GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tasunkwui da kai”kayi hak’uri d’an Sarai Insha-ALLAH zan je.Yagyad’a kai”to muje in rakaki. Nagode zan je ni kad’ai suka d’an ta6a hira kad’an suka yi sallama. Abakin a sibitin ta tsaya ta sai kayan marmari sannan tashiga.

Sudaida ce tabud’e k’ofar,suka kalli juna Bilkisu ba girman kai sai ta gaisheta,tatsuke baki cikin yamutsa fuska ta amsa mata dak’yar sannan tabata hanya.Tashiga da sallama ta durk’usa ckin natsuwa me had’e da kunya tagaishe da Hajiya tana tambayar ya me jiki?Dan ALLAH amin uzuri da banzo da wuri ba yanayin karatun mune sai a hankali,Tamatsa jikin gadan tana gaishe da Yaya Asma’u da tambayarta karfin jiki.Tayi murmushi”jiki Alhamdulillahi tunda gobe ma za a sallame ni.

Hajiya ta kalli Sudaida”kawo mata ruwa mana.Tajuya tama Bilkisun wani kallo”Hajiya ita tace miki tana jin k’ishi?Mutanan d’akin suka bita da kallo in ka d’auke Bilkisu da Hajiya.Bilkisu ta sunkwui da kanta,Hajiya kuma tana nazarin Sudaida a karo na barkatai kenan tana nuna halin-ko-inkula da duk wani abu daya shafi Julaibibi tun lokacin da maganarsu da Bilkisu ta kan-kama, takad’a kai”lallai da magana karuwa ta ziyarci tuzuru.

Yanzu sai ta ce tana jin k’ishi za a bata ruwa Sudaida?Bak’on ka annabin ka.Tamik’e tana k’unk’uni tad’auko ruwan ta dangwarar a gabanta.Hajiya tadafa kafad’ar Bilkisu da sigar rarrashi dan abinda Sudaida tayi bai kyautu ba sam”kiyi hakuri Bilkisu”Tad’anyi murmushi me had’e da kunya”ba kome Hajiya,dan kar suce taji haushin furucin Sudaida ne da baza ta shaba tunda ba ta jin k’ishi,kad’an ta tsiyaya a kofi tana kur6.

Sudaida ta galla musu harara, tabud’e jakar ta tad’auko earphone tamak’ala a wayarta sannan ta toshe kunnuwan ta dashi, tashiga bin wak’ar, zaman d’akin ya gundireta sai tafita tabasu waje ganin hadari yana had’uwa yasa tawuce gida

Feshin ruwan yafarkar da Khausar daga baccin data fara,ga littafan data barbaza a saman tebur har sun fara jik’ewa,tarufe taga tasuke labulan sannan takalli Sudaida “saboda ALLAH kina ganin ruwa zai jik’a min littafai amma kika ki rufe taga?Tayi kamar ba da ita take magana ba,sai ta fizge wayar”bakya jine ina miki magana?Tabita da kallo”ke wai kwana biyun nan lafiya kuwa?Eh ita takawo haka,tamik’a mata hannu bani waya ta.Tabata wayar tana gyad’a kai”lallai kam nima naga alama lafiyar ce takawo haka,tayi d’as da yan yatsunta”to amma fa karki manta duk kanwar ja ce,baki fini tsummaba bazan zauna kina 6ar6ad’eni da k’wark’wataba, wallahi ban kar zomo;tanunata da yatsa ke baki isa ki kisa ni d’aukar rataya ba.Sudaida tabita da wani malalacin kallo”ALLAH sarki.

Suna tsaye kusa da rafin Matsirga d’ansarai yad’aga kai yana kallan Qudirar Ubangiji duk da ba ranar yafara gani ba,Tsawon tudun yayi gidan sama hawa uku tanan ruwan yake fitowa yana gangarawa wani rami a can k’asa me tsananin zurfi kuma a saman turawa sukayi titin jirgi k’asa kuma har yanzu tanan d’in yake wucewa,sa dai gaskiya duk wanda yafad’a ramin nan to ya gama numfashi a doron duniya wallahi.

Bello yarik’o hannun Bilkisu “Adda zo mu tafi gida kinga hadari yafara had’uwa kar ruwa ya 6alle.Julaibib ya kalleshi”to mutafi suna tafiya suna d’an ta6a hira har suka zo k’ofar gidan.Julaibib yabud’e mota yad’auko wasu wara-warai (Awarwaro)masu kyan gaske a d’an gidan su”wannan kyautar soyayyace ta musamman ga wacce tayi nasarar mallake zuciyar Julaibib… Bilkisu Megadon Zinare…Bilkisu Zinariya kike kinfi azurfa.Yamik’a mata tasa hannu biyu ta kar6a “nagode k’warai Julaibib d’ansarai”.

Ke kad’ai nake so Megado…

Tasunkwui da kai tana d’an murmushi cikin jin kunya kumatunta suka lotsa.Yad’an d’age gira”au baza kice kome bane?Tad’an d’ago takalli Bello ya ko zuba musu idanu kuriii yana kallansu. Yayi murmushi”Oh na fahimta,a dinga sara ana duba bakin gatari ko?Tagyad’a kai.Sukayi sallama a gaggauce dan an fara yayyafi.

A sanda hantsi yadubi ludayi amma har lokacin garin da sanyi saboda ruwan saman da aka dinga tsuugawa kamar da bakin k’warya tun dare har wayewar gari sai wajan k’arfe bakwai da rabi ruwan yad’auke,Iska tana ta k’adawa. Tibishi yakalleshi amma jiya ka burgeni.Yakai mishi duka”wani burgewa ka sa inata tari kamar zan shid’e,sukayi dariya suka tafa”ai da haka za ka zama k’wararre.Tibishi yad’an ta6a shi”kai ga mutuniyar ta ka can,yajuyo da sauri “haba dai? Bai gan taba dan ta riga ta sha kwana” amma dai bata ganni bako? Yagalla mishi harara “kaji d’an iska to idan ma ta ganka sai me? Yamik’e”a ah wallahi da matsala,katafi kawai anjima anjima zan nemeka a waya.

Tabishi yarik’o rigarshi ta baya “dakata malam ai ba haka mukayi dakai ba,sai ka bani kud’i indai kana so katafi,baiyi magana ba yaciro d’ari biyar yabashi yajuya da sauri dan kar tayi nisa.Tabishi yabishi da kallo yana kyalkyala dariya”Sinan shegen duniya,kura da fatar akuya yad’an yi tsaiii…nawucewar wasu dak’ik’u yana kissima wani abu a zuci sai kuma yad’an motsa kafad’a”any way akwai dai ranar k’in dillanci ranar da hajar me gari zai 6ata.

Gudu-gudu sauri-sauri har ya cimmata yasha gabanta”haba Sudaida Sarauniyar Sinan ai ya dace ki tsaya ki saurareni ko?Tagirgiza kai”bai dace ba” Sinan katafi kabani waje karka 6ata min lokaci a banza a wofi.Yakwantar da murya yadinga mata kalaman rarrashi da bambaki har sai da yaga tana murmush”amma ai kai kafad’a min da bakin ka ka daina kulasu Tibishi amma ayyukanka suna k’aryata furrucin ka,jiya da yamma gab da za a fara ruwa tare naganku ka goyo shi a mashin kunyi hanyar D’One takalleshi cikin natsuwa wajan shan giyar koko ka kaishi da kanka Sinan?Yanzu kuma na sake ganinku tare kuna hirarku kuna ta dariya har da tafa hannaye; Sinan wai mantawa kake yi da d’abi’a tana na so? Zama da mad’aukin kanwa yana kawo farin kai fa. Haba Sinan me…

Yatari numfashinta”Kiyi hak’uri Sudaida amma wallahi Tibishi shi ke bibiyata,ni kuma abinda yasa nakasa korarshi muyi baran-baran ina mishi kwad’ayin musulunci,wata kila ta dalilin Sinan masoyinki sai kiga ya samu dacewa zuwa addinin gaskiya kina wannan ai babban jihadi nevko?Tajijjiga kai”mutum d’aya yashiryu ta dalilin ka yafi abaka jajayan rak’uma guda dubu “Yad’an shafa k’irjinshi bangaren zuciya”Oh ALLAH nagode maka”sukayi dariya yad’an taka mata sannan sukayi sallama tawuce gidan Hajiya.

Shi kuma yakoma wajan Tibishi yana fada mishi”abinda nake so dakai mudaina had’iwa a cikkn gari,ni idan inada buk’atar ganinka zan biyo ka har D’One.Yamishi wani malalacin kallo cikin fesar da hayak’in maro (wiwi) tabaki ta hanci “saboda wata Sudaida?To in tamabaye ka mana “haka zaka aure ta bata san kome a tare da kai ba sai halin waliyai?Ranar da duk tagano kana kanaga zata zauna dakai cikin aminci da amana? Yatareshi cikin hayaniya”kar kamin sanadin 6acin rai da sanyin safiyar nan dan zan gwada maka rashin mutum ci dan abu kazan uban ka,kafin Sudaida tasan kome ai na daina.Tibishi yagyad’a kai “wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunne.Yanuna shi da yatsa”indai muna tare da Sudaida to karka kuskura ka doshi wajan.Angama ranka yadad’e yajuya yayi tafiyar shi yana ma Sinan dariyar rainin wayo.

Kafin tayi wani yunk’urin tashi dan ta jiyo muryar shi,har sun shigo d’akin-shak’awar. Musaddiq yakalle ta”d’auko kayan da Baba yabaki kiba Julaibib tamik’e “to. Musaddiq yamik’a mishi hannu sukayi musafaha”to ALLAH yatsare hanya shi Musaddiq a Kaduna yake bautar k’asa yanzu zai koma.Yazauna zaman jiran ta sama da dak’ik’u talatin bata kawo mishi ba ya kira wayar ta ta k’i d’agawa,sai yamik’e zuwa tsakar gidan ana yasame ta sunata hirar su dasu a’isha.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button