GWAJIN DAFI COMPLETENOVELS

GWAJIN DAFI COMPLETE

GWAJIN DAFI COMPLETE HAUSA NOVEL

Da jami’ar Abuja zan tafi amma nace ni nan nake so,ni kaina kuma ban san dalilin dayasa na za6i nan d’in ba,ashe k’addarar had’uwa ta da wannan miskilin d’an uwan na kane zai zama silar koma wata wajan mahaifina wanda dama ba abinda yake so sama da ya ganni kusa dashi,saboda mahaifiyata lokacin da data haifi k’anina ko ganinshi batayi ba ta rasu,da yammacin ranar shima abinda ta haifa yace ga garinku nan,mutuwarta ta dakeshi sosai saboda suna san juna suna zaman lafiya. Yadad’e baiyi wani aure ba,auran da yasa ke ma Me Martaba ne yagaji da ganinshi haka ya aura mishi matar. Saboda ni duk lokacin daya samu sarari yake zuwa Nigeria kasarmu ta gado.

Musaddiq ya kuma jan dogon tsaki fiye dana d’azu ALLAH yashiryeka.Julaibib yayi murmushi”amin shiriyar da ba ta ALLAH ba shirme da shiririta ce kuwa ,amin nagode”.

Shi da Inna suna zaune a tsakar gida,yana 6arar gyad’a Inna kuma tana gyaran tsakin masara, jefi -jefi suke magana, saboda shirin da suke sauraro a gidan rediyo.

Assalamu alaikum.

“Inna tana nan…?

Daga zauren gidan suka jiyota.Cikin murmushi suka amsa sallamar.Inna tarage sautin rediyon “maraba da yar gidan Inna,to shigo mana kya tsaya a zaure kamar wata bak’uwa?Tashigo tana yar dariya”Inna na yi laifi na zaci kinyi fushi ne shi yasa naji tsoron shigowa kai tsaye”Dan ALLAH Inna kiyi hak’uri.Tazauna tana kallanshi”barka da warhaka Yaya Julaibib,Ina kwana.Yad’an shafa kai,tare da dauke kai daga kallan da take mishi.

Sudaida…Lafiya lau, ya karatu’?

Alhamdulillahi gashinan muna tayi ba kama hannun yaro.

Tajuya wajan Inna tana gaisheta. ALLAH Inna jiya dakika aiko mantawa nayi da aka tashi daga makarantar allo ban shigo ba.Inna ta girgiza kai”ba kome nima nayi tunanin haka.Tasa hannu ta d’ibo gyad’ar tana tayashi 6arewa,yau za musha fate kenan?Inna tace wai da dambu zanyi. Tad’an k’aryar da kanta gefen dama”kai Inna gwamma dai faten,kin san Hajiya(Kakarsu)tafi san shi,zaifi armashi ma idan Yaya Julaibib yaje yasiyo mana tantak’washi.Yad’ago kai yana kallanta”ni zanje insiyo miki tantak’washi?Tace to ai da Hajiya da Inna za musha.Baice komai ba yamik’e yashiga dak’inshi, bai dad’e ba yafito yanasa hula,yama Inna sallama yafita… Sudaida tad’an d’aga murya karfa ka manta kaji?Yak’arasa ficewa.Shiruma amsace.

Sai bayan sallar azahar suka shigo shida Musaddiq.Tace yauwa na ma huta dama yanzu nake shirin biyoku shago.Musaddiq yakalleta “ta samu kenan,idan kaji gangami da labari.Yabud’e kwanan data ajiye agabansu,tana murmushi”Yaya Musaddiq chips d’in gwaza namuku tunda baku cika san shan fateba”Yad’auki d’aya yakai baki,kai wannan yarinya da iyayi kike wai zuwa kashin rana da fitila.To Yaya Musaddiq chips lallai sai da dankalin turawa?Gobe ma da dankalin hausa zanyi. Julaibib yamik’e”kici lafiya…kai zo mutafi gidan Hajiya baza a rasa abincin arzik’i acan ba.Haushi yakamata”to wannan na tsiya ne?A ah sai dai shima chips d’in bazan ciba.

Inna tasa baki”kai baza a maka gwaninta ba kenan?Ya waiwaya ya kalli Sudaida da wani irin kallo data kasa fassarawa”ni nasa ki? Tagalla mishi harara dan ba k’aramin haushi yaba taba,shiruma amsace ta shige d’akin-girki dan k’arasa abinda takeyi.Taja tsaki”shi wannan d’ansarai autan Innan ALLAH yasawwak’e mishi”.

Yana wankin kayanshi tashigo gidan, Asma’u ce ita yake bi.Takalleshi”manya ba a ganinku sai an cike foam,foam d’inma sai wanda ake buga mishi stamp.Yayi murmushi”Yaya Asma’u ban kai nan ba,wa ne kare da hantar kura?Barin dai k’arasa inzo mugaisa.Tawuce d’akin Inna suka gaisa,sai ta mik’e”barin lek’a d’akin autan na ki ko zan samu abun sawa a bakin salati.Tashige ciki tana mishi bincike. Yagama shanya kayan sannan yabita,baiji dad’in abinda ta mishi ba,gaba d’aya ta hargitsa mishi d’akin,har kayan sawanshi na cikin akwati sai da ta bincike.Yazauna yana kallanta cikin zancen zuci “Yaya Asma’u yar sa’ido ce ta gaban kwatance, da shiga sharo ba shanu,kamar wata yar C I D,kaza dai garin tone-tone wata rana zata tono wuk’ar yanka ta.

Takalleshi”kai d’akin na ka ba wani abu da mutum zai kai bakinshi zuwa uwar hanji sai tarin littafai kala-kala?Yana tattara littafan data hargitsa yace”to dama me zaki samu a d’akin talaka kuma d’an makaranta?Aike zaki taimakamin koda da yar dubu goma in k’ara na Hand-out da ‘yan wasu abubuwan,kinga kinyi halin girma,ladanki yana wajan ALLAH.Lallai yaran nan ka ci abinci sauranka ruwan sanyin randan Inna.Yanzu duk cikinmu akwai wanda ke cin kud’in Baba kai harma da Innan kamar ka? “Ni?Yanuna kanshi da d’an yatsanshi”sharri dai ba kyau Yaya Asma’u.Tad’an harareshi tana dariya” za ka fad’i haka mana.Yagyad’akai”ALLAH Yaya Asma’u tunda ke hajiya ce kamata yayi ace kin d’auko ma Inna yar aiki,kina biyanta duk k’arshen wata,ni jarin nawa baiyi k’wari bane dani zanyi hakan.

Tamishi wani kallo”ALLAH sarki, Inna ce za a d’auko ma yar aiki?To ina abun yake wai maye ya cinye jariri?Tabbb…kai akwai ka da san kashe kud’i na ba gaira ba dalili,amma fa harda dan baka san yadda ake wahala wajan nemo su bane.Na sani mana tunda nima ina sana’a.Ta tareshi da sauri “A ah ban yadda ba sana’ar taka har wata sana’ace da zaka fad’i wahalhalun cikinta?Kuna komawa Gidan-Waya Baba zai cigaba da kula muku da kome, kaga ai yafiku shan wahala daga kai har Musaddiq d’in,ko zirga-zirgan da yake yi tsakanin nan da Kaduna ai bakwayi.Hun Julaibib arzik’i gashin hancine rabuwa dashi ba dad’i,kabari sai ka gama karatun,ka fara sana’a ka’in da na’in sai muyi zancen. Yace to Ubangiji yanuna mana lokacin.

Dama so yake yaji me za tace, amma ai ya riga yasan halinta na rowa,indai maganar kud’ine kuma itace zata bayar tofa sai anyi tata6urza,sa6anin idan itace zata kar6a yanzu mutum zai sha dogon lissafi da sharhi.Tamike” kai ni barinje wajan Inna baza a rasa abun kaiwa bakin salati ba.Yagirgizai kai”yanzu haka da abinda yakawota gidan,kuma abun tirrrr d’in tana da rufin asirinta dai-dai gwargwado dan tafi Yaya Karima ne sa ba kusa ba, amma Yaya Karima ta fita wadatar zuci.

Da safe kafin Inna tafito ya gama had’a karin kumallo,yashare tsakar gidan,ya wanke bayi,tafito tana shi mishi albarka kamar yadda tasaba “Ubangiji yamaka albarka, yarufa maka asiri duniya da lahira.

Yayi murmus”Amin Innar mu ALLAH yabar manake, yad’an kalleta”nifa yar aiki zan d’auko miki Insha-ALLAH kafin mukoma makaranta, ayyukan suna miki yawa,ni kuma a yanzu ina san ganinki cikin jin dad’i da hutu.Tayi yar dariya”to banda abinka Julaibib ina aikin yake da har za a d’auko maiyi?Dagani sai Alhaji,idan kana garine muke mu uku fa.Tagirgiza kai “ni kam nagode,da duk ya’ya haka suke jin tausayi da soyayyar mahaifansu to da al’umma ta kasance cikin tsabta da kwanciyar hankali mara yankewa,nagode maka gaya amma kabar zancen yar aiki,kai baka san ‘yan aikace-aikacen ma motsa jiki bane?Na sani Inna”to kibari asamo miki koda wacce zata dinga miki hidimar tsakar gida,ke kuma kicigaba da yin abinci.

Ga kayan motsa jikina nan ba sai ki dinga amfani dasuba.Inna takama ha6a????tana dariya”Wuuu rabani da wuyu”kashin k’ota”kayan motsa jiki na zamani ai sai ku,ni ina zan iya da wad’annan k’arafa da na’urori? ALLAH dai yamaka albarka autana.Yayi murmushi yana shafa kwantaccen bak’i gashin kanshi me shek’i da kyallin irin mayukan gyaran gashin da yake amfani dasu. Suna gama karyawa yamata sallama yatafi shagonsu dan neman na halali,dansu an d’orasu a kan dogara da kai a hakan kuma suka taso,ba dogara da kud’in mahaifa ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button