta bayan sun hau titi”lallai baku raina Mr Goje ba.Yaya Julaibib wargi waje yake samu,shi wannnan Malamin mugune na gasken-gaske gashi kuma yanzu shine Labour Master,ya yanka ma mutum k’atan fili iya ganinka yace sai ka nome shi wallahi k’aramin abu ne a wajan shi.

Hankalin Sudaida bai kwanta ba har sai da taganta a Staff-Room agaban tebur d’inshi ta’ajiye littafin ta kuma sa hannu,tafito tana sauke numfaahi”wai ALLAH na! Nayadda k’wallan mangwaro na huta da kud’a.Takoma wajan Julaibib yanata kallanta ta gilashin motar yana kissima wani abu a zuci,tad’auki jakarta. Yad’ora hannun damar shi a saman sitiyarin motar”kin ko karya?A ah.Yakalli agogon motar ai da sauran lokaci kafin kuyi assebmbly ko muje Staff-Quater gidan abokina Aminu Idris ki karya a can?Tagoya jakar”barshi kawai Yaya Julaibib,ai Yaya Khausar zata kawomin.Sukayi sallama,yad’an lek’o da kai “kuyi hak’uri yau akwai inda zani dana dawo na d’auke ku”tad’aga hannu tana mishi adabo ba matsala nagode,tabi motar da kallo har yafita daga gate d’in farko sannan tajuya zuwa ajinsu tana murmushi.

Kwanci ta tashi asarar me rai,biki saura wata d’aya,awannan lokacin Julaibib baya samun zama saboda zirga-zirga tsakanin Azare da Zonkwa,Yadad’a gyara bangaranshi dan anan zasu zauna tunda bai gama ginin shiba.Dasafe yaje gaishe da Kawunshi sunata hira musamman abinda yashafi kasuwancinsu,sai da zai tafi yamik’a mishi wasu mukallai na gidan kane,na baka d’aya daga cikin gidaje na na Unguwar-Rama daura da masallacin Yarbawa hakak malak. Julaibib yad’ago kai bayan ya duba takardar shaidar mallakar gidan sunan shinei ajiki”Kawu nagode ALLAH yasa da mafificin sakamakon shi, ALLAH yak’ara girma.Amin.wannan ai ba kome bane.

Yad’auki Musaddiq sukaje suka ga gida,sabone dal sai k’ura dayayi tunda bakowa yasa yara suka wanke lungu da sak’o na gidan.Kafin yakoma Azare sun sa kome da ake buk’ata suka kulle sau ranar daza a kawo amarya.

Yajingina da bishiyar mangwaran k’ofar gidan yana kur6an madarar shanun tatsar lokacin,hirarsu sukeyi cikin nishad’i irin ta masoyan juna.Bilkisu har naji kin fara k’amshin amarci fa.Tad’anyi murmushi.Yayi tsai da idanun shi yana kallanta”Megado baki ce kome ba? Takauda kai”Kazo ka tafi bana so kayi dare a hanya daga nan zuwa Azare tafiyace me tsayin gaske”Megadon bana san tafiya yau “Takalleshi cikin kulawa”saboda me?Yanunata da yatsa.

Tad’anyi luuu da idanunta kamar zata rufesu sai kuma ta sunkwui da kai”Julaibib ai kai nawane,ni d’in nan ta kace Insha-ALLAH,amma bazan so ace nice silar ta6ar6arewar al’amuranka masu mahimmanci ba,bautama k’asa a matsayin ka na d’an bautar k’asar dole ne,kome kuma za kayi to kayishi yadda ake buk’ata,kazama me amana; tafiyarka ai ba itace rabuwar muba,koda munyi nesa da juna to amma ai zukatanmu suna tare,kuma ga waya muna gaisawa,muna chatting, har video call duk munayi,tad’ago cikin natsuwa da kulawa tad’an kalleshi”duk basu wadatar ba d’ansarai?

Yanad’e hannayan shi a k’irji yana murmushi “sun wadatar Megado,ke macen alheri ce da bata taya 6era 6ari.Yamik’a mata kofin madarar yashiga mota yazauna yana d’aura belt “ALLAH yamiki albarka Bilkisu “tarufe mishi murfin”Amin d’ansarai nagode,sukayi sallama. Tabi bayan motar da kallo a hankali yake tuk’in har ya6acema ganinta.Tajuya zuwa cikin gida tana mishi addu’ar sauka lafiya.

Inna tabita da kallo”har ya tafi?Sai lokacin tasan Inna tana tsakar gida,ta zauna a gefan tabarmar tana d’an murmushi,kumatun ta suka lotsa ciki”a kunyace tace ya tafi Inna”sai kuma tamik’e da sauri ta shige d’aki.

Tana shan rake tana ‘yan wak’ok’inta cikin nishad’i,Khausar kuma tana karanta wani littafi”The secret of occultics powers”su Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu,a’isha tace ya naganku haka?Khausar takalle su “to da ya kike so ki ganmu? Tazauna a gefan gadon”banga kun shirya ba,za muje ganin d’akin amaryane. Khausar ta ajiye littafin”har kin tunamin ance da mahaukaci baya duka.Tabud’e wadrobe tad’auko hijab sannan takalli Sudaida”to mayyar rake badai za kice jiranki za muyi har sai kin gama shaba?

Tamusu kallan uku ahu”kuyi tafiyarku dan ni bana zuwa gayyar sod’i.Suka bita da kallo cikin mad’aukakin mamaki”gayyar sod’i fa kikace? Zuwa gidan Yaya Julaibib d’in?Tayi kamar bataji suba…zuwa can bayan ta shaki iska ta baki ta hanci tafesar tana wani tsuke baki”Eh shi d’in fa wani abu ne?Ni dai wallahi banga abinda zanje gani wanda ban san shiba,ban ta6a ganin shi ba, taja dogon tsaki”gado ne fa da sauran tarkace, tad’ora hannun damar ta a katakon gadan su, wannan ai gadone ko?To gashi na gani akaima nake bacci,sauran tarkacenma muna dasu a d’akin-shak’atawa da d’akin-girki,kuma bama amaryace za tazo da suba,ta kuma jan dogon tsaki cikin tafasar zuciya”kai ALLAH yasauwak’e ma Fulani,wai ace kome mijine zaiyi,ga uban sadaki da suka yanke mai,dubu hamsin sai kace siyar da ita za suyi”ai dai k’arancin sadaki yawan albarkar aure wallahi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button