
Khausar ta tareta da sauri”ke dakata haka malama ai a addinance dama mijine yakeyin kome na d’aki yakuma biya sadaki,dan hakkin akanshi yake ba akan iyayan taba,mu hausawa mune muka fifita al’ada sama da addini a wannan bangaran,kema ai kin sani sarai ban san abinda yasaki wannan furucin ba.
A’isha ma takalleta”lallai ma yarinyar nan yanzu idan ma siyar da itan za suyi sai su siyar da ita a kud’i me mugun rangwame haka? Dan ALLAH nawa ne 50K? Kai Sudaida me yake damun kine naga alama bakya san
Nurse Bilkisu Muhammad Lamid’o…
Ni kuma wallahi tana burgeni saboda sauk’in halinta,wallahi sam bata d’auki duniya kayan gabas me k’amshin turaran d’an goma ba, haka fa ranan nan da muka had’u da ita a hanyar Islamiyyar su itafa tafara gaishemu amma kikayi banza da ita,bakyau irin wannan halin ko Yaya d’ansarai da baya san kula mutane amma idan kika mishi magana zai kulaki ko sama-sama ne.
Nasmat tana ta nazarin kalaman Sudaida tayi yar dariya tana tafi tasake kallan Sudaida”kina kishi ne?Takusa k’warewa da raken da take sha Dammm… Zuciyar ta tabuga tamata wani kallo”kishi kamar yaya,me zai sani yin haka?So…Nasmat ta bata amsa.Duk sai suka zubama Sudaida idanu”biri fa yaso yayi kama da mutum. Numfashinta yad’auke na wucin gadi… Tamik’e cikin fushi tana kallan Nasmat “so fa kika ce?Tagyada kai”eh kwarai kuwa so.Sai tafara hayagaga…”eh so ne sai me?Suka kyalkyale da dariya ganin yadda take masifa”eh ina san nashi amma ba irin soyayyar da kike tunani bane, soyayyace irin ta yan uwan taka, karki manta ina da masoyi na da makaranta yake jira in gama sai in koma k’ark’ashin shi ta inuwar aure.
Nasmat ta daki kafad’arta tana dariya “ahaf ba mage ba miyauuu…Takalli su a’isha”kuzo mutafi kunji tunda baza tajeba.Tabisu da kallo har suka gama fita a d’akin.Tad’auki hijab tasa gwamma kawai tabisu,sai wani irin abu mara dad’i ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar ta,kawai sai ta koma ta kwanta,tad’ora tafin hannun damar ta a saman goshin ta dayake barazanar yin ciwo, ta yamutsa fuska tana hura iskar bakinta tana jin wani d’aci kamar tasha mad’aci.
Mama uwargidan Alhaji Ibrahim macen albarka,macen k’warai dattijuwa me yakana da karamci, uwargidan cinta na dalci da amana takeyi,abinda yahaifar da kwanciyar hankali kenan,yasa zuri’ar gidan suka dunk’ule suka zama tsintsiya mad’aurinki d’aya.Duka Ya’yan gidan ta d’aukesu abu d’aya kamar ita ta haifesu.A d’aki tasamu Sudaida a kwance idanun ta a rufe,amma ba bacci takeyi ba.Ta zauna a gefan gadan,Sudaida tabud’e idanun ta da suka d’an canja kala.Mama takalleta da kulawa”wai mantawa kikayi da Sinan a waje?Tadad’a kwantar da kanta a saman matashi “Mama kaina ne yake min ciwo”sanin hali yafi sanin kama”sai tayi murmushi kawai”To ai ya kamata kije kifad’a mishi kar yayi jiran gawon shanu ko?A ciki ta amsa kamar ranta bai mata dad’i ba”to Mama na ji.
Tana fitowa yatareta”Sudaida Sarauniyar Sinan”taturo baki gaba tana d’an harararshi”kai baka san kaina ne ya dameni da ciwo kuma Mama ta matsamin dole nafito”yayi murmushi wani lokaci haka take abu kamar wata ‘yar k’aramar yarinya wai an matsamata dole tafito.Sai ya marairaice”Oh ALLAH! Wayyo! Sannu Sarauniyar Sinan taso muje ki kar6o magani? Tagirgiza kai’ai ma navfara jin sauk’i.Yasauke numfashi”kai nagode ma ALLAH,dama ni ne maganin ko?Sukayi dariya.
Tana d’ago kai za tayi magana caraf idanun su yahad’u dana Julaibib,yana sanye da shadda ruwan k’asa yayi shar…shar dashi,magana yakeyi a waya yaja yatsaya nesa dasu.Tad’an ta6e baki”wayar tak’ici tak’i cinyewa,ba mamaki shi da wannna Bafulatanar ce.Yagama wayar sannan yamata wannan rikitaccen kallan da tadad’e bataga ya mataba,dama baya kulasu in dai yatarar suna hira ko magana tamishi sai yayi kamar ba dashi take yi ba”kunnan uwar shegu”tabishi da kallo har yashige cikin gidan.Takalli Sinan ni zan wuce”Shikenan anjima zan bada masoyin Sarauniyar Sinan akawo miki (rake) tayi d’an murmushi “nagode.
Ranar Juma’a suna gidan Yaya Karima sunje mata ziyara sai gashi yashigo da sallama.Yazauna suna gaisawa da Yaya Karima tana tsokanar shi”Kai autan Inna har wani haske naga ka fara ko kaima kana gyaran angwancinne dasu halawa da dilka?Yakai hannu yana sosa k’asumbarshi yana yar dariya”Kai Yaya Karima duk sukayi dariya;banda Sudaida da ta tayi kamar bataji me aka fad’a ba,tacigaba da cin sinasir d’inta,Nasmat tace”wai ina masar Bauchin dana ce ka kawomin tsaraba?Haba ke kuwa Nasmat ai k’aton aiki za ki bani ace tun daga Bauchi har Zonkwa in rik’o masa?Gaskiya bazan iyaba,indai za kici kantu(rid’i)to kije wajan Inna ki kar6a.
Ni masa nake so tunda baka kawo min ba ai shikenan nagode ALLAH kuma yabamu lafiya, amma da Bilkisu ce tace tana san masar ai baza ka d’auki hakan a matsayin k’aton aiki ba ko? To dake da Bilkisu Megadon Zinare…d’aya ne? Sudaida tamik’e”uh wannan Bilkisun dai ko gadon Mahogany ba ta dashi”tajuya za ta bar d’akin. Yarik’o gefen hijab d’inta..kafin yayi magana tajuyo cikin fushi”Yaya d’ansarai sake min hijab ka san dai bana wasa da maza.Su Nasmat suka kyalkyale da dariya kaji wata magana kuma? Yakalketa cikin natsuwa”idan kuma ban sake ba fa?Tayaye hijab d’in gaba d’aya daga jikinta tajefa mishi a fuska “kaje ka kai mata”fuuu…tafita mayafin Yaya Karima tajawo a igiya tayafa.Duk suka bita da kallo.Yaya Karima takama ha6a”to ana wata ga wata aure ya mutu ga gara.Takalli Julaibib ya sunkwui da kai”ranshi a 6ace yake,amma ta san bazai yi magana ba tunda yayi haka,wannan halin shine tun yana yaro indai ya sunkwui da kai.
Yamik’e da hijab d’in a hannun shi “Yaya Karima ni zan wuce idan Baban Abdul yadawo kya mik’a min sak’on gaisuwa.To auta mungode kwarai kagaishe dasu Inna sai na shigo.
Har yakoma Azare Sudaida bata yadda sun kuma had’uwa ba ko gidan Inna bata sake zuwa ba dan kar ma su had’u sai bayan data tabbatar ya tafi sannan taje.Yakirata sau d’aya a waya tak’i daga wa shima bai sake kira ba.
Tana zaune a dakalin k’ofar gida da tunanin inasu Mama suka suka tafi haka harda kulle gidan gaba d’aya bayan sun san za su dawo daga makaranta?Sagir yazo da gudunshi zai kwashi kayan wasa a inda ya6oye can wani sak’o, tarik’o hannu”su Mama ina suka tafi?Matsirga su da Yaya Musaddiq da akwatuna,tasake shi yatafi. Lefe sukaje kaiwa kenan? Tad’an ta6e baki.
Gidan Yaya Musaddiq tawuce. Safiyya tace”wata sabon gani.Tazauna a kujera tana yar dariya”ALLAH Yaya Safiyya ba lokacine kullum muna hanyar makaranta.Tagyad’a kai”na yadda,to shiga d’akin-girki kizubo abinci danna san kin kwaso yunwa,tak’arasa kwanciya a kujerar “ai azumi ma nake yi,ke me yahanaki zuwa garin Fulani kai lefen?Uhun ke dai bari har na shirya sai ga baki na yi ba zato ba tsammani basu dad’e da tafiya ba.Takuma ta6e baki tamaida idanun ta tarufe kamar tana bacci amma ranta in yayi dubu ya 6aci,taja tsaki tanata juye-juye,data gaji sai tamik’e tafito da littafin lissafinta tana nazarin Quadratic Equation.
Julaibib da Bilkisu suna tsaye a wajan da ake ajiye motoci na cikin makarantarsu, tana tambayar shi “ya me jiki? Yagirgiza kai”ni fa ki daina tambaya ta ya me jiki, idan kina san sanin ya take ai zuwa za kiyi ki gaishe ta ko? Haba Megado wallahi kin bani kunya ace Yaya Asma’u takwanta a asibiti kwanaki goma kenan amma ki kasa zuwa gaisheta,aiko ba soyayya a tsakanin mu to akwai hakkin musulmi akan musulmi koda ba dangin Iya ba na Baba,gaishe da mutum idan ba shi da lafiya yana daya daga cikin hakkoki biyar akan musulmi da musulmi.