
Hajiya tashigo”yayane Sudaida kike kuka kuma?Musaddiq yayi kwafa”kyale ni da ita kawai Hajiya samun waje ne kuturu da gad’a a rama.Julaibib yadafa kafad’arshi”ka kyaleta mana wata kila bayan ciwon k’afafun akwai hujjar datasa tak’i zuwa,ka san hali da dabi’ar mata Iyayanmu, yan’uwanmu,k’anninmu sai hak’uri, sai ana kawar dakai awasu lokutan idan ba haka ba,sai su maida kai wani iri,yazame hannun Julaibib daga kafad’ar shi, yajuya yayi tafiyar shi;tasauke numfashi sai a lokacin tashak’i iskar yanci”kai Yaya Musaadiq barkono ne,yanzu haka yakema Safiyya wannan halin?Hajiya tace”barin kira miki shi yaba ki amsa dan wak’a abakin me ita ta fi dad’i.Takama ha6a”wuuu…Tabbb Hajiya rufa min asiri kar k’ilu taja bauuu…
Ya tashi sahur azumin nafila na ranar alhamis yana juya zuman dayasa a shayin na’a na’a da ‘ya’yan algarib yayi tsai…cikin tunano mafarkin dayayi da daddare…
“Kasham yake gani da kayan fulani tayi kyau k’irar kalangunta ya fito rad’am,amma idan tayi magana muryar Sudaida yake ji.
Shekarun baya yayi wannan mafarkin to yanzu ma mafarkin ya dawo shi ya rasa gane kan wannan mafarkin.Yayi bismillah yafara kur6a amma ko kwata bai sha ba kome ya gundire shi,shayin yamishi wani irin d’and’ano mara dad’i,ya ajiye kofin a saman tebur.Yad’auki farar hular zita yasa yad’auki Alqur’ani me girma yana karantawa har aka kira assalatu daga mabambantan masallatai na unguwar,yayi raka’atal fajri sannan yafito suka tafi masallaci shi da Baba.
Tana fitowa daga asibiti motar shi tana tsayawa,yabita da kallo tayi kyau a cikin fararan kayan riga da wando da d’an madaidaicin farin hijab,suka kalli juna sai yamik’a mata hannu ta san me yake so dan haka tamik’a mishi ragowan Schweppes d’in da yake hannun ta”ya ajiye a mota dashi zan yi bud’a baki “Megado kinga kyan da kike k’arawa kuwa tun bamu fara cin Shahrul-Asal (Honey Moon) ba?Ya d’aga kai sama alamar tunani”Bilkisu k’wak’walwata 6angaren nazari da tunani ta gaza gano yadda zan fasalta irin kyan da kike tayi,wai meye sirrin ne?Yazubama tattausan jajayan la66anta idanu;tayi dariyar da tun had’uwar su bata ta6a irinta agabanshi ba, kumatunta suka lotsa ciki sosai yar siririyar wushiryar ta,ta dad’a k’awata fuskar ta,Ya ilahi… Shi da kanshi ya kauda kai yana jin wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi game da ita.
Wai kai kwana biyun nan me yake damun kane sai kadinga wasu maganganu kamar lokacin kafara gani na?Yamata wani kallo”yunwar so ke damun zuciya ta. Matsirga zan tafi,takawar da wannan maganar.Yakalleta cikin makaki”wani irin Matsirga kuma da safen nan?Haba kibari kid’an samu bacci koda awa uku ne,kinga aikin dare kika yi na san baki yi bacci ba,idan kika d’an huta bayan azahar ba sai ki tafi ba?”ni dai dan ALLAH yanzu nake san tafiya kar inyi hutun jaki da kaya aka,agida sai in huta gaba d’aya.A ah Megado ban yadda ba,ba ranar lahadi da yamma kika dawo daga Matsirgan ba?Tagyad’a kai”Inna nake san gani, tayi yar dariya”wallahi gobe da safe zan dawo Insha-ALLAH.Ba ga waya ba kikara ta mana.Tad’an marairaice”ni dai nafi so inganta ganin idanu na.Yad’an harareta”shikenan tunda kin na ce sai kin tafi to muje in kaiki,idan muka kwana sai mubugo sammako da sassafe dan nima Zari’a zani a goben.
Tad’an bud’e idanu dan mamaki”ka kwana a ina?Bai bata amsa ba yashiga mota yazauna sannan yakalle ta”shigo mutafi mun… Kiran wayar Baba takatse shi yad’aga da sallama “kazo yanzu na yi baki suna jiran ka a shago.Ya amsa cikin ladabi”to Baba gani nan zuwa.Yad’anyi jimmm…d’ansarai lafiya kuwa?Kiyi hak’uri Megado na so kwarai mutafi tare to sai dai hak’ata bata tadda ruwa ba,akwai bak’in da suke jirana a shago.A ah ba kome” tashiga ta zauna yaja motar.
Tasha yakaita yasata a motar haya, gidan gaba yabiya kud’in mutum biyun dan ta zauna ba takura,suna ta hirarsu yana fad’a mata wasu kalamai masu nauyi,tad’an harareshi sannan ta sunkwui da kai “ka san ALLAH idan baka daina fad’a min wad’annan kalaman ba zan daina sauraranka,kuma ko waya ka kira bazan d’aga ba, yayi yar dariya”ni kuma ban san inda kike bako? Kaji yar rainin hankali kamar wata k’aramar yarinya, ba aikin asibiti kikeyi ba? Wancan makon ba d’akin yan hatsari kuma maza aka kaiku ku musu dressing ba?Wani dare ne jemage bai gani ba?
Tasa hannun damar ta tashafa dogon karan hancin ta,tayi kamar bata gane me yake nufi ba.Akwai dararan da jemage bai gani ba fa.To wani dare ne kuwa?Shima yatambaye ta. Tamishi wani kallo daya sa zuciyar shi bugawa Dammm…bai kuma san dalili ba.Daren da aka haife shi da daran mutuwar shi ko ya gani? Yagirgiza kai.Kiran Adnan yashigo wayar shi, yad’aga da sallama.Adnan ya amsa sannan ya tambaye shi”kana ina ne d’ansaarai?Ina tashar mota.Tashar mota kuma?Me kakeyi a tasha? Bilkisu zan sa a motar Matsirga.Tam dama Hajiya zan kai unguwa Yaya Aminu yafita da motar gida. Shikenan zo ka kar6i mukullin.Suka cigaba da hirar su har Adnan d’in yak’araso suka gaisa da Bilkisu a mutunce yakar6i mukullin motar yatafi.
Shafff…ya manta da kiran Baba sai da kiran shi yasake shigowa sannan ya tuna”Baba ayi hak’uri gani nan zuwa”yamayar da wayar aljihu “Bilkisu barin je in dawo.Takalleshi cikin natsuwa “bak’i fa kukayi kafin kugama abinda za kuyi ka dawo ai na tsufa a gida,sai dai munyi waya. Yagyad’a kai”shike nan nagode ALLAH yamiki albarka.Amin.
“Sai munyi waya…suka fad’a atare.
Sannan suka kalli juna sukayi murmushi yad’aga hannu yana mata adabo yajuya da d’an sauri dan kar Baba yasake kiran shi,tabi bayan shi da kallo har ya tsallaka titi ya6ace ma ganinta,tamaida kanta jikin kujera tana sake kiran lambar Inna dan ta kira sau shurin masak’i amma bata shigaba,saboda matsalar na’urar sadarwa. Motar su ta cika suna shirin tashi ta tura ma Julaibib sak’on murya(voice note).
“Julaibib yanzu motar mu ta tashi… Ina sauka kai zan fara kira,ta mishi sautin sumba muahhh… ????”
Abinda yaketa rok’on ta ayan kwanakin nan tamishi kenan,amma k’ememe tace wai ita bata iya ba,rannan data bashi haushi yace”kar ALLAH yasa ki iya d’in za ki zo hannu duk sai kin biyani bashi dalla-dalla.
Yadawo daga sallar azahar zai shiga d’aki kiran Bilkisu yashigo,yayi murmushi “haba Nurse Megado ko dak’ik’u talatin bakuyi da tashi bare kice har kin sauka, yad’aga da sallama “hayaniya da kururuwane ya cika kunnuwan shi “Bilkisu lafiya kuwa?Wata murya ta amsa”ba Bilkisu bace kazo Wadom yanzu-yanzu sunyi hatsari ne”Innalillahi Wa’inna’ilahi raji’un” Istirja’in shi Inna taji fito daga d’akin-girki da sauri. Yajingina kanshi da bango jikin shi a sanyaye “lafiya kuwa d’ansarai? Sai ga Musaddiq ya shigo duk suka zuba mishi idanu su. Musaddiq yace”me yafarune?Inna tawatsa hannu”abinda nake tambayar shi kenan kashigo.Yadafa kafad’arshi”yi magana mana Julaibaib…”Megado ce sukayi hatsari.Inna da Musaddiq suka yi Istirja’i suma, yaja hannunshi”to tsayuwar me muke yi?Inna sai mun dawo.Tabisu har zaure bakin ta d’auke da addu’ar Ubangiji yatsare musu hanya.
Gudu sosai Musaddiq yayi.Wajan ya cika dank’am da mutane da jerin motoci,wani hukuncin Ubangiji kuma daga Bikkisu sai wani dake gidan baya sune sukaji mummunan ciwuka, sauran dai k’uk’k’urjewa kawai sukayi, shi dama d’an Wadom d’in ne yan’uwan shi sun zo sun d’auke shi zuwa asibiti.