GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ruguzowar wani abu yaji a k’ahon zuciyar shi lokacin daya ga Bilkisu a kwance sambal cikin jini fuj’atan, zuciyar shi tafara wata irin bugawa da k’arfin gaske kanshi yasara, yahad’iye wani abu me zafi,yasa hannayenshi biyu ya cicci6eta zai sa a mota sai kawai wajan ya kaure da salati, masu ihu na yi,masu fad’in Jesus Christ,Holy Mary nayi,masu d’ora hannaye aka suna sambatu da yarukan su na yi, bai fahimci kome ba sai da yaga Musaddiq ya d’auki farin hijab d’inta da yarine da jini ya koma ja,yad’aure mata kai,ashe kan tsagewa yayi ana hango ciki, yashimfid’eta a bayan mota.

Jama’ar wajan na musu fatan su sauka lafiya, ita kuma ALLAH yata shi kafad’a yasa kaffarace.Shi kanshi Musaddiq ta maza yayi yake tuk’in saboda ya shiga rud’u da damuwa,a haka har suka koma Zonkwa.

“Saint Louis Hospital 6angaren hatsari da taimakon agaji na gaggawa(Accident and Emergency) aka wuce da ita,Julaibib ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai-kawo yake yi a barandar wajan.Musaddiq yarik’o hannun shi suka zauna”kayi hak’uri Julaibib na kira Malam Lamid’o a waya yanzu haka suna hanya.

Suna zaune jingum-jingum har su Baba da Malam Lamid’o da Yayyin Bilkisu Maude da Tukur sukazo, zaman awanni biyu sannan zugan likitocin da ma’aikatan jinya suka fito daga d’akin.Gaba d’aya suma suka mik’e kowanne hankali a tashe,Babban likitan yace ku biyoni office.

Cikin natsuwa yad’ago yana kallansu bayan ya gama yan rubuce-rubucen shi a wani fallan takadda me sunan asibitin”kuyi hak’uri Insha-ALLAH kome zai zo da sauk’i,yanzu dai mun bata taimakon gaggawa wanda za mu iya amma gaskiya abin ya fi k’arfin mu dan ya shafi k’wak’walwarta sai dai kuwuce da ita Shika, Ahmadu Bello Teaching Hospital Ubangiji yaba ta lafiya,yanad’e takaddan yamik’a ma Malam Lamid’o”Idan kunje ku ne mi…

“Doctor Garga Ibrahim Manogi…

Maude yagyad’a kai”Alhamdulilahi Doctor Manogi k’wararren ne akan abinda yashafi k’wak’walwa (Neurology) kuma k’anwar Innar su yake aure, dan haka fad’uwa ce tazo dai-dai da zama.Suka koma d’akin da Bilkisi take kwance, jikinsu yayi mugun sanyi,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba, Ubangiji kamana kyakkyawan k’arshe????tukur yace muna 6ata lokaci ai gwamma muyi harama.

Malam Lamid’o da Tukur agaban motar sai Julaibib da Bilkisu a baya,su Baba dasu Musaddiq suka lek’o to Ubangiji yakaiku lafiya. Maude yace gobe sammako za muyi da Inna, Malam Lamid’o yagyad’a ka.Tukur yaja motar, suka bisu da kallo har suka fita daga asibitin suka hau kwalta.

Julaibib yazuba mata idanu zuciyar shi na bugawa da k’arfin gaske d’ik d’ik d’ikkk…wuyan ta ya karye an sa mata stiffness collar,kanta yana cinyar shi har lokacin jini bai daina zuba ba,bandejin da aka nannad’e kanta dashi saura kad’an yajik’e,hannunta nadama akwai karaya guda biyu,idonta na dama ya zurma ciki sosai alamar ya fashe ruwan ciki ya gama tsiyayewa,idonta na hagu kuma ya kumbura suntum har wani kyalli yakeyi,gaba d’aya kamanninta ya canja saboda kumburin da fuskarta tayi. Idanun shi sun kad’a jawur kanshi yana wani irin sara mishi,yakad’a kai cikin maimaita Istirja’i yana tallafe da kanta… Motar tsittt kowa da yadda abin yadake shi,wucewar wasu dak’ik’u hannun hagunta da yarik’e yaji ya saki tayi wata ajiyar zuciya Dammm…zuciyar shi tabuga!Yasake zuba mata idanu yana ta6a wuyan ta,harbawan da yake yi ya tsaya cakkk…Tukur yana kalkanshi ta madubi a hankali yagangara gefen titi yatsaya.Malam Lamid’o tun shigar shi motar kanshi ak’asa yad’ago”Tukur lafiya?Duk suka juya baya,Tukur yabud’e motar yakoma baya yana tatta6a ta,da rawar murya yace”Malam kamar fa bata numfashi.Sukayi shiru nawasu yan dak’ik’u.Malam Lamid’o ya tabbatar Bilkisu ta mutu!

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!…KULLU NAFSIN ZAA’IK’ATIL MAUT!Kowace rai sai ta d’and’ani mutuwa????ubangiji mun tuba,dama kowane d’an Adam me kuskure ne,sai dai mafi kyawun masu kuskure sune masu tuba.Ubangijin mu kamana gam da katar da kyakkyawan k’arshe,mu mutu cikin da’a da dokokin ka????????…

“Julaibib yace Malam Bilkisu fa bata mutu ba,dogon suma tayi.Tukur ma yagyad’a kai”nima haka nake tunani yakoma gidan gaba yazauna yana k’ok’arin tayar da motar”Malam inaga jinin da take ta zubarwa ne yahaifar da haka.Juya da motar nan mukoma gida a mata wanka akaita d’akin ta na gaskiya Ubangiji yasa k’arshen wahalar kenan Bilkisu,kwallah suka cika idanun shi,yasa gefen babbar rigar shi yagoge. Julaibib da Tukur sukace “a ah Malam Bikkisu bata mutu ba,Insha-ALLAH kuma za ta warke. Malam Lamid’o yadafa kafad’ar Julaibib”kar muyi haka daku mana, ni tunda naga Bilkisu dama na san indai ba wani hukunci na Ubangiji ba to baza ta rayu ba,idan ma ta rayu to za ta samu tasgaro me yawa arayuwar ta,kuyi hak’uri Bikkisu ta riga ta tafi ni naga mutuwa ba d’aya ba ba biyu ba.

A asibiti ma likita yabasu tabbacin ta rasu,dukkansu hawayene yake zubo musu sharrr… Sharrr… Wayyo ALLAH!Duniya gidan ci rani,duniya gidan azo a wuce! Kowa sai ya koma gidan shi na asali (Lahira)

Gidansu Julaibib suka wuce da gawar Bilkisu dan Malam Lamid’o ya ce ba sai sun tafi Matsirga ba,duk inda musulmi yamutu ai za a iya yi mishi wanka a mishi sallah akwaishi makwancin shi.

Inna da Musaddiq da Hajiya suna zaune cikin jimami sai ga Julaibib yashigo cikin tashin hankali “Lafiya kuwa Hajiya ta tare shi,me yadawo da kai? Ya zauna a kujera idanun shi sun kad’a jawur,wata jijiya ta fito rad’am a gefen goshin shi kamar shatin bulala, yabisu da kallo sai kuma yamik’e, jikinsu ya basu dan haka cikin zafin nama Musaddiq yarik’o shi”Hajiya tace kayi hak’uri… Mutuwa ba ta jira ALLAH baya barin wani dan wani, ALLAH shi yayi Bilkisu, dama aran ta aka ba mu,to lokacin tafiyarta ta yi dan haka bamu isa mu hana ba,suka cigaba da rarrashin shi da kalamai masu taushi,Musaddiq yafita wajan su Malam Lamid’o dan har an shiga da ita d’akin-shak’atawar Inna.

Maude ne yazo da Inna,tana ganin ta a kwance sambal fararan kayan aikinta sun rine da jini sun koma kalar ja,tayi fari fattt…ta d’ashe alamar babu sauran jini ajikinta.Inna ta zuba mata idanu cikin hawaye”Bilkisu ke ce kika zama haka? Takad’a kai cikin sarewa da al’amarin rayuwa, kamanninta sun canja ta zama wata irin halitta,a fuskarta ba irin halittar d’an Adam ba amma wai hukuncin Ubangiji sauran gangar jikin ta lafiya lau ko k’warzone ba bu na ciwo,in banda hannun damar ta “Bilkisu kece mace d’aya acikin ‘ya’yana na so ganin auran ki sai dai kash… Kana na ka ALLAH na na shi kuma na ALLAH shine dai-dai,ALLAH yamiki rahama yasa k’arshen wahalar kenan,Bilkisu kin dace Insha-ALLAH dan kin mutu a d’aya daga cikin ranakun da babu tambayar kabari akan mamaci,kin mutu ranar alhamis, tasa hannu tashare hawaya ta fuskanci su Innan Julaibib “mu mata abinda aka fiso ama mamaci da gaggawa,su uku suka mata wanka suka samata likkafani suka sata a makara Innan tad’auko fallan zani aka lullu6eta,Maude da Julaibib suka fita da ita aka mata sallah sai makabarta! Sun dad’e suna ne ma mata gafara musamman mahaifinta da masoyin ta Julaibib da Yayyinta su Maude da sauran yan’uwa da abokan arziki.

“YA ALLAH!KA GAFARTA MATA!YA ALLAH KABA TA TABBATA!

Suka juya zuwa cikin gari jikinsu a sanyaye,zuciyoyin su cike da alhini da d’acin mutuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button